Mata biyar da Taliban ta kasa rufe bakinsu a Afghanistan

Top artwork
    • Marubuci, Daga Quentin Sommerville
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Mutum-mutumin dusar kankara ne kawai. Amma a yayin da lokacin tsananin hunturu ya abka wa a'lummar kasar Afghanistan da ke fama da matsananciyar yunwa, zubar dusar kankara mai yawa kan samar da farin ciki a wani dan karamin wuri na birnin Kabul.

Wasu matasan mata sun tsaya kusa da mutum-mutumin dusar kankara domin daukar hotunan kan su. A yayin da suke ta annashuwa tare da kallon fuskar wayoyinsu, za su iya kasancewa a ko ina.

Mayakan Taliban uku sun hange su. Sun kuma karaso kusa - matan sun tsere. Cikin murmushi, daya daga cikinsu ya taka kusa da mutum-mutumin dusar kankarar - wanda ma watakila yana tunanin ya saba wa addinin musulunci.

Ya fasa hannayen da aka yi masa da itace, sannan a hankali ya cire idanun da aka yi masa da duwatsu, har ma da hancin. Daga karshe ya datse kan sa cikin sauri.

Ban dade da dawowa birnin Kabul ba bayan shafe shekaru 10 bana nan, kuma tuni wani dan Taliban ya yi min lakca a kan fahimtar al'adun kasar Afghanistan.

Ya yi ikirarin sanin abubuwan da suka fi dacewa da matan Afghanistan.

"Shaidanu masu shudin idanu'' (Yan kasashen Yammaci) sun lalata mana kasa, kamar yadda yake nunawa.

A maimakon na amince da kalamansu gaskiya ne, na bukaci ji daga matan da kan su. Da dama sun boye kan su, duka saboda fargaba game da makomarsu kana wasu kuma saboda rayuwarsu.

Har yanzu akwai mata a kan titunan birnin Kabul, wasu har yanzu sanye da kaya irin na Turawan Yammaci, amma ana cigaba da take musu 'yanci - 'yancinsu na yin aiki, da karatu, da fita zuwa wurare da kuma 'yan rayuwar cin gashin kai.

Na hadu da matan da aka tilasata wa boyewa daga sabuwar Afghanistan, da suka tari aradu da ka wajen bayyana damuwarsu a fili.

Za kuma su iya yin hakan ne ta hanyar boye ko su wanene su - amma ban da Fatima, wacce ta jajirce cewa a nuna fuskarta.

Presentational yellow line

Fatima

Ungozoma, shekaru 44

Fatima artwork

Sau biyu kungiyar Taliban ke haramta wa Fatima cika burin rayuwarta. Lokacin da suka mulki Afghanistan da farko, sun tilasta mata aure lokacin tana da shekaru 14 kuma iliminta ya kawo karshe.

Me yiwuwa wannan karon, ungozama mai shekaru 44 za ta ci gaba da aiki, amma kamar sauran mata da na tattauna da su, rayuwar yau da kullum ta kara lalacewa.

Harkokin karatun Fatima da aiki abubuwa ne masu matukar wahalar cin galaba. Bayan da ta yi aure, ba ta koma karatu ba har sai da ta kai shekara 32.

Lokacin, Taliban ta dade da barin mulki. Amma bai zama wani abu ne mai sauki ba - a lokacin sabuwar gwamnatin dimokaradiya ta Afghanistan.

Ta ce ta yi kwasa-kwasai da dama a cikin ɗan kankanen lokacin da ta samu - amma akwai lokacin da aka haramta mata yin karatu.

"Su kan duba katin shaida ta su ce, '' kin yi tsufa da zama a cikin aji da sauran dalibai.''

Daga bisani ta samu ta karasa karatun digirinta shekaru biyu da suka gabata - amma kuma ta sake fuskantar wani kalubalen.

"Yana da matukar wahala ga budurwa ta samu ilimi a Afghanistan, ka yi tunanin wahalar da mace mai aure ke fuskanta kafin a dauke ta aiki.''

Amma Fatima ta samu nasara kuma tuni ta riga ta karbi haihuwar dubban jarirai.

"Na so yin aiki a yankin da zan iya horar da mata,'' ta ce. ''Idan mace ta samu ilimi, ta kan girmar da lafiyayyu da hazikan 'ya'ya.

Ta hanyar hakan, za ta iya samar da yaro mai amfani a cikin al'umma - wanda zai iya kawo sauyi.''

Fatima sits with her tapestries

Fatima ta amince cewa da alamu mulkin Taliban ya riga ya kafu, amma tana fatan wannan karon za su gudanar da mulkin da ya banbanta da na baya da suka yi.

