Dukkan cefanen 'yan wasa da aka yi a Premier League a bana kawo yanzu

EPL Summer Transfer

Asalin hoton, Getty Images

Ranar 5 ga watan Agusta za a fara kakar wasan Premier League ta 2022/23, inda za a fara da kece raini tsakanin Crystal Palace da Arsenal a Selhust Park.

Tuni kungiyoyi 20 da za su fafata a kakar bana suka daura aniyar yadda za su taka rawar gani a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.

Wasu da dama sun sayo sabbin 'yan wasa don kara bunkasa kwazonsu, yayin da wasu suka buga wasannin sada munta.

A bana Nottingham Forest wadda rabon da ta buga Premier League tun bayan shekara 23, ita ce kan gaba da ta dauki yan kwallo 13 kawo wannan lokacin.

Leicester City ce kawo yanzu ba ta sayi dan kwallo ko daya ba, watakila ta dauka nan gaba.

Ranar Asabar Liverpool ta doke Manchester City 3-1 ta lashe Community Shield, daga nan an buga gangar tunkarar kakar bana kenan.

Manchester City ce ta lashe Premier League a 2021/22 da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool a ranar karshe da aka rufe wasannin.

Jadawalin makon farko a gasar Premier League ta bana:

Ranar Juma'a 5 ga watan Agusta

Crystal Palace da Arsenal

Ranar Asabar 6 ga watan Agusta

Fulham da Liverpool

Leeds United da Wolverhampton Wanderers

Newcastle United da Nottingham Forest

Tottenham da Southampton

Bournemouth da Aston Villa

Everton da Chelsea

Ranar Lahadi 7 ga watan Agusta

Manchester United da Brighton

Leicester City da Brentford

West Ham da Manchester City.

AFC Bournemouth

Ryan Fredericks (West Ham) Joe Rothwell (Blackburn) Marcus Tavernier (Middlesbrough) 

Gabriel Jesus

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Arsenal ta kamma daukar dan kwallon tawagar Brazil, Gabriel Jesus, daga Manchester City kan fam miliyan 45, bisa yarjejeniya mai tsawo.

Dan wasan, mai shekara 25, ya zama na hudu da Mikel Arteta ya dauka a bana, bayan Fabio Vieira da Matt Turner da dan wasan Brazil, Marquinhos.

Arteta, wanda ya yi aiki tare da Jesus a lokacin da ya yi mataimin Pep Guardiola a Manchester City na kokarin daukar mai cin kwallaye, bayan da Alexandre Lacazette da Pierre-Emerick Aubameyang suka bar kungiyar.

Jesus, wanda zai sa riga mai lamba tara a Gunners ya bar City, bayan kaka biyar da rabi da ya yi a Etihad.

Ya yi wasa 236 da cin kwallo 95 da lashe Premier League hudu da League Cup uku da FA Cup.

City wadda ta dauki Premier League a kakar da ta wuce ta sayar da Jesus ne, bayan da ta dauko dan kwallon Norway, Erling Haaland daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 51.2 a watan Yuni.

Jesus ya bayar da kwallo takwas aka zura a raga a Manchester City a kakar 2021-22, wanda ya yi kan-kan-kan da Kevin de Bruyne a wannan bajintar.

'Yan wasan da Arsenal ta dauka kawo yanzu

Marquinhos (Sao Paulo) Fabio Vieira (Porto) Matt Turner (NE Revolution) Gabriel Jesus (Man City) Oleksandr Zinchenko (Man City) 

Aston Villa

Philippe Coutinho (Barcelona) Boubacar Kamara (Marseille) Diego Carlos (Sevilla) Robin Olsen (Roma) Rory Wilson (Rangers) Ludwig Augustinsson (Sevilla) aro Ewan Simpson (Hearts) 

Max Dickov Max Wilcox (Bolton) Aaron Hickey (Bologna) Keane Lewis-Potter (Hull) Kyreece Lisbie (bai da kwantiragi) Thomas Strakosha (Lazio) Yehor Yarmoliuk (Dnipro) Ben Mee (Burnley) Michael Olakigbe (Fulham) 

Brighton & Hove Albion

Julio Enciso (Libertad Asuncion) Benicio Baker-Boaitey (Porto) Simon Adingra (Nordsjaelland) 

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta tabbatar da kammala daukar dan kwallon Ingila, Raheem Sterling daga Manchester City kan fam miliyan 50.

Sterling, mai shekara 27, ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyar a Stamford Bridge.

