Gaske ne APC ce ke yi wa jam'iyyun adawa maƙarƙashiya?

Jam'iyyun adawa a Najeriya
Lokacin karatu: Minti 3

Jam'iyyun hamayya na Najeriya na alaƙanta rikicin da ke addabar jam'iyyun na cikin gida da irin matakan yi musu maƙarƙashiya da jam'iyya mai mulki ta APC ke ɗauka.

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP da takwarorinta NNPP da LP na fama da rikicin cikin gida kan jagoranci, inda ɓangarorin jam'iyyun daban-daban ke iƙrarin su ne halastattun jagoron jam'iyyun.

Misali, jam'iyyar PDP na fama da rikicin jagoranci dangane da wane ne halastaccen shugaba da sakataren jam'iyyar, inda ɓangarorin biyu da ke rikici ke ta buga shari'a.

Umaru Damagum wanda makusancin tsohon gwamnan jihar Rivers ne kuma ministan Abuja, Nyesom Wike da abokan hamayya ke zargi da yunƙurin raba kan jam'iyyar ta PDP.

Ita ma jam'iyyar LP ta Peter Obi na fama da nata rikicin kan wane ne halastaccen jagoran jam'iyyar.

Hakan ne ya sa jam'iyyun adawar ke ɗora alhakin gwara kan ƴan jam'iyyun ga jam'iyyar APC mai mulki.

Da me jam'iyyun hamayya suka dogara?

Tinubu

Dr Tanko Yunusa na jam'iyyar LP ya ce su sun gamsu cewar jam'iyya mai mulki ta APC ce ke gwara kan ƴan jam'iyyun hamayya domin ka da kansu ya haɗu su ƙalaubalanci jam'iyyar a nan gaba.

"Haɗa kanmu ya zamar mana abu mai wuya. Mun kasa fahimtar juna kuma sai ya zama kafar da ajam'iyya mai mulki za ta shigo ta ƙara (rura wutar da take ci) a cikin jam'iyyun." In ji Dr Tanko Yunusa.

Ko a kwanakin baya ma sai ƴan jam'iyyar NNPP ɓangaren sanata Rabi'u Musa Kwankwaso suka yi irin wannan zargin na cewa jam'iyyar APC ce ta kitsa wa ɗaya ɓangaren da ke jayayya da tsagin Kwankwasiyya ya dakatar da Rabi'u Musa Kwankwaso.

To sai dai ita ma jam'iyya mai mulkin ta APC ta taɓa yin irin wannan zargi lokacin da ƴan jam'iyyar a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano suka sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje. APC ta ɗora alhakin al'amarin kan jam'iyyar NNPP.

Martanin jam'iyyar APC

Jam'iyyar APC mai mulki ta sha musanta zarge-zargen da jam'iyyun masu hamayya ke yi mata na zama kanwa uwar gami wajen kitsa musu rashin zaman lafiya.

Malam Bala Ibrahim shi ne sakataren yaɗa labaran jam'iyyar ta APC kuma ya bayyana zarge-zargen da ihu bayan hari.

"Babu dalilin da zai sa mu muna kan mulki amma mu ci gaba da haddasa musu fitina a cikin jam'iyyunsu. An riga an kada su saboda haka mutumin da ka fi ƙarfin sa har ka kada shi to mene ne kuma za ka bi ka rinƙa tattaka shi,

Su dai nemi inda matsalarsu take a wani wuri can domin sanin yadda za su sasanta a tsakaninsu in kuma ba za su iya adawa ba su ɗaga hannu su ce ba za su iya adawa ba." In ji Bala Ibrahim.

Ra'ayin masana siyasa

Farfesa Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa ne kuma malami a jami'ar Abuja ya ce akwai ƙanshin gaskiya a irin waɗannan zarge-zarge sai dai kuma ya ce ba yau farau ba.

Ya ce an yi wa jam'iyyar PDP irin waɗannan zarge-zarge lokacin tana kan mulki, inda aka zarge ta yamutsa zaman lafiyar jam'iyyun adawa na lokacin irin su APP da APGA da AD da sauransu.

"An rinƙa kai ruwa rana tsakanin manya-mayan ƴaƴansu har daga ma jam'iyyun ba su kai labari ba. To muddin rigingimun da ke cikin jam'iyyar PDP da NNPP da LP suka ci gaba to su ɗin ma sannu a hankali za su ɓalɓalce ba za su kai labari ba saboda ai sai jam'iiyun sun zama tsintsiya ɗaya maɗaurinki ɗaya sannan za su samu nasara." In ji farfesa Kari.

Hakan ne kuma ya sa ƴan Najeriya da dama tunanin cewa da wuya jam'iyyun da hamayya su iya taɓuka wani abun a zo-a-gani a kakar zaɓen 2027, bisa la'akari da irin rashin kataɓus ɗin jam'iyyun ta fuskar yin hamayya da jam'iyya mai mulki.