Taliban ta tilasta wa matan Afghanistan sanya niƙabi

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Patrick Jackson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
A karon farko cikin gwamman shekaru, matan Afghanistan za su rika sanya nikabi karkashin wata doka da gwamnatin Taliban ta amince da ita.
Duk macen da ta ki bin wannan doka ko ta yi watsi da ita, hukumomi sun yi jan kunnen cewa za a iya daure babban namijin gidansu ko wanda ke lura da ita tsawon kwana uku a gidan yari.
A shekarun 1990 lokacin da Taliban ta karbe iko da Afghanistan, ta saka dokar sanya nikabi a matsayin wajibi.
Amma a wannan karon ba su sanya dokar ba tun bara da suka karbi iko.
Mata da dama a Afghanistan sun saba da sanya nikabi, yayin da wasu kamar mazauna birni ke sanya mayafi da zai rufe musu kansu kawai.
Ma'aikatar hana baɗala da inganta kyawawan ɗabi'u ta gwamnatin Taliban ce ta tabbatar da dokar.
Sai dai jami'an Taliban na fassara dokar a matsayin "shawara" amma kuma sun bayyana hukunci ga duk wanda ya ki bin ta:
- Da farko za a rika ziyarar gidajensu da mazajensu da 'yan uwansu ko iyayensu maza domin a rika tattaunawa da su
- Na biyu, za a rika kiran muharramansu zuwa ma'aikatar
- Na uku, za a dauki maharraman nasu don kai su kotu kuma za a iya daure su a gidan yari tsawon kwana uku
Kur'ani mai girma ya gaya wa Musulmai maza da mata cewa su rika shigar mutunci. Ko ta wane hali maza su yi shigar da za ta rufe al'aurarsu daga cibiya zuwa gwiwa. Mata kuma su rufe duka jikinsu ban da fuskarsu da hannu da tafin kafafuwansu lokacin da suke tare da mazan da ba muharramansu ba.
An ci gaba da wannan muhawarar a Musulunce, kan cewa hijabi ya isa ko kuma sai mace ta sanya nikabi.
Hijabi, shi ne wanda za su sanya ya rufe jikinsu, nikabi kuma ya rufe fuska ban da ido, wani lokacin ma har idon, wani lokacin yana zuwa da abaya.
Mafi yawan dokokin da Taliban ke sanyawa masu tsauri sun fi yawa a kan mata.
Afghanistan ce kasa daya a duniya da ta hana neman ilimi saboda jinsi.
An hana mata zuwa neman ilimin sakandare, an rushe ma'aikatar mata, a wasu yankunan kuma an hana mata da yawa zuwa aiki.












