Tsarin da Rasha ke bi wajen sauya tunanin 'yan Ukraine

Yara na zuwa makaranta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a koyar da yaran da ke zuwa makaranta a yankunan Ukraine da aka yi wa kawanya da manhajar Rasha

A daidai lokacin da yara a kasar Ukraine da ke yankunan da aka yi wa kawanya ke shirin komawa makaranta ranar 1 ga watan Satumba, za a rika koyar da su darasin tarihi daban ba kamar yadda aka saba a baya ba.

BBC ta gano cewa ana matsa wa malamai a Ukraine wajen amfani da manhajar koyarwa ta Rasha.

Wanda hakan ke nufin sanin ilimin duniya ta yadda Kremlin ke so.

An canza yawancin sunaye da ke cikin wannan labari.

A yankunan kudancin Ukraine da Rasha ta kama, an sanya wa gine-ginen ma'aikata da kuma na makaranta tutocin kasar Rasha.

A birnin Melitopol da Rasha ke iko da shi, 'yar Iryna mai shekara 13, na shirin komawa makaranta domin fara aji biyu a makarantar karamar sakandire.

Sai dai mahaifiyarta na nuna damuwa.

"Abin da ya fi damuwa da manhajar koyarwar ta Rasha shi ne abin da za a koya musu a bangaren tarihi.

Za a koyar da shi ta wani bangare’, a cewar Iryna. Ta kuma fusata yadda ake koyar da su darussa da harshen Rasha a maimakon na Ukraniya: ‘Suna tilasta amfani da al’adunsu – ba na son yara su zama wadanda lamarin zai shafa,’’ in ji Iryna.

An yi ta kama da yunkurin shafe tarihin Ukraine a yankunan da aka mamaye a bainar jama’a a kafafen intanet da ke goyon bayan Rasha.

An sha nuna hotunan dakarun Rasha na cire takardun tarihi na Ukraine daga dakunan karatu.

Ma’aikatar fadakarwa ta Rasha, ta yi alkawarin samar takardun tarihin kasar ga yankunan da ta mamaye a Ukraine.

BBC ta yi nazarin abin da takardun makaranta da ma’aikatar fadakarwar ta amince za a yi amfani da su da kuma bambance-bambance tsakaninsu da wadanda aka wallafa a 2016 da 2022, kafin soma yakin.

Tsarin da Rasha ke bi wajen sauya tunanin 'yan Ukraine
Littatafan Rasha
Bayanan hoto, Littattafan Rasha sun bayyana kwace ikon Crimea a matsayin 'sake hada-kan Rasha' da cewa ''yan kishin kasa masu tsattsauran ra'ayi ke mulkin Ukraine''
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

BBC ta tuntubi ma’aikatar fadakarwa ta Rashar, sai dai ba ta samu wata amsa ba.

Iryna ta yi niyyar barin yankunan Ukraine da aka yi wa mamaya, amma ba ta son ta tafi ta bar gidanta.

Ta kafe cewa ita ba ta amince ‘yarta ta ci gaba da karatu karakshin manhajar koyarwa ta Rashanci ba amma ta damu kan barin ‘yar tata a gida.

Bisa manufa, dalibai kan yi karatu da manhajar harshen Ukraniya ta hanyar intanet, sai dai iyaye na nuna damuwa kan abin da hakan zai jawo.

"Me zai faru idan wani ya sanar da mu kan sabuwar manhajar karatu ta Rasha da aka kawo ko idan an fara yi min barazana ni da ‘yata saboda rashin samun karatu da manhajar Rasha? A cewar Iryna.

A ranar 19 ga watan Augusta, wani rubutu da wata kafar sada zumunta ta Telegram mai goyon bayan Rasha ta yi, ta wallafa wani sako da wani malami mai goyon bayan Rasha a wata makaranta a wajen garin Melitopol ya aika.

Sakon ya ce ‘ba za a koyar ta hanyar intanet ba a yankunanmu da muka yantar’’ (yadda Rasha ta kwatanta yankunan da ta mamaye).

