Real Madrid za ta kara da Milan da Barca da Chelsea a Amurka

Real Madrid za ta fafata da AC Milan da Barcelona da kuma Chelsea a Soccer Champions Tour, a Amurka a 2024 daga cikin wasannin tunkarar kakar badi.

Za ta fara fafatawa da AC Milan ranar 31 ga watan Yuli a Soldier Field a Chicago da kungiyar Italiya.

Real da Milan sun hadu a gasar zakarun Turai karo 15, kowacce ta yi nasara shida da canjaras uku.

Wasan da suka kara a bayan nan:

Champions League Laraba 3 ga watan Nuwamba 2010

  • AC Milan 2 - 2 Real Madrid

Champions League Talata 19 ga watan Oktoba 2010

Real Madrid 2 - 0 Milan

Karawa ta biyu kuwa ita ce ta hamayya da ake kira El Clasico da Barcelona a MetLife Stadium a Rutherford.

Za su kece raini kenan ranar 3 ga watan Agusta a birnin New Jersey.

Kungiyar Santiago Bernabeu ta hadu da Barcelona sau biyu a bana, za kuma su kara fuskanta juna a La Liga ranar 21 ga watan Afirilu a Santiago Bernabeu.

Wasa biyu da aka yi tsakanin Real Madrid da Barca a bana

Spanish Super Cup Lahadi 14 ga watan Janairun 2024

  • Real Madrid 4 - 1 Barcelona

Sifanish La Liga Asabar 28 ga watan Oktoban 2023

  • Barcelona 1 - 2 Real Madrid

Real Madrid za ta buga wasa na uku na karshe da Chelsea ranar 6 ga watan Agusta a Bank of America Stadium a Charlotte.

Real Madrid da Chelsea sun kara a wasannin zakarun Turai karo tara, inda kungiyar Italiya ta yi nasara hudu ta Sifaniya ta ci uku da canjaras biyu.

Wasa da suka fuskanci juna a bayan nan

Champions League Talata 18 ga watan Afirilun 2023

  • Chelsea 0 - 2 Real Madrid

Champions League Laraba 12 ga watan Afirilun We 2023

  • Real Madrid 2 - 0 Chelsea

Dukkan 'yan wasan Real Madrid za su buga wasannin na Soccer Champions Tour 2024, in banda wadanda za su yi wasan daf da karshe a UEFA European Championship idan kungiyar ta kai matakin da wadanda za su kara a Copa America.

Wasannin Soccer Champions Tour da Real Madrid za ta buga:

Real Madrid da AC Milan (31 ga Yuli a Soldier Field a Chicago).

Barcelona da Real Madrid (3 ga Agusta a MetLife Stadium a Rutherford)

Chelsea da Real Madrid (6 ga Agusta a Bank of America Stadium a Charlotte)

Real tana ta daya a teburin La Liga da tazarar maki takwas tsakaninta da Barcelona, kuma saura wasa tara a kammala kakar bana.

Haka kuma Real ta kai daf da na kusa da na karshe a Champions League, inda za ta kara gida da waje da Manchester City, mai rike da kofin bara.