Me ya sa ɗaiɗaikun mutane ke fin jam'iyya ƙarfi a siyasar Najeriya?

…

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Asabar da ta gabata ne jam'iyyar NNPP a Kano ta kora ɗanmajalisa mai wakiltar mazaɓar Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin daga jam'iyyar bayan zarginsa da karya dokokinta.

Shi ma dai ɗanmajalisar ya bayyana amincewarsa da koron, duk da ya ce ba a masa adalci ba, domin a cewarsa ba a ba shi damar kare kansa ba, kamar yadda dokoki suka tanada, sannan ya ce nan gaba kaɗan zai sanar da inda zai koma domin ci gaba da gudanar da harkokin siyasa.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin siyasar Najeriya tana ɗaukar wani irin salo, wanda wasu ɗaiɗaikun mutane ne suke juya akalar jam'iyyun, maimakon yadda aka saba a gani a lokutan baya.

A ƙasar, wadda ake yi wa kallon giwar Afirka, za a iya cewa kowace jam'iyya tana da wani jigo da ake ganin yana riƙe da mafi yawan ƙarfin iko a cikinta, wanda yawanci yadda ya dama haka za a sha.

Wannan ya sa wasu suke tambayar shin me hakan yake nufi ga ci gaban dimokuraɗiyar ƙasar?

Me ya sa haka?

A game da abin da ya sa hakan ke faruwa, BBC ta tuntuɓi Dokta Kabiru Sa'id Sufi, malami a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami'a da ke Kano kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, wanda ya ce akwai ƴan siyasar da suke ganin su ne gata ga jam'iyyar, ba ita ce take musu gata ba.

Ya ce, "akwai mutanen da wataƙila su ne suke ba jam'iyyar tagomashi, to irin waɗannan mutanen gani suke yi su ne suke yi wa jam'iyar alfarma ba ita take musu alfarma ba."

Sufi ya bayyana wasu abubuwa da ya ce yana ganin su ne suke sa ƴansiyasar suke tunƙaho kamar haka:

  • Tarin dukiya
  • Yawan magoya baya
  • Muƙami

Ya ce waɗannan su ne abin da ake gani a zahiri a siyasar ƙasar, "har suke ganin sun fi ƙarfin jam'iyyar duk da cewa ba haka ya kamata ba."

Ya ce waɗannan abubuwan sun sa wasu ƴansiyasar suna ganin jam'iyar ba za ta iya tursasa su ba, sai dai a lallaɓa su.

"Wani lokacin kuma sun dade a siyasar sai suke ganin duk jam'iyyar da suka shiga tamkar sun motsa ta ne."

Me hakan ke nufi?

A game da abin da ƙarfin ɗaiɗaikun ƴansiyasar ke nufi ga dimukuraɗiyya, Sufi ya ce koma-baya ne sosai ga dimukuraɗiyya domin a cewarsa hakan ya fita daga tsarin daidai.

"Komai da aka yi a dimukuradiyya an yi ne domin ya tafi da tsari mai kyau. Shi ya sa ake yi wa jam'iyya kallon uwa, amma idan aka juya, sai ya zama ta zama ta koma ƴa, to lallai za a lalata dimokuraɗiyya domin da doron jam'iyya ne ake mulki, da ita ake hamayya kuma da ita ake kare muradun ƴanƙasa."

Ya ƙara da cewa idan ya kasance jam'iyya ba ta da ƙarfin da za ta iya waɗannan abubuwan, "to zai kasance dimukuraɗiyyar ta samu cikas saboda abubuwa da yawa da kamata jam'iyyun su yi, ba za sa iya yi ba."

Ladabtar da ƴaƴan jam'iyyar

Babban abin da ya sa dakatar da ƴansiyasa ke jan hankali shi ne maganar ladabtar da su idan sun aikata abubuwan da ake gani sun karya dokokin jam'iyyar da ta ba su takara.

Sai dai Sufi ya ce maganar ladabtar da ƴaƴan jam'iyyar tana da wahalar gaske, saboda a cewarsa, "za su iya ladaftar da su ne idan ya kasance jam'iyyar ce take musu gata, amma idan ya kasance ƴan siyasar ne suke ganin suna yi wa jam'iyyar gata, to ai ta rasa wannan damar ta yi wa ƴaƴanta ɗin ladabi. Hsalima gani suke idan suka fice, jam'iyar ce ta yi asara, ko kuma za su iya komawa wajen abokiyar hamayyarta."

Me ya kamata a yi?

Ganin yadda lamarin ya daɗe yana ci wa jam'iyya tuwo a ƙwarya, Kabiru Sufi ya ce komawa ga asalin tsari ne zai magance matsalar.

Ya ce daga cikin tsare-tsaren da yake ganin za su kawo sauƙin lamarin, "akwai tsari da ya kamata jam'iyyu su yi ta yadda idan aka kora ɗansiyasa, duk inda ya koma kar a karɓe shi, ko kuma su gindaya masa sharuɗa. Amma idan mutum ya san idan ya fice daga wannan jam'iyar, duk abin da ya yi, idan ya koma wata jam'iyyr za a karɓe shi, za su yi ta aikata haka."

Masanin na siyasa ya lissafa wasu abubuwa da yake ganin idan aka yi jam'iyyu za su iya dawowa da tagomashin su.

  • Jam'iyyu su fahimce cewa sun samu naƙasu
  • Hukumomin zaɓe su taimaka musu
  • Su yi yarjejeniya hana karɓar wanda aka kora a wata jam'iyya
  • Su yi aiki tare wajen ƙwatar ƙarfin su
  • Al'ummu su taimaka musu