Ƴan Afghanistan da ke yaƙi da aƙidar Taliban da suka ce Birtaniya ta ci amanarsu

Nooria
Bayanan hoto, Nooria, wacce ta kasance malamar Ingilishi kafin Taliban ta karbi ikon Afghanistan, ta shiga buya tun bayan da Taliban ta kwace iko

Cikin wata farar jaka ta roba, Ammar na dauke da wasu takardu wadanda mafi yawansu mallakarsa ne.

Sun ja hankalinmu sosai ta yadda sai da muka ziyarce shi a gida, sai da ya zo ya same mu a motarsa a wani wuri na daban, a tsorace yake da tafiyar saboda mayakan Taliban za su iya caje kayansa a wajen duba ababen hawa su iya bankado takardunsa.

Cikin takardun nasa, har da na yarjejeniyar aikinsa da Hukumar Burtaniya a matsayinsa na malami na tsawo shekara biyu, da dai wasu sauran shaidu da za su tabbatar da alaƙarsa da Burtaniya, amma ya riƙa fatan kai wa ga tudun mun tsira shi da iyalansa.

Ana fargabar abin da zai iya faruwa da rayuwarsa saboda aikinsa da gwamnatin Burtaniya.

“Muna koyar da al’adun Burtaniya a nan Afrghanistan. Bayan yaren Turanci da muke koyarwa.

"Muna koyar da su kan manufofin da Taliban take kai wadanda babu su a addinin Islama, waɗanda haramun ne.

"Shi ya sa suke yi mana kallon dabbobi kuma suke son hukunta mu. Hakan kuma barazana ce a wurinmu,” in ji shi.

A baya Taliban ta taba tsare shi – tsoro ya kama shi yana ganin aikinsa ya jefa iyalansa cikin hadari su ma.

"Sun kama ni suka kai ni ofishin ‘yan sanda suka tambayeni ko ina yi wa gwamnatin kasashen waje aiki.

"Na yi sa’a ba su samu wata shaida ba a gidana da wayata. Amma ba na jin abin ya kare daga nan. Duka bin da nake suna kallo na, sun sanya idanunsu a kaina.

"Amma daya ne daga cikin daruruwan malaman da suka yi aiki da Hukumar Burtaniya, da aikin da ake zuwa a samu mutane har inda suke domin wayar da kai, irin wadanda ake zaton an bari a baya, kuma mafi yawansu mata ne.

Noori ana daga cikin wadanda suka yi aikin koyarwar.

“Ba karamin kalubale ba ne a garemu. Suna da irin tunanin nan na ra’ayin rikau, kuma suna cewa abubuwan da muke koyarwa ba su dace ba.

Duk inda muka je ana mana kallon wakilan gwamnatin Burtaniya.

‘’Wasu na tunanin cewa mu ‘yan leken asirin Burtaniya ne.” In ji ta, kuma hakan bya sanya rayuwarta da ta iyalanta cikin hadari karkashin mulkin Taliba.

'Yan kungiyar Taliban

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mayakan Taliban ke sintiri a kan titunan Kabul, babban birnin Afghanistan, yayin bikin cika shekara daya da kwace iko da Kabul
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayin da kungiyar ta yi sanarwar samar da aminci da tsaro ga duk wanda ya yi aiki da gwamnatin Burtaniya da ƙawayenta a baya, ana samun hujjoji na kisan ramuwar gayya ga mutane.

Majalisar Dinkin Duniya ta samu hujjoji har 160. Nooria ta shiga wasan ɓuya ne tun lokacin da Taliban ta karbe iko a watan Agustan bara.

''Ba karamin abin tayar da hankali ba ne.

Yanayin ya fi na rayuwar fursuna muni. Ba za mu iya tafiya inda muke so ba lokacin da muka ga dama.

Dole sai mun yi ɓadda kama idan muna son fita waje. Abun yana damun rayuwata. Wani lokacin sai in ji kamar yawuwar tawa za ta zo ƙarshe," In ji ta.

Ta zargi Hukumar Burtaniya da nuna bambanci tsakanin ma’aikatanta.

“Sun sauya wa wasu daga cikin ma’aikatasu da ke zaune a ofis-ofis wurin aiki, mu sun barmu a nan. Ba ma su fada mana yaushe za su sauya mana wuri ba.”

Nooria da sauran malamai sun nemi a sauya musu wurin aiki ta hanyar wani tsari da na Burtaniya da ake kira (ACRS) amma har yanzu babu wani abu da suka samu bayan wasu lambobi da aka raba musu.