Tun da sanyin safiya dan kwallon tawagar Ingila ya yi ban kwana da 'yan wasa da ma'aikatan Etihad ta kafar sada zumunta.

''Na koma Manchester City ina da shekara 20. Yanzu ni cikakken mutun ne,'' in ji Sterling.

''Zan dade ina tuna lashe kofi 11 a kaka bakwai a Etihad har tsawon rayuwata.

City ta dauki Sterling daga Liverpool kan fam miliyan 49 a 2015.Ya kuma ci wa kungiyar Etihad kwallo 131 a wasa 339 da lashe Premier League hudu.

Sterling wanda ya buga wa Ingila wasa 77, zai zama na farko da Chelsea ta saya abana, tun bayan da attajirai suka sayi kungiyar karkashin jagorancin, Todd Boehly.

Kociyan Chelsea na fatan kara karfin gaban kungiyar, bayan da Romelu Lukaku ya sake komawa Inter Milan, wadda zai yi wa wasannin aro kaka daya.

Dan kwallon Belgium, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a Stamford Bridge mai 15 a raga a dukkan fafatawa, sai Kai Havertz mai 14 da Mason Mount mai 13.

Tun bayan da Pep Guardiola ya zama kociyan City a 2016, Sergio Aguero ne kan gaba a cin kwallaye a kungiyar mai 124, sai Sterling da ya ci 120.

Sterling ya zura kwwallo 13 a wasa 30 a gasar Premier League da aka kammala a kakar da ta wuce da daukar lik kuma kofi na 11 jumulla da ya lashe a Etihad.

'Yan wasan da Chelsea ta saya a bana

Eddie Beach Raheem Sterling (Man City) Kalidou Koulibaly (Napoli) Omari Hutchinson (Arsenal) 

Crystal Palace

Malcolm Ebiowei (Derby) Sam Johnstone (bai da kwantiragi) Cheick Doucoure (Lens) Cormac Austin Chris Richards (Bayern Munich) 

James Tarkowski (Burnley) Ruben Vinagre (Sporting) aro Dwight McNeil (Burnley) 

Joao Palhinha (Sporting) Kristian Sekularac (Juventus) Callum McFarlane Andreas Pereira (Man Utd) Manor Solomon (Shakhtar Donetsk) Kevin Mbabu (Wolfsburg) 

Leeds United

Brenden Aaronson (RB Salzburg) Rasmus Kristensen (RB Salzburg) Marc Roca (Bayern Munich) Darko Gyabi (Man City) Tyler Adams (RB Leipzig) Luis Sinisterra (Feyenoord) Sonny Perkins 

Leicester City 

Ba ta dauki dan wasa ko daya ba

Darwin Nunez

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta kammala cinikin dan kwallon tawagar Uruguay, Darwin Nunez daga Benfica kan yarjejeniyar kaka shida kan fam miliyan 64.

Mai shekara 22 zai zama mafi tsada da kungiyar ta saya a tarihi, idan aka hada da kudin tsarabe-tsarabe da zai kai fam miliyan 85 jumulla.

Nunez ya ci kwallo 34 a wasa 41 da ya yi wa Benfica a kakar da aka kammala.

Wanda Liverpool ta dauka da kudi da yawa a tarihi, shi ne Virgil van Dijk, kan fam miliyan 75 daga Southampton a 2018.

Kudin da aka sayo Nunez zai karu zuwa fam miliyan 85, idan har zai ke buga wasa a koda yaushe.

Kudin karin tsarabe-tsarabe ya kunshi kwallo nawa zai ci da idan Liverpool ta dauki Champions League.

Komawar dan kwallon zuwa Liverpool ya danganci samun takardar izinin taka leda a Ingila.

Nunez, wanda ya ci wa Uruguay kwallo 11, ya zura 26 a raga a karawa 28 a babbar gasar tamaula a Portugal a 2021-22 - guda 25 da ya ci da shi aka fara wasa.

Ya kuma ci shida a fafatawa 10 a Champions League da aka karkare, har da wadanda ya zura a ragar Liverpool a karawa gida da waje a kwata fainals cikin watan Afirilu.

Liverpool ta lashe Carabao Cup da FA Cup a kakar da ta kare ta kuma yi ta biyu a Champions League, bayan da Real Madrid ta dauki na 14 jumulla.

'Yan wasan da Liverpool ta dauka a bana

Fabio Carvalho (Fulham) Darwin Nunez (Benfica) Calvin Ramsay (Aberdeen)

Manchester City

Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images

Erling Haaland ya ce yana "wurin da ya dace da zai cika burinsa" bayana Manchester City ta kammala sayen sa daga Borussia Dortmund a kan £51.2m.

