Wane tasiri kwace garuruwan da Ukraine ta yi a hannun Rasha zai yi kan Putin?

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Bayan wata shida ana gwabza yaki, ba a san me shugaban Rasha ke shirin kaddamarwa nan gaba ba.

An saba ganin yadda gidan talabijin na kasa a Rasha yake bude shirinsa a duk mako da nasarorin da Kremlin ke samu a yaki da Ukraine.

To amma shirin na ranar Lahadi ya bude da akasin haka.

''A fagen daga a wannan aiki na musamman da ake yi a Ukraine, wannan ne mako mafi wahala,'' a cewar mai gabatar da shirin Dmitry Kiselev, wanda ake iya ganin alamun damuwa a fuskarsa.

''Lamarin ya fi muni a yankin Kharkiv, inda abokan gaba suka fi mu yawa, da hakan ya sa dole dakarunmu suka bar garuruwan da suka kwato wa 'yanci a baya.''

Rasha ta kwace yankunan watannin da suka wuce, to amma bayan bata-kashi da sojojin Ukraine, dakarun Rasha sun rasa yankuna da dama a arewa maso gabashin Ukraine.

Sai dai duk da haka kafar yada labaran Rasha na nuna cewa janyewar sojojin kasar a yankin Kharkiv ba ta nufin gazawar mayakansu.

''Ma'aikatar tsaron Rasha ta yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa dakarun Rasha sun kwashi kashinsu a hannu a garuruwan Balakliya da Kupiansk da Izyum,'' a cewar jaridar Rossiyskaya Gazeta. ''Ba guduwa suka yi ba, dama an tsara cewa za su janye daga wurin.''

A jaridar Moskovsky Komsomolets kuwa, wani mai sharhi kan harkokin soji ya ba da na sa ra'ayin da cewa ''a bayyane take cewa mun raina abokan gaba. Sojojin Rasha sun saki jiki ne har matsala ta faru... Hakan ya sa aka ci galaba a kanmu, muka yi kokarin rage asarar sojojin da za a iya samu ta hanyar barin yankin kafin a yi wa sauran da suka rage kawanya.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi ma Shugaban Chechnya Ramzan Kadyrov ya yi irin wadannan kalamai.

''Idan ba a sauya tsari ba yau ko gobe, to kuwa dole na tattauna da shugabannin ma'aikatar tsaro da kuma ofishin shugaban kasa, na bayyana musu halin da ake ciki. Lamarin yana da daure kai.''

Watanni shida kenan da Vladimir Putin ya kaddamar da kutsen Ukraine gaba-gadi. A kwanakin da suka biyo baya, 'yan siyasa a Rasha da masu sharhi a kafar talabijin sun rika bayyana abin da Kremlin ta kira da ''aiki na musamman'' cewa za a kammala shi cikin 'yan kwanaki; 'yan Ukraine za su jinjina wa dakarun Rasha a matsayin wadanda suka 'yantar da su, kuma gwamnatin Ukraine za ta ruguje.

Hakan ba ta samu ba.

A maimakon haka, watanni shida kenan, sojojin Rasha na ci gaba da rasa wurare.

Babbar tambayar a nan ita ce: Shin ko hakan zai yi tasiri ga siyasar Vladimir Putin?

Sama da shekaru 20, Mr Putin na ci gaba da zama gagarabadau a Rasha, kan yadda yake tafiyar da lamura a kasar.

Akwai masu ganin shi kamar Harry Houdini, saboda yadda yake kubucewa daga kowane irin tarko da aka yi masa.

Duk wani kulli ko tarko da aka yi wa Mr Putin a ko da yaushe yana da dabarun kubuta. Sai dai hakan ya sauya bayan 24 ga watan Fabrairu.

Watanni shida da suka wuce sun nuna cewa lissafin Shugaba Putin na kutsawa Ukraine ya ba shi ruwa. Ya kasa samun nasara cikin gaggawa, an tabka kazamar asara, ga kuma shan kashi mai muni.

Idan kwarjinin shugaba mai kama-karya ya dusashe, zai iya haifar masa da matsala. Putin na da masaniya kan tarihin Rasha. Shugabannin da suka kaddamar da yaki suka yi rashin nasara ba su gama lafiya ba.

Kashin da Rasha ta sha a hannun Japan ya haifar da juyin-juya-halin shekarar 1905. Kazalika rashin nasara a Yakin Duniya na Daya a shekarar 1917 ya haifar da juyin-juya-hali da kawo karshen mulkin Tsar.

To amma karara, Shugaba Putin bai shirya shan kaye ba.

A ranar Litinin, mai magana da yawunsa Dmitry Peskov ya fada wa 'yan jarida cewa '' Rasha za ta cigaba da aikin da take yi na musamman a Ukraine har sai ta cimma burinta.''

Hakan ya kai mu ga wata tambayar: Me Putin zai yi nan gaba?

Abu ne mai wahala wani ya iya fada maka abin da Vladimir Putin ke tunani ko yake kitsawa. Watakila abin da zai yi ya danganta daga bayanan da ya samu daga sojojinsa da shugabannin hukumar leken asirin kasar.

To amma abu biyu da muka sani su ne: da wahala shugaban na Rasha ya amsa yin kuskure. Kuma ba ya sauya matakin da ya dauka.

.

Asalin hoton, Kremln.ru

Bayanan hoto, A Moscow, za a iya ganin Vladimir Putin a natse cikin annashawa, yayin da yake kaddamar da wani sabon Lilo

Daga abin da muka gani daga kafar yada labaran gwamnati, Rasha ta jingina shan kayen da take yi a fagen kan taimakon da kasashen Yamma ke bai wa Ukraine.

''Kyiv, wadda ke samun taimakon Nato, na kawo mana hare-hare,'' in ji gidan talabijin na Rasha.

Babu wata tambaya mafi hadari da ta fi yawo a zukata tsawon watanni kamar: idan har ya gaza samun nasara ta hanyar makaman da aka saba gani a yaki, ko Shugaba Putin zai iya amfani da makamin nukiliya?

A 'yan kwanakin da suka gabata, kwamandan sojojin Ukraine, Valeriy Zaluzhnyi, ya yi gargadin cewa: ''akwai barazanar sojojin Rasha na iya amfani da makamin nukiliya idan suka samu kansu a wani yanayi.''

Ga yanzu da babu alamun razana daga bangaren Kremlin. Gidan talabijin na Rasha na ci gaba da nuna cewa nasara tasu ce. Suna bayyana harba makamai masu linzami da Rasha ta yi kan wasu cibiyoyin makamashin Ukraine da ''wani ci gaba a aiki na musamman'' da suke yi.

Ga Shugaban Rasha, Asabar din da ta gabata, kamar yadda rahotanni suka nuna cewa kasarsa na rasa yankuna hannun Ukraine, hankalinsa bai tashi ba. An nuna Vladimir Putin a natse a Moscow, yana kaddamar da wani babban lilo mai juya wa da jama'a, mafi tsawo a turai.

Har yanzu Shugaban Rashar na da yakinin cewa, kamar sabon babban lilon Moscow da ya kaddamar da ke juyawa da jama'a, ''aikin na musamman da yake yi'' nasara za ta juyo kansa.