"Ina cike da fatan cewa Taliban ba ta tauye hakkokin mata na samun ilimi da aiki ba,'' ta bayyana min. ''Idan ba haka ba, suna datse hannun daya daga jikin al'umma ne. Al'ummarmu na da ginshikai biyu,'' ginshikin maza da daya ginshiki na mata, Ta yaya za ka tafiyar da rayuwarka da bangare daya ko hannu daya?"

Fatima ta yi sa'a cewa har yanzu tana aiki. ''Taliban ba za ta iya hana ni aiki a asibiti ba saboda sun san cewa ana bukata,'' ta ce.

Amma an shafe watanni ba a biya ta ba - kana tana dora laifin a kan takukumin kasashen Yammaci, ba Tailban ba.

"Amurka da kasashen Yamma sun toshe hanyoyin samun kudin shiga na Afghanistan," ta ce.

Fatima ta kan yi aikin sa'oi 24, tana karbar haihuwar jarirai da yawansu ya kai 23 a wancan lokacin. Amma babu kudin ciyar da marasa lafiya da ma'aikata.

Kuma tana da sako ga Amurka da kasashen Yamma: '' Takunkumi kan Taliban zai kashe mu cikin sauri fiye da take hakkinmu da Taliban ke yi.

Yarinya na mutuwa saboda yunwa kana uwa ko ta sayar da diyarta saboda yunwa ko kuma daga matsin lambar yi mata auren dole. Batun iliminsu karatunsu ba shi da wani muhimmanci idan suna mutuwa da yunwa.''

Rayuwa, ko shakka babu, ba wai game da aiki ne kawai ba - kuma Fatima na bakin ciki kan abubuwan da ta rasa.

Ta ce ta kan kwanta ido biyu cikin dare cikin damuwa. Gashin kan ta ya fara zubewa saboda shiga damuwa a cikin watanni biyar da suka gabata. Kana akwai wasu sauye-sauye.

Fatima's tapestry artwork

A lokacin da ba ta aiki, ta kan yi sana'ar sake-sake. Ta nuna min wasu daga cikin ayyukanta - da ke nuna wuraren al'adun, kamar gasar wasannin Buzkashi na kasar, inda maza a kan dawakai ke fafatawa don samun cin gasar da matattun dabbobi.

Amma aikinta na baya-bayan nan sun nuna wasu sauye-sauye da dana na watanni kadan da suka gabata.

Akwai zayyanar sake-sake da ke nuna kwashe mata da maza daga filin saukar jiragen sama na Kabul, a cikin kwanaki bayan da kungiyar Taliban ta shiga birnin.

Sauran sun nuna yadda ake sa ido a kan mata da kuma mata sanye burka.

Aikinta, ta ce yanzu Ana mayar da hankali ne kan bacewa a tsakanin alummar Afghanistan - wadanda suka bar kasar, da matan da suka bace daga cikin unguwarsu, da wadanda ba su taba fita daga gidajensu ba.

A baya, Fatima ta koya wa mata dinki - matan da ta ce suna samun kudaden shiga ta sayar da kayayyakinsu.

Amma Taliban na kallon ayyukan zanen a matsayin saba wa addinin Musulunci, kuma wadannan mata na makale a cikin gida.

"Muna shiga bikin baje kolin nuna kayayyaki a ciki da wajen Afghanistan - kuma muna samun riba,'' Fatima ta bayyana, "[wadancan matan] su ke kula da iyalansu.

Presentational yellow line

Ameena

Jami'ar leken asiri, shekaru 29

Ameena artwork

Ga Ameena mai shekaru 29, wuraren gyaran gashi su ne kadan daga cikin damuwarta. Ta ce tana fargaba game da rayuwarta.

A ranar 15 ga watan Agusta, ta fara ranar da ziyartar gofishin Hukumar Lura da Al'amuran Tsaro (NDS), hukumar leken asirin kasar Afghanistan. Ta yi ta kai komo ba dare ba rana a daidai lokacin larduna zuwa larduna na ta fadawa hannun Taliban, tana dawo da dawo da mata jami'an hukumar zuwa tudun-mun-tsira na birnin Kabul.

A can ta rika bas u kudi tare da daukar nauyinsu, kafin da koma helkwatar ta NDS da ke kan hanyar zuwa fillin saukar jiragen sama na Kabul.

"Na samu damar kwashe wa mata jami'an NDS kusan 100 a fadin kasar. Amin mamaki ne a gare ni cewa Kabul ya fada hannun 'yan Taliban,'' ta shaida min lokacin da ta ke kurbar shayi.

