Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manoma sun koma amfani da fasahohi don yi wa shuka barbara
- Marubuci, Natalie Lisbona
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, wakiliyar BBC kan fasaha daga Tel Aviv
Cikin hasken hantsi da ya ƙwalle, Thai Sade yana karkade bishiyoyin dan itaciyar fiya, wadanda nan gaba kadan zai yi wa barbara ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Bisa amfani da fasahar moshav, wani garin manoma na tsakiyar ƙasar Isra'ila, Mista Sade shi ne mai kamfanin fasaha na BloomX. Kuma ya ce kamfanin ya gano wata hanya da ake amfani da na'ura ko inji don yi wa shukoki barbara tamkar yadda kudajen zuma ke yi.
"Ba wai muna maye gurbin ƙudajen zuma ba ne... maimakon haka, muna samar da hanyoyin barbara mafi inganci ga manoma, da nufin rage dogaro a kan ƙudajen zuman da ake kiwo don samun zumar sayarwa," a cewarsa.
Uku cikin hudu na amfanin gona da ake shukawa a duniya don samar da kayan marmari ko wani nau'in irin shuka don amfanin dan'adam, sun dogara ne, akalla a wani bangare a kan ƙwari masu yi wa shuka barbara.
Kuma ƙudajen zuma, ko dai zuman da ake kiwo, ko kuma nau'o'in ƙudajen zuma sama da 20,000 da ake samu a dazuka ne, ke yin aikin dauko bununin da ake barbarar da shi.
An yi ƙiyasin cewa ƙudan zuma a Amurka shi ke yin barbarar kashi 75 cikin 100 na itatuwan kayan marmari da gyaɗa da kuma ganyayyaki da ake shukawa a ƙasar. Wannan adadin shi ne aka yi ƙiyasi a dukkan ƙasashen Turai, yayin da sauran ƙwari ke yin barbarar kashi 25.
Sai dai abin damuwar ga manoma shi ne yadda ƙudan zuma ke ƙarancin samu a wasu sassan duniya sakamakon sauyin yanayi da kuma yadda ake amafani da magungunan kashe ƙwari.
Kudan zuma a Turai ya yi ƙaranci ne saboda wata cutar da ke kashe ƙwari da ta addabi ƙasashen.
Kamfanin fasaha na BloomX yanzu haka ya mayar da hankali wajen barbarar dan itaciyar fiya da nau'in inibi (blueberry) ko da kuwa an samu ƙarancin ƙudan zuma, fasahar za ta taimaka.
Injin da kamfanin ya samar ana kiran sa da Robee, kuma yana da abin turawa daga kowanne ɓangare.
Injin na jijjiga ne bayan an kunna shi, kuma idan aka jingina shi a jikin bishiyar blueberry, yana sanya bishiyar ta yi wa kanta barbara. Yanayin yadda injin ke jijjiga na samar da hanya iri ɗaya da wadda ƙudan zuma ke samarwa idan ya hau kan bishiya.
Sai kuma ɗaya injin, da kamfanin na BloomX ya samar mai suna Crossbee da ake amfani da shi wajen yi wa fiya barbara.
Yanzu haka ana amfani da waɗannan injina a Kudancin Amurka da Afirka ta Kudu da Sifaniya da kuma Isra'ila, kamfanin dai ya ce ya taimaka wajen yiwa bishiyoyi barbara da kashi 30 cikin 100.
Ana sarrafa Injinan da wata manhaja da ake saukewa a waya kuma tana amfani da manhajar sanin wuri don haka duk inda aka yi aiki da ita, tana ajiye adireshin wurin.
A jihar Califonia ta Amurka, noman nau'in gyaɗar almond, babbar sana'a ce.
Ana noman almond kashi tamanin na abin ake samarwa a duniya, yayin da darajar almond din ta kai sama da dala biliyan 10 duk shekara.
Wasu rahotanni na cewa kashi 70 cikin 100 na ƙudan zumar da ake sayarwa a sauran sassan Amurka, ana kai su Califonia ne domin noman gyadar almond.
Wata farfesa a fannin aikin noma a jami'ar Washinton, Lisa Wasko DeVetter ta ce fasahar yin barbara za ta taimaka saboda yadda wasu yankunan Amurka ke fama da ƙarancin ƙudan zuma.
"Tafiya mai tsawo na ragewa ƙudan zuma kuzari, sai dai noman almond na taimaka wa masu kiwon zuma wajen samun kuɗaɗen shiga" inji ta.
"sai dai hakan na janyo koma baya a wasu yankunan da ke noma tsirran da ke buƙatar ƙudan zuma na fuskantar matsala saboda buƙatar da ake da ita wajen noman almond a Califonia."
Wasu masu sharhi na ganin cewa noman almond na haifar da ƙarewarsu a doron ƙasa, yayin da amsu kiwon su ke ganin cewa yawan amfani da magungunan kashe ƙwari a gona ke kawo ƙarshen zuman ƙuda da kuma wahalar da sukje fuskanta yayin da ake tafiyar dubban kilomitoci wajen kai su inda ake buƙatarsu.
Shugaban kamfanin fasaha da ya ƙware wajen samar da injinan barbara na zamani a Isra'ila Edete, Eylam Ran ya ce " suna samar da sidarin da ke taimakawa wajen yi wa filawa ciki."
"Muna kuma yin hakan ga tuffa da nau'in inibi da gayɗar almonds, kuma sinadaren na ɗauke da taki."
Injinan kamfanin Edete ana amfani da su ne a yankin Califonia, kuma yanzu haka an soma amfani da fasahar wajen noman almond.
Mista Ran ya ce wannan fasahar za ta samar da farin ciki ga ƙudan zuma saboda wajen da ake amfani da su ba wurin da ya dace da su bane, maimakon hakan kashe su yake.
Diane Drinkwater na ɗaya daga cikin ƴan ƙungiyar masu kiwon ƙudan zuma a Birtaniya ta ce " Da za a ba lafiya da walwalar ƙudan zuma mahimmanci, to da ba a buƙatar wata fasahar barbara ga tsirrai,
"Ƙudan zuma ya kasance yana irin wanann aikin shekara da shekaru kuma kyauta, kuma ɗaukar shi daga wani wuri zuwa wani wajen na taimakawa masu kula da ƙudan zuman wajen samun ingantacciyar rayuwa."