Mene ne bututun Nord Stream 1 na Turai?

Asalin hoton, Getty Images
An rufe bututun Nord Stream 1 sakamakon zubar da mai da yake yi bayan hujewar da ya yi, kamar yadda kamfanin Gazprom ya bayyana.
Kamfanin na ƙasar Rasha ya ce an gano matsalar ne a ɗaya daga cikin tashoshin, a lokacin da aka je duba bututun tare da wasu ma'aikata daga wani kamfanin ƙasar Jamus da suke taya su gyara.
Kamfanin Gazprom ya bayyana cewa ana gyaran hujewar bututu a manyan injina ne kawai a ayyuka na musamman - lamarin da Rasha ta ce takunkumin ƙasashen yamma ya jawo wa CIKAS.
A kwanakin baya ne dai Turai ta zargi Rasha da taƙaita fitar da gas ɗin da take yi domin mayar da martani kan takunkumin da aka saka mata.
Mene ne Nord Stream 1 kuma yaya adadin gas din da yake samarwa?
Bututun Nord Stream 1 na da tsawon kilomita 1,200 wanda ya bi ta cikin tekun Baltic tun daga gaɓar tekun Rasha kusa da St Petersburg zuwa arewa maso gabashin Jamus.
Bututun ya shafe shekara goma yana aiki kuma yana jigilar gas mai yawan miliyan 170 na cubic meter na gas tun daga Rasha har zuwa Jamus.
Haka kuma kamfanin Nord Stream AG ne mamallakin bututun wanda akasarin masu hannun jari a kamfanin mallakar kamfanin Gazprom ne na ƙasar Rasha.
Haka kuma Jamus ɗin ta yi alkwarin gina wani sabon bututun mai suna Nord Stream 2 sai dai an dakatar da aikin jim kaɗan kafin Rasha ta yi wa Ukraine kutse.

Ta yaya Rasha ta rage tura gas ɗin kuma ta ya hakan ya shafi Turai?
A watan Mayu, Gazprom ya rufe gas ɗin Yamal wanda ya bi ta cikin Belarus da Poland kuma yake kai gas Jamus da sauran ƙasashen Turai.
Sai dai a tsakiyar Yuni, Gazprom ya rage gas ɗin da yake jigila ta bututun Nord Stream 1 da kashi uku bisa huɗu - daga cubic meter miliyan 170 zuwa cubic meter 40.
A farkon Yuli, an rufe Nord Stream 1 na tsawon kwana goma inda kamfanin ya ce yana so ya yi gyara.
Hakan ya sake faruwa a farkon makon nan a lokacin da Rasha ta dakatar da fitar da gas ɗin zuwa Turai inda ya ce akwai buƙatar a yi gyara.
Ministan tattalin arziki na Jamus Robert Habeck ya musanta cewa an samu wata matsala da za a ce za a yi gyara inda ya ce bututun lafiyarsa kalau.
Sai dai mai magana da yawun Shugaban Rasha Vladimir Putin ya dage kan cewa takunkumin da ƙasashen yamma suka sa ya jawo cikas da kuma lalata kayayyakin Rasha.
Haka kuma Gazprom ɗin ya ce zai dakatar da jigilar gas zuwa kamfanin makamashi na Faransa Engie.

Asalin hoton, Reuters
Ta yaya wannan datse jigilar gas ɗin ya shafi Turai
Nahiyar Turai musamman Jamus za a iya cewa ta dogara ne kusan baki ɗaya ga gas ɗin Rasha domin samun makamashin da take buƙata.
A lokacin da Rasha ta sanar da niyyarta ta rage fitar da gas ɗin a watan Yuli, a rana ɗaya gas ɗin ya ƙaru daga wurin yan sari da kashi goma cikin 100.
A halin yanzu farashin gas ya ƙaru da kusan kashi 450 cikin 100 idan aka kwatanta da bara.
Wane martani kasashen Turai ke yi game da rage fitar da iskar gas?
Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine a baya ya zargi Rasha da ƙaddamar da yakin iskar gas a kan kasashen Turai’’.
"Rasha na amfani da gas a matsayin makami, a cewar Kate Dourian, wani jami’i a cibiyar samar da makamashi.
Kafin Rasha ta mamaye Ukraine, Jamus na samun kashi 55 na iskar gas dinta daga Rasha. Kasar ta Jamus ta yi kokarin rage haka zuwa kashi 35, inda kuma ta sha alwashin cewa za ta daina shigar da gas kwata-kwata daga Rasha.
A wani bangare na hakan, ta nemi hanyoyi mafita na shiga da iskar gas, inda yanzu take sayowa daga Norway da kuma Netherland.
Jamus din tana kuma shirin sayo tashoshi biyar domin shigo da iskar gas da aka sarrafa daga Qatar da Amurka, in ji Ms Dourian.
Sai dai hakan zai kunshi gina sabbin bututai daga bakin teku zuwa sauran biranen Jamus, wadda zai dauki watanni da dama.
Ta ya ya Turai ke rage bukatar sayo gas?
Kungiyar Tarayyar Turai ta cimma wata yarjejeniya da za ta sanya mambobinta rage amfani da gas da kashi 15.
Gwamnatin Jamus na fatan rage amfani da gas da kashi 2 ta hanyar rage amfani da hasken lantarki da kuma saka abubuwa su yi zafi a gine-ginen jama’a lokacin hunturu.
Sifaniya ma tuni ta riga ta kawo irin wadannan dokoki, inda Switzerland ma ke shirin yin hakan.
Yawancin Turawa ma na daukar matakai da kansu.
"A Jamus," a cewar Ms Nakhle, "mutane na sayan murhun katako da kuma saka na’urorin samar da hasken rana. Kowa na daukar matakan rage amfani da iskar gas.
"Kada mu dauki yadda mutane ke fama da karancin gas a matsayin abin wasa."