"Lokacin da na isa ofis, na ga kowa cikin bacin rai yana tserewa. Na tambaye su inda za su tafi. Sun bayyana min cewa, Madam, don Allah yi sauri kif ice daga ofis - 'yan Taliban sun so.''

Amma Ameena ta sake dawowa kan teburinta ta mayar da abin wasa, saboda yanayin mummunan cunkoson ababan hawan birnin Kabul, ba ta taba tsammani Taliban za su iya zuwa har helkwatar ta NDS ba har sai ya zuwa wayewar gari.

Ta ce, daga bisani ma'aikatan sashen lura da ma'aikata sun zo gare ta kana suka tambaye ta abinda ya kamata su yi saboda duka ma'aikatan na ficewa.''Na tambaye su, 'Ina sauran jami'an?''

Ta fahimci cewa duka sun fice - in baya ga mataimakan kwamandojin biyu.

Daga misalin karfe biyu da rabi na ranar, Ameena ta fice daga gida tare da 'yan rakiyarta dauke da makamai. Ba za sake dawowa helkwatar NDS ba.

A baya dai ta kalli yadda shugaba Ashraf Ghani ministocinsa tare da ministan tsaronsa dashugaban hukumar tsaro ta NDSya bayar da umarnin cewa dole a kare birnin Kabul ko ta halin kaka.

Yanzu a gida, ta gani a akwatin talabijin cewa mayakan Talibann na cikin fadar Shugaban kasa.

Ka da shi ma Shugaba Ghani ya tsere.

Bayan 'yan watanni, ta cigaba da jin bakin cikin cewa ya bar kasar.

Ameena looks out of window

"Abinda ya kamata ya yi shi ne ya jajirce har iya karshen rayuwarsa saboda shi ne shugaba kuma jagoran daukacin dakarun tsaron kasar Afghanistan," ta ce.

"Mutumin da ke jagorantar al'amuran tsaro bai kamata ya tsere ba, kuma dole ya jajirce da rayuwarsa - karshen rayuwarsa a duniya.''

Wayewar gari bayan nan, al'amura sun kasance cikin fargaba. Mayakan Taliban sun kai samame gidanta amma lokacin da riga ta fice saboda tsoron rayuwarta.

Ta bayyana cewa, mayakan Taliban, sun dauke motarta da bidigar da ta bari a gida.

"Mamaki shi ne abin alfahari ga duk wani soja. Abin bakin ciki ne a gare mu lokacin da 'yan ta'adda suka zo suka kwace makamanka.''

Presentational yellow line

Mina

Dalibar Jami'a, shekaru 22

Mina artwork

Mina bata yi wani kira ga kasashen Yammaci ba, sai da wannan: "Ku kyale mu," ta bayyana da karfinta. Bayan shekaru 20 na tallafin kasashen Yammaci a Afghanistan, har yanzu 'yancin mata na fuskantar barazana, ko kafin dawowar Taliban, ta ce.

Mina daliba ce mai kwazo, bayan kammala jarrabawar ''Kankur'' ta kasar "Kankur", wacce dalibai 300,000 suka nema a fannoni 50,000 places a jami'a.

Bayan shekaru shafe shekaru hudu tana karatu, wata guda kacal ya rage mata ta kammala lokacin da Taliban ta shigo.

Ta ce a ''cikin sa'oi kadan'' makomarta ta gamu cikas. Ba za a sake samun wata diploma a jami'a ba.

Mina na da burin zama jami'ar diplomasiyya kamar saura, kuma watakila ta kara karatu a jami'ar Oxford.

Amma kuma bauta wa kasar Afghanistan shi ne zai kasance mafi muhimmanci.

"Muddin babu ilimi, ayyukanmu za su kasance da ayar tambaya da rashin tabbas. Ba mu da wata makoma mai kyau,'' ta ce.

Mina ta tunatar da cewa ko kafin dawowar Taliban, Afghanistan na kokarin dakile duk wani abu da ya shafi 'yancin mata.

Ta girma a karkashin mulkin dimokaradiyya na Afghanista, amma har yanzu tana cewa dole sai tana fafutikar samu karamin 'yanci.

"Dangi da 'yanuwa da dama sun bayyana min cewa karatu a fannin kimiyyar siyasa da kuma shar'ia bai dace da 'yanmata ba.''

Ga Mina, da saura dubban daruruwa kamar ta, duka wadannan nasarorins sun gushe cikin lokaci daya. Tana shafe kusan lokutanta a cikin daki tana aiki kan rubuce-rubucenta.

Mina's identity has been disguised

Duk da cewa abubuwan da ta bayyana masu cike da sarkakiya ne, ta kuma ce yanzu cin zarafi ya ragu a kan titina yanzu da yake Taliban wadanda suka kayi kaurin suna wajen cin zali da yanke hukunci kai tsaye, suna kan mulki.