Za a cire wa Iyayen da suka ki tura ‘ya’yansu domin koyarwa ‘hakkinsu na iyaye’ muddin suka saba ka’ida.

Malaman da aka nemo aka kuma fitar dasu daga kasar

Yakin ya kuma shafi malamai da ke goyon bayan Ukraine, inda aka tilasta wa wasu buya da aika wasu sake-koyar da su da kuma barazanar fitar da su daga kasar.

Dmytro, ya kasance shugaban makaranta a garin Melitopol.

Yana da dalibai sama da 500 kafin mamayar Rasha.

A yanzu, ya shiga buya bayan nemansa da dakarun Rasha ke yi saboda kokarin shirya wa yara a Ukraine koyo da manhajar kasar ta intanet.

Shugaban makarantar ya ce yana sane da malamai da aka tilasata wa ko kuma suka bai wa jami’an Rasha hadin-kai.

Inda aka tura su zuwa Crimea ko kuma Rasha don sake koyar da su ta hanyar tsarin da gwamnatin Rasha ke da shi.

"An fada musu cewa"mu ‘yan Rasha ne, dukkan mu mutane daya ne. Ya kamata mu hada kai" sannan akwai kuma bukatar sanar da yara hakan," a cewarsa.

Yayin da Dmytro ya zabi zama a yankunan da Rasha ke iko da su, malamai da dama da kuma iyaye sun yanke shawarar barin yankunan.

dakarun Rasha da wani yaro kan keke

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An zargi dakarun Rasha da barazanar fitar da malaman da ke goyon bayan Ukraine daga kasar

Marina, malama ce a garin Nova Kakhovka da ke yankin Kherson, ta tsere a karshen watan Yuli.

Ta yanke shawarar hakan ne bayan da dakarun Rasha da wani shugaban ilimi da Rasha ta kai, suka sanar da cewa za su rufe makarantar da take saboda shugabanta ya ki bayar da hadin-kai.

Marina ta ce ta ji batun karancin ma’aikata a garin na Nova Kakhova, inda wasu malamai ke koyar da darussa da ba su da alaka fiye da daya.

Ta nuna damuwa cewa tsarin ilimi da Rasha ta kawo zai yi illa ta wajen sauya musu tunani.

"Aikin da suka saka a gaba shi ne sauya tunani da kuma sanya akidunsu cikin zukatan yara.

Suna son ‘ya’yanmu su manta kasar da suke rayuwa a ciki da manta su waye su.’’

Yi wa tarihi kwaskwarima

Leonid Katsva, mawallafi ne dan kasar Rasha da ya koyar da dalibai darussan tarihi har na tsawon shekara 42 a Moscow.

Ya ga yadda aka rika sauya ainihin abin da ya faru cikin littatafan makaranta na Rasha.

Idan aka zo ga batun yadda aka kwatanta kwace iko da Crimea, mawallafin ya ce "ba a yi magana ba kan ayyukan da dakarun Rasha suka yi a lokacin. "

A sabuwar shekara ta makaranta, Mista Katsva ya yi imanin cewa littatafai za su kunshi darussa masu wahala na ayyukan kasashen yamma.

‘Littatafan makaranta da aka wallafa da sauri, a yanzu za su bi hanyar kafar talabijin ta Rasha,’’ in ji Katsva.

Wata yarinya a Ukraine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iyaye na cikin damuwar rasa hakkinsu na iyaye idan suka bar 'ya'yansu yin karatu da manhajar Ukraine

"Wannan hujja ce mai karfi da ke nuna cewa fadar Kremlin na amfani da ilimi a matsayin makamin farfaganda", a cewar Dmytro da ke garin Melitopol.

Sai dai, yana fatan cewa duk da samun damar manhajar koyarwa ta harshen Rasha ta intanet, yara daga yankin za su iya koyo kan lamurra da kuma fahimtar ainihin tarihin Ukraine.

"Yaranmu suna yawan tambaya a kan me ya sa aka saka tutocin wata kasa cikin makarantunsu.

Me zan iya cewa…ko da yaro dan shekara shida ya fahimci cewa hakan ba daidai ba ne.''