Yadda sojojin Najeriya suka hallaka ƴanbindiga da dama a Zamfara

Lokacin karatu: Minti 4

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun hallaka ƴanbindiga da dama a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Sojojin sun samu nasarar kashe ƴanbindigar ne a wansu hare-hare ta sama da suka kai a wani yanki na ƙaramar hukumar Bukkuyum, inda jiragen yaƙi suka yi ruwan wuta kan wani sansanin ƴanbindigar a dajin Makakkari, kamar yadda wata sanarwa da sojojin suka fitar ta bayyana.

Ƴanbindigar sun daɗe suna cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yamma, musamman ma jihar Zamfara - inda suke afka wa al'ummomi a ƙauyuka da garkuwa don neman kuɗin fansa da ƙona gidaje da kuma satar abinci.

Harin da sojojin suka kai na zuwa ne a daidai lokacin da ƴanbindigar ke ci gaba da kai hare-hare babu ƙakkautawa, musamman garkuwa da mutane.

Ko a ranar Juma'a da ta wuce, ƴanbindiga sun kai hari ƙauyen Adabka da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum, inda suka yi garkuwa da mutane da dama da kuma hallaka jami'an tsaro 13, kamar yadda kamfanin dilalncin labarai na AFP ya ruwaito.

Ta yaya lamarin ya faru?

Cikin wata sanarwar da rundunar sojin sama ta ƙasar ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Air Commodore, Ehimen Ejodame ya ce dakarun ƙasar sun kai harin ne a lokacin da ƴanbindigar na shirin kai hari kan wani ƙauye ne a Zamfara.

''Bayanan sirri da muka tattara sun tabbatar da motsin ƴanbindiga kimanin 400 da ke shirin far wa wani ƙauyen manoma, nan take kuma dakarunmu suka far musu da hare-hare ta sama da ta ƙasa'', in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun samu nasarar kashe wasu jagororin ƴanbindigar da dama da kuma mabiyansu masu yawan gaske.

'Jim kaɗan bayan ƴanbindigar sun gama taro'

Wani ɗan jarida mai bincike a kan ayyukan ƴanbindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya, Mannir Sani Fura-Girke ya shaida wa BBC cewa tun da farko ƴanbindigar sun taru a gidan wani ɗanbindiga mai suna Kachalla Buba Guntu a wani gandun daji a Bukkuyum - bayan sun bar gidan shi ne kan hanyarsu ta zuwa Anka kwatsam sai jirgin soji ya afka musu.

"A halin yanzu ana ci gaba da tattara bayanai na yawan ƴanbindigar da aka kashe'', in ɗanjaridar

Ya ƙara da cewa akwai manyan ƴanbindiga da dama cikin waɗanda aka kashe ganin cewa bayan kammala taro da suka yi ne jirgin sama na soji ya far musu.

Ya ce sun yi taro ne inda suke shirin kai hari a ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum da kuma Bakura.

"Kawo yanzu ba a fara fitar da sunayen manyan ƴanbindigar da suka mutu saboda akwai sojoji da motocin suna can suna farmaki a yankin," in ji shi.

Ya kuma ce sojoji suna ci gaba da dannawa zuwa wasu dazuka da ke yankin, bayan harin da jirgin ya kai.

Sai dai ya ce abin da yake yi wa sojojin cikas a yanzu shi ne motocinsu ba sa iya zuwa wajen da ƴanbindigar suke sakamakon ruwan sama da ake yi a kwanakin-nan, abin da ya sa suke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

"Amma waɗannan hare-hare da jiragen yaƙin sojojin suka yi a yanzu, zai taimakawa manoma don su koma gonakinsu''.

''Idan aka ci gaba da samun irin wannan nasara mutane za su samu sauƙi matuka," in ji Mannir Sani Fura-Girke.

Rikicin ƴanbindigar na bazuwa

Harin na zuwa ne kimanin mako guda bayan da wasu malaman addinin Musulunci a ƙasar suka yi iƙirarin tattaunawa da ƙasurgumin ɗanbindigar nan Bello Turji da aka jima ana nema ruwa a jallo, da nufin kawo zaman lafiya.

Cikin wata hira da kafar DCL Hausa mai yaɗa labarai a shafukan sada zumunta, ɗaya daga cikin malaman da ke cikin kwamitin, Malam Musa Yusuf wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah, ya ce Bello Turji ya sako mutum 32 da ya yi garkuwa da su, tare da bayar da wasu daga cikin makamansa.

Hare-haren da ƴanbindiga na ci gaba da bazuwa zuwa wurare da dama, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Satar shanu da yin garkuwa da mutane ya zama abin da ƴanbindigar suka fi mayar da hankali a yanzu.

Baya ga wannan, suna kuma saka wa manoma haraji kafin su samu damar zuwa gonakinsu.

Rikicin yana ƙara ta'azzara matsalar yunwa a yankin arewa maso yamma saboda mutane ba sa samun damar zuwa gona - ga kuma sauyin yanayi da dakatar da tallafi da ƙasashen yamma suka yi.

Duk da girke sojoji da dama da gwamnati ta yi domin yaƙi da ƴanbindigar, lamarin ya ki ci ya ki cinyewa.

A watan Yuli, sojojin Najeriya suka kashe aƙalla ƴanbindiga 95 a wasu hare-hare ta sama a jihar Neja.

Sai dai lamarin yana ƙara yi wa sojojin yawa, inda ƴanbindigar ke bazuwa daga arewa maso yamma zuwa tsakiyar Najeriya.