Duk da cewa Hukumar Burtaniya ta bude wannan kafa ta neman mafaka, sai dai Gwamnatin Burtaniya na bai wa ma’aikatanta na ofis ne wannan dama amma ban da malamai da ma’aikatan kwantaragi.

Sun ce suna ta kokarin samun mafakar daga Gwamnatin Burtaniya.

Ofishin harkokin wajen Burtaniya ya ce ma’aikatan kwantaragi na da damar samun sauyin wurin aikin, karkashin shirin ACRS, ta ce tana ƙoƙarin samar da mafakar cikin gaggawa sai dai har yanzu babu amsa kan bukatunsu da suka tura.

“Ina ganin har sai dan kwantaragi ya mutu za su iya daukar mataki a kai. Sannan za su dauki matakin da ya dace, in ji Ammar.

Ita kanta hanyar tsirar ba ta da tabbas ga ma’aikatan gwamnatin Burtaniya.

Jaffer ya yi aiki a matsayin babban mai bayar da shawar kan aiwatar da ayyukan da manufofin gwamnatin Buratniya a Afghanistan.

Kai tsaye wani kwamfanin Burtaniya – da gwamnatin Buraniya ke daukar nauyi.

Kafin 2021, ya rika fuskantar barazana daga Taliban, lokacin da aka rika kasha fitattun masu aiki da kungiyoyin fararen hula a Afghanistan.

Ya nuna mana sakonnin da ya rika samu, wanda ake zarginsa da leken asiri ga gwamnatocin waje kuma ana yi masa barazanar za a kashe shi saboda “bijirewa addinin Musulunci”.

Tun daga watan Agustan bara, ya sauya wuraren zama har sau bakwai. 

Dubban 'yan Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shekara daya da ya gabata, dubun-dubatar 'yan Afghanistan, sun yi ta turereniya zuwa filin jirgin saman Kabul da nufin tserewa 'ya Taliban da ke son cimmusu

"Ɗana ba shi da lafiya, amma mun kasa bude ko da tagogin motar bas din, saboda mutane da ke kokarin shigowa daga waje za su kutsa cikin motar.

‘Yan Taliban na ta Harbin bindiga a sama. Yarona ya shiga dimuwa bayan ganin abin da ke faruwa.’’

A ranar ne kuma aka kai harin bama-bamai kan filin jirgin sama da ya kashe sama da mutum 180.

A ranar ne kuma shirin kwace mutane na gwamnatin Burtaniya ya kawo karshe, inda Jaffer da iyalansa basu samu damar tsallakawa ba domin barin Afghanistan.

Tun bayan nan, martanin da ya samu daga gwamnatin Burtaniya ita ce bukatar samun shirin ARAP .

"Na yi aiki tare da su. Na saukaka musu. ‘Yan uwanmu ‘yan Afghanistan da ke wajen ba su nuna musu wariya ba ta cewa su ‘yan kasashen waje ne, saboda mun ƙarfafa wa mutane gwuiwa don su bari ayi aikin da aka tsara yi.

Mun gamu da barazana, sannan a yanzu an barni a haka. Bani da wani wuri da zanje a fadin duniyan domin yin rayuwa mai ƙima, ‘a cewarsa cikin muryarsa yana kuka.

"Mece ce makomar ‘ya’yana? ‘Yata ba ta da damar yin karatu. Ina da babban buri a kanta. Shin ‘ya’yana kanana za su zama masu tsassauran ra’ayi?

"Na yi ta tambayar kaina me yasa na kawo su wannan duniyar. Idan wannan ce makomarsu, watakila kar su rayu,’’ a cewarsa.

Mun tattauna da akalla wasu mutum uku da suke aiki da gwamnatin Burtaniya, da suka hada da wani mai fassara da yaje filin daga tare da dakarun sojin ta Burtaniya.

Dukkansu sun bayyana yadda mutane da suka bautawa suka yaudare su.

Dakarun sojin Burtaniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu masu fassara kusan 2,850 da suka yi aiki da dakarun sojin Burtaniya a Afghanistan

Gwamnatin Burtaniya ta ƙwace mutum akalla 15,000 a watan Agustan bara da ƙarin wasu 5,000 tun bayan nan.

Amma dubban mutane na can suna jira, inda suke rayuwa cikin fargaba, kuma da ke maƙale cikin kwangaye da jiran sammanin tsira.

"Na kasance ina alfaharin aiki da gwamnatin Burtaniya,’’ a cewar Nooria.

"Amma a yanzu, na yi nadama. Har ma ina ji da ban musu aiki ba tsawon rayuwata saboda ba su dauki rayukan mu da kuma aikin mu da muhimmanci ba, kuma sun zalunce mu saboda barin mu a baya.’’