Wasu gwamnonin Arewa sun musanta rahoton karɓo bashi

...

Asalin hoton, other

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ba ta ciyo rancen kuɗi naira biliyan 14.26 ba, sai dai kuɗin wani ɓangare ne na kuɗaɗen da gwamnatin da ta shuɗe ta ciyo na naira biliyan 20.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce gwamnati ba ta ci wani bashi a gida ko waje ba tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal.

A makon jiya ne hukumar kula da basuka ta Najeriya ta fitar da rahoto game da gwamnonin da suka ci bashi a cikin wata shida.

Rahoton ya ce sababbin gwamnonin jihohi 13 na ƙasar ciki har da Kano, da Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna sun ci bashin naira biliyan 226 daga masu bayar da bashi a ciki da wajen ƙasar, bayan rantsar da su a watan Mayun 2023.

Hukumar ta kuma ce ta haɗa alƙaluman ne bayan jimillar lissafin da suka yi kan farashin dala a kan naira 889.

Amma gwamnatin jihar Zamfara ta musanta hakan inda ta ce, "Muna so mu fayyace rahoton ofishin kula da basuka (DMO) cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ciyo bashin Naira biliyan 14.26.

"Gwamnatin jihar Zamfara ba ta taɓa neman buƙatar karɓar rance ba ko tuntuɓar majalisar jiha ko ta ƙasa domin neman wannan buƙata," in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce ya kamata jama'a su gane cewa gwamnatin baya ce a jihar ta ciyo bashin kuɗin na naira biliyan 20, amma ta ƙasa karɓar kuɗaɗen duka.

“Gwamnatin da ta gabata ta karbi naira biliyan 4 daga cikin rancen biliyan 20 da aka nema domin aikin filin jirgin sama na Zamfara, duk da cewa ba a yi amfani da kuɗaɗen ba.

“Bayan da muka shigo ofis, mun gano cewa sharuɗan biyan kuɗin ya sa kawo karshen yarjejeniyar ba zai yiwu ba ba tare da ya jawo babbar asara ga jiha ba," in ji sanarwar.

Sokoto fa?

Gwamnan Sokoto

Asalin hoton, Ahmed Aliyu Facebook Page

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu shi ma ya musanta bayanan da ke ƙunshe a cikin rahoton hukumar kula da basussuka ta Najeriya cewa gwamnatinsa ta ƙarɓi bashin kimanin naira biliyan 89 a cikin gida da kuma kusan dala miliyan talatin da bakwai daga waje.

Gwamnan ya ce bai ci bashin ko sisin kwabo ba a cikin wata goman da ya yi yana gwamna, "Ko tsakanin mutum da mutum za a ƙarbi bashi akwai yarjejeniya balle bashin da ya shafi gwamnati, kuma ana bin dokar zuwa majalisa kafin a anso bashin amman mu ba mu yi ko wanne ba."

Alhaji Ahmed Aliyu ya ce rahoton ƙarya ne bai da asali bai da tasiri, kuma yana kira ga dukkan wanda ya ce ya ci bashi ya zo ya bada shaidar hakan," Idan ma an yi domin a ɓata mani suna ne, hakan bai shiga ba saboda a matsayina na gwamnan jihar Sokoto tun lokacin da na anshi mulki ina biyan albashi 18 ko 19 ko 20 ga wata."

Gwamnan ya bayyana cewa ba wai yana nufin ba zai ci bashi a nan gaba ba, amman dai a halin da ake ciki bai ci bashi ba, kuma babu wani dan kwangila da ke binsu bashi.

Alhaji Ahmed Aliyu ya shaida wa BBC cewa zai dauki mataki kan rahoton da aka yi masa ƙazafi. "Abin da muke samu da shi muke amfani muna yin abubuwan da suka kamata.

Rahoton da hukumar ta fitar ya ce gwamnan jihar Sokoto ya ciyo bashin dala miliyan 125.1 daga waje.

A shekarar 2023 gwamnonin Najeriya sun sami kason rabon arziƙin ƙasa da ya fi kowanne yawa da ya ɗara na shekara 7.

Wanda ƙaruwar rabon arzikin na ƙasa ga sassan mulkin ƙasar uku, ya faru ne biyo bayan cire tallafin man fetur ɗin ƙasar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi.

Wani ƙwarya-ƙwaryan nazari ya nuna cewar a 2023 gwamnoni sun sami kason rabon arzikin kasa mai yawa da ya kai naira biliya 627 a cikin watan Satumbar bara, sai watan Disamba da suka sami naira biliyan 610, sai Agusta da suka sami naira biliyan 555, sai Nuwamba da suka sami naira biliyan 533, yayin da a watan Yulin 2023 din suka sami naira biliyan 514, sai watan Oktoba 497.

Martanin jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ita ma ta musanta rahoton Hukumar kula da basusuka ta Najeriya inda ta ce gwamnatin jihar ba ta ciyo bashin ko sisin kwabo ba.

Kwamishinan kuɗi na jihar Katsina Bashir Tanimu a tattaunawarsa da BBC ya ce gwamnatinsu ba ta ciyo wani bashi ba kuma iya bashin da suka san an ciyo a jihar shine wanda gwamnatin da suka gada ta ciyo a cikin watan Maris ɗin 2023.

"Tun daga watan Mayun da aka rantsar da gwamnan jihar mu har ya zuwa yanzu, a matsayina na kwamishinan kudi na jihar, bai ciyo bashin ko da na sisin kwabo ba daga ko wane banki ko kuma daga gwamnatin tarayya"

"A wannan lokaci ne hukumar kula da basusukan Najeriya ta bayar da alƙaluman cewa ga adadin bashin da yake a ƙarƙashin jihar Katsina wanda waccen gwamnatin da ta shuɗe saboda halin da suka sami kansu na suna buƙatar kuɗaɗe sai suka je suka anso basusuka na gwamnatin tarayya wato na Babban Bankin ƙasar wanda ake cewa 'Excess Crude' na biliyan 10." kwamishinan ya ƙara da cewa.

"Akwai kuma bashin da aka anso na 'CBN salary bail out' na wata biliyan10 sannan kuma akwai 'scoop bonds' waɗanda suka yi wanda sun sami amincewa na biliyan 55 amma kuma abin da suka samu biliyan 31." in ji Kwamishinan.

Kwamishinan ya ƙara da cewa waɗannan basusukan sune wanda wannan gwamnatin ta tarar inda kuma ya ce a kowane wata ana cirewa daga cikin kuɗaɗen da ake ware musu."