Edouard Mendy ya karya ɗan yatsansa

An yi wa golan Chelsea, Edouard Mendy tiyata bayan da ya samu karaya a ɗan yatsa.

Ɗan kwallon Senegal mai shekaru 30, bai buga wa Chelsea wasa ba tun bayan gasar cin kofin duniya saboda rauni a kafaɗarsa.

Golan Spaniya, Kepa Arrizabalaga shi ne ya kasance mai tsaron raga a wasannin Chelsea hudu da suka gabata.

Chelsea ce ta goma a teburin gasar firemiyar Ingila kuma a ranar Lahadi ta sha kashi a hannu Manchester City a gasar cin kofin FA.