Dan wasan mai shekara 21 ya zura kwallo 86 a wasanni 89 da ya buga wa Dortmund kuma ya isa City ne a matsayin daya daga cikin 'yan wasan gaba da suka fi zura kwallo.

Ya sanya hannu a kan kwangilar shekara biyar zuwa 2027 kuma zai je kungiyar ranar 1 ga watan Yuli.

A watan Mayu ne dan kasar ta Norway ya kulla yarjejeniya da City.

United ta haƙura da Haaland, Barcelona da Tottenham na rububin Jonathan

A baya dai kungiyoyin da ke buga gasar La Liga Real Madrid da Barcelona sun nemi daukar Haaland kafin ya yanke shawarar yin aiki da Guardiola.

Haaland ya zura kwallaye 92 a gasar lig a wasa 121 jimilla da ya buga wa Molde, Red Bull Salzburg da kuma Dortmund.

'Yan wasan da Manchester City ta dauka

Erling Haaland (Dortmund) Stefan Ortega Moreno (bai da kwantiragi) Kalvin Phillips (Leeds) 

Manchester United

Lisandro Martinez

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta kammala daukar dan kwallon tawagar Argentina, mai tsaron baya Lisandro Martinez daga Ajax kan fam miliyan 57.

Kociyan United, Erik ten Hag ya yi murna da daukar dan kwallon mai shekara 24, wanda ya saya a lokacin yana horar da Ajax a 2019.

Ya koma Old Trafford kan kwantiragin kaka biyar da zai kare a karshen 2027 da yarjejeniyar za a iya tsawaitata zuwa kaka daya idan ya taka rawar gani.

Martinez ya yiwa Ajax wasa 120 tun bayan da ya koma Netherlands da taka leda daga kungiyar Argentina, Defensa y Justicia kan fam miliyan 6.3 a 2019, ya kuma taka leda a Newell's Old Boys.

Ya buga wa Argentina wasa bakwai tun lokacin da ya fara taka mata leda a Maris din 2019.

Ya kuma buga mata wasa a 2021 a gasar Copa America da kasar ta lashe a Brazil.

Martinez ya taka leda karkashin Ten Hag a Ajax ya kuma dauki Eredivisie a kungiya a 2021 da kuma 2022 da daukar Dutch Cup a 2021.

Shi ne kuma fitatcen dan wasan Ajax da ya taka rawar gani a kungiyar a kakar 2021-22.

Dan kwallon Argentina shi ne na uku da United ta saya a bana, bayan Christian Eriksen da Tyrell Malacia.

Haka kuma United tana ta kokarin daukar Frenkie de Jong daga Barcelona.

'Yan wasan da Manchester United ta dauka

Tyrell Malacia (Feyenoord) Christian Eriksen (bai da kwantiragi) Lisandro Martinez (Ajax) 

Newcastle United

Alex Murphy (Galway United) Nick Pope (Burnley) Matt Targett (Aston Villa) Sven Botman (Lille) Charlie McArthur (Kilmarnock) 

Nottingham Forest

Ryan Hammond (Millwall) Taiwo Awoniyi (Union Berlin) Dean Henderson (Man Utd) aro Giulian Biancone (Troyes) Moussa Niakhate (Mainz) Omar Richards (Bayern Munich) Neco Williams (Liverpool) Wayne Hennessey (Burnley) Brandon Aguilera (Alajuelense) Harry Toffolo (Huddersfield) Lewis O'Brien (Huddersfield) Jesse Lingard (bai da kwantiragi) Orel Mangala (Stuttgart) 

Alex Iwumene (Sutton) Gavin Bazunu (Man City) Mateusz Lis (Altay) Armel Bella-Kotchap (Bochum) Romeo Lavia (Man City) Joe Aribo (Rangers) Sekou Mara (Bordeaux) 

Tottenham Hotspur

Ivan Perisic (bai da kwantiragi) Fraser Forster (Southampton) Yves Bissouma (Brighton) Richarlison (Everton) Tyrell Ashcroft (Reading) Josh Keeley (St Patrick's Athletic) Clement Lenglet (Barcelona) Loan Djed Spence (Middlesbrough) 

West Ham United

Nayef Aguerd (Rennes) Alphonse Areola (PSG) Patrick Kelly (Coleraine) Flynn Downes (Swansea) Gianluca Scamacca (Sassuolo) 

Wolverhampton Wanderers

Nathan Collins (Burnley)