Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace ce Camilla – Matar sabon Sarkin Ingila?
Ita ce abar ƙaunar Charles, makusanciyarsa tun suna matasa kuma mai ɗakinsa ta tsawon shekara 17. Kuma yanzu, ita ce wadda take auren Basarake da a Turancin Ingilishi ake yi wa laƙabi da 'Queen Consort'.
Al'umma sun saba ganin Camilla kusa da mai gidanta a taruka da bukukuwa amma kamar yadda ta taɓa faɗa, abu ne mai sauƙi.
Mata kaɗan ne suka fuskanci suka kamar Camilla Parker Bowles. Ita ce ta kasance a tsakiyar rabuwar auren da aka yi a ƙarni, sau da dama ana kwatanta ta da Diana, tsohuwar matar Charles.
Matakinta na zabin Charles ya jefa rayuwarta cikin ƙalubale. Tsawon shekaru, tana idon kafafen yada labarai - suna bibiyarta, da ɗabi'unta sannan tana yawan fuskantar suka ta ko ina.
Amma ta samu galabar hana ƙalubalen da take fuskanta ya yi tasiri a kanta inda a hankali ta tabbatar da matsayinta na mace mafi girman matsayi a tsakanin iyalin masarauta.
Ya kasance tafiya mai nisa ga matar da ake cewa Yarima Charles ya tsunduma cikin kogin ƙaunarta a lokacin da suka haɗu suna ‘yan shekaru 20.
An ɗauki lokaci kafin Sarauniya Elizabeth ta nuna goyon bayanta ga soyayyarsu amma a shekarunta na ƙarshe ta nuna goyon bayanta ga Camilla.
Ba lalle sabuwar Sarauniyar ta samu cikakken goyon bayan al'umma ba amma kamar yadda ta faɗa da kanta, cikin wata hira da aka yi da ita da mujallar Vogue a farkon wannan shekarar: "Ina fatan samun galaba kan duk wani ƙalubale na ci gaba da harkokina. Dole ne rayuwa ta ci gaba."
Auren magajin sarauniya ba zai zama makomar da aka yi wa Camilla Rosemary Shand hasashe ba, wadda aka haifa ranar 17 ga watan Yulin 1947. Iyalinta sun kasance masu wadata da sanin mutane amma tabbas ba su da jinin sarauta.
Ta tashi kusa da ƴan uwanta a yanayi mai kyau, tana wasa da ɗan uwanta da ƴar uwanta a unguwar da suke zaune a Sussex. Mahaifinta, Bruce Stand, wanda tsohon soja ne, yana son karanta mata tatsuniyoyi a lokacin barci sannan mahaifiyarta, Rosalind, tana hidimar kai yara makaranta da kuma zuwa bakin tekun.
Tasowarta ta bambanta da ta Charles wanda sau da dama ba ya tare da mahaifansa ba saboda suna tafiye-tafiye zuwa ƙasashen duniya.
Kammala makaranta a Switzerland, ta shirya Camilla ga iya zama a tsakanin al'ummar birnin London. Ta yi fice kuma daga tsakiyar shekarun 1960, ta tsinci kanta cikin soyayya da wani tsohon soja, Andrew Parker Bowles.
A farkon shekarun 1970 ne aka haɗa ta da matashi Yarima Charles. A cewar Jonathan Dimbleby, wanda ya rubuta littafi kan yariman, "ta kasance mai nuna ƙauna gare shi, kuma nan da nan ta faɗa kogin so - ya kuma tsunduma sonta kusan lokaci guda." Amma lamarin bai zo a lokacin da ya dace ba.
Charles a lokacin yana dan shekaru 20 kuma yana aiki a rundunar sojin ruwa. An tura shi aiki ƙasar waje a ƙarshen shekarar 1972. Kuma a lokacin da baya nan, Andrew ya nemi amincewar Camilla ta aure shi kuma ta amince. Me ya sa ba ta jira Charles ya nemi aurenta ba? Ƙawayenta na raɗe-raɗin kawai ba ta hango kanta ba ne a matsayin sarauniya.
Sai dai duk da haka, sun ci gaba da hulɗa. Charles da Andrew sun buga ƙwallon polo tare kuma ma'auratan sun buƙaci Charles ya kasance uba ga ɗansu na farko, Tom. Hotunan Charles da Camilla a wajen wasan ƙwallon polo sun nuna suna cikin annashuwa.
A lokacin bazara cikin 1981, Charles ya hadu tare da neman soyayyar matashiya Lady Diana Spencer. Duk da haka, suna tare da Camilla. A littafin Diana: Labarinta na gaskiya, marubuci Andrew Morton ya yi bayani dalla-dalla yadda Diana ta kusa soke aurensu kwanaki biyu kafin ranar bayan da ta gano wani abin hannu da Charles ya yi wa Camilla wanda a jiki aka rubuta "F" da "G"-lakabin da suka bai wa junansu shi ne Fred da Gladys.
Diana ta yi ta fama da kasancewar Camilla tana hulɗa da mijinta. Charles dai ya jaddada cewa sun koma suna alaƙa ne a lokacin da aurensa ya mutu. Amma Diana ta bayyana a wata hira da ta yi a 1995 "mu uku ne a auren nan."
Yayin da rayuwar auren Charles da na Camilla ke tangal-tangal, wasu daga cikin kanun labaran sun tayar da hankali, har aka fito da bayanan wani kiran waya cikin dare da aka naɗa cikin sirri a 1989 aka kuma yaɗa ga jama'a shekara huɗu bayan nan.
Irin hirar da aka ji a wayar, ta nuna irin kusancin da ke tsakanin Charles da Camilla.
Mutuwar auren Camilla ya tabbata a 1995. Auren Charles da Diana kuma ya mutu a 1996. Hakan ya nuna irin tsananin son da Camilla take yi wa Charles da har ta zaɓi ta kasance da shi duk da yadda jama'a ke sukarta da kuma halin da ƴaƴanta suka shiga - Tom da Laura.
Tom Parker Bowles sun yi magana kan lokutan da mai hoto ke shiga cikin bishiyoyi a wajen gidansu da ke Wiltshire. "Babu wani abu da wani zai ce game da iyalinmu da zai dame mu," kamar yadda ya rubuta a Jaridar The Times a 2017, inda ya ƙara da cewa: "Babu wani abu da zai damu mahaifiyata."
Camilla ta ce: "Babu wanda yake so a rika maganarsa kullum. Dole ne ka samu hanyar da za ka ci gaba da rayuwarka.
"Samun hanyar magance sukar ya ƙara zama abu mai wuya a 1997 bayan mutuwar Diana. A bainar jama'a, Charles ya mayar da hankali kan ƴaƴansa William da Harry inda Camilla ke wani gefen. Amma dangantakarsu ta ci gaba. Matsayar Charles ita ce yana tare da Camilla don haka ya soma wani kamfe na saka ta a idon jama'a. Ya fara ne da zuwa otal ɗin Ritz a 1999 inda suka yi bikin cikar ƴar uwar Camilla shekara 50. Shekara shida