Ukraine ta ce ta kwato wasu yankuna daga hannun Rasha

Asalin hoton, Reuters
Ukraine ta ce ta samu nasarar kwato wasu yankuna da dama daga cikin wadanda dakarun Rasha suka kwace iko da su tun bayan mamayr da Rashar ta yi wa kasar.
Rahotanni na cewa yankuna da dama a rabin gabashin Ukraine sun rasa wutar lantarki bayan hare-haren da dakarun Rasha suka kai kan cibiyoyin samar da wutar da sauran kayayyakin jin dadin jama'a. An shiga wannan yanayi ne bayan da Ukraine ta ce ta samu gagarumar nasara a martanin da take mayar wa Rasha a yakin a yankin Kharkiv, inda ta ce ta sake kwato yankuna da dama da Rashar ta kame. Bayan rahotannin da suka rika bayyana na rashin wutar lantarkin, sai kuma Shugaban Ukraine din Volodymyr Zelensky a jawabin da ya saba gabatarwa da daddare ya tabbatar da hakan inda ya dora alhakin lamarin a kan Rasha. Ya zargi mai mamayar kasar tasa da haddasa gagarumar matsalar katsewar wutar lantarki a gabashin Ukraine inda aka rasa wutar gaba daya a yankunan Kharkiv da Donetsk, a wasu sassan kuma matsalar ba ta yi tsanani ba sosai, inda ake samun wutar nan da can daga lokaci zuwa lokaci. Shugaban ya ce, Rasha ta kai hare-hare kan muhimman abubuwan jin dadin rayuwar jama’a wadanda ba su da alaka da soji, ba don komai ba sai don ta hana mutane samun wutar lantarki da dumama muhallansu.
Sai dai daga baya an yi nasarar mayar da wutar lantarkin a wasu wuraren, amma kuma duk da haka jami’ai sun ce wurare da dama har yanzu ba su da wutar wasu ma kuma bas u ruwa.
Wani jami’i mai taimaka wa shugaban Ukraine din ya ce an harba makami a tashar samar da lantarki ta Kharkiv.
Mukadashin shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a yankin Anatolii Torianyk, ya yi magana kan harin.
Ya ce, ''wani makami mai linzami ya fada kan wata cibiyar samar da lantarki. An lalata wata nau'ra da ke ba wa birnin Kharkiv wuta.
Akwai mutum biyu da ke bakin aiki a cikin ginin da makamin ya fada wa.
Mun samu daya da ya mutu. Ana kuma kan fara neman na biyun.''
gajin garjin na Kharkiv Ihor Terekhov, ya kira matakin da cewa wata ramuwa ce Rasha ke son yi a kan nasarar da sojojin Ukraine ke samu a baya-bayan nan.
Wani wakilin BBC ya ce an rika jin karar ruwan makamai masu linzami ba kakkautawa a birnin a cikin dare.
Rasha dai ta musanta zargin kai hari kan cibiyoyin farar hula.
A martanin gwamnatin Rasha ta bakin wani magajin garin da ke kusa yankin Kharkiv-- Belgorod, ya dora alhakin katsewar lantarkin ne a kan matsala da ya ce an samu a wata karanar tasha.
Kuma ya ce tuni an shawo kan matsalar tare da mayar da lantarkin.
Duka wannan dai na kasancewa ne yayin da rahotanni ke cewa Ukraine na samun gagarumar nasarar sake kwato yankunan da Rasha ta karbe iko da su a 'yan kwanakin nan.