Amma duk da haka, har yanzy ta damu game da fita waje. Mata da dama sun ce suna fargabar cewa za a ci zarafinsu a wuraren bincike na Taliban, kan rashin lullbe jikinsu da hijabi, ko kuma tafiya ba tare da wani muharrami ba.

An kuma zargi Taliban da bincika wayoyin salular mata don duba wasu abubuwa da suka dauka ba su dace ba.

Hana wa mata samun ilimi zai haifar da mummunan tasiri na tsawon lokaci, amma cire su daga wuraren aiki - kamar yadda Taliban suka yi - ana jin sa a jiki ba tare da bata lokaci ba a yayin da Afghanistan ke fuskantar tashe-tashen hankulan da ke shafar al'umma. Mata da dama su ne ke daukar nauyin lyalansu.

Presentational yellow line

Zahra & Samira

Mata 'yan sanda, shekara 34 da 36

Zahra & Samira

Jami'an 'yansandan biyu Zahra da Samira, sun san juna tun suna yara. Suna wasa da dariya tare kana sun nuna min yadda suke atisayen koyon harbo a wani filin horar da harbin. Akasarin harbin a tsakiya ne.

Tallafin Amurka ya yi matukar fadada yawan adadin matan da ke shiga aikin 'yansanda da soja. Amma yanzu tallafin kudin ya kau bayan tawagar karshe ta dakarun Amurka suka fice daga kasar.

Zahra ta cigaba da kasancewa a wurin aikinta har ya zuwa lokacin da lardin Laghman na gabashin Kabul ya fada hannun Taliban.

Lokacin da mayakan Taliban suka takura rundunarsu, ta yi tunanin tserewa da rayuwarta.

"Ba mu fahimci ko muna zaune a kasarmu ne ko kuma a wani wuri daban bane,'' ta ce.''

Yanzu akwau matukar wahala. Kamar b azan iya numfashi ba. 'Yayana na zuwa makaranta, da kwasa-kwasai a jami'oi, amma ba a yanzu ba.

Ta ce matsalolin tattalin arziki na kara ta'azzara a kullum. '' Mun makale a cikin gida babu aikin yi kuma babu samun kudin shiga na tallafa wa rayuwarmu.''

Kana mata sun raa fiye da abin da ya saba shigowa hannunsu.

Lokacin da ta keg yada kai da ken una yarda da abinda kawarta ta fada, Samira ta ce: '' Na sama shawo kan manyan matsalolin rayuwata, amma ban da yanzu.

Na kan je makarantar 'yata in taka cikin walwala a wuraren shakatawa cikin alfahari. Ina da kudi, na karfinn sayen abubuwa, kana na kan iya gabatar da kai na a wurin jama'a cikin alfahari - amma ban da yanzu. Na rasa ko ni wacece yanzu.''

Samira ta tuna baya a lokacin da kungiyar Tailban da kwace mulki - lokacin da ta zauna shiru a wani lungun saman dakinta a birnin Kabul tana kallon jiragen saman a tashi sama, suna daukar mata da maza 'yan kasarta zuwa tudun mun tsira.

Zahra and Samira

Zahra ta bayyana watannin a matsayin kamar a ce ''bakin inki da aka watsa a kan farin abu.''

Mata na cikin razana. Dari-dari a duk lokacin da sabbib mutane suka shigo unguwarsu. Taliban ta yi ikirarin yin afuwa fa wadanda suka yi aiki tare da tsohuwar gwamnati. Amma kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana da sahihan bayanai cewa an hallaka mutane fiye da 100 da suka yi aiki da gwamnatin da ta shude tun bayan da Taliban ta karbi mulki.

Alia Azizi, wata jami'ar 'yansanda kuma shugabar gidan yarin mata, ta yi batan dabo har na tsawon watanni hudu.

Ba a sake ganinta ba tun bayan da jami'an gwamnatin Taliban suka kiranyo ta aiki. Wani gangamin shafukan sada zumunta #FreeAliaAzizi ya yi kir da a sako ta.

Kana cikin wannan mako, an sako mata uku da suka yi batan dabo tare da iyalansu bayan sun halarci wani gangami kan 'yancin mata a birnin Kabul.

Presentational yellow line

Godiya ga wadanda suka tsara aikin

Mai ɗaukar rahoto: Quentin Sommerville

Edita:: Kathryn Westcott

Ci gaban shiri : Paul Sargeant da Dominic Bailey

Tsarawa: Joy Roxas and Prina Shah

Development: Zoë Thomas and Becky Rush

Zane-zan-: Klawe Rzecz

Ɗaukar hoto : Dave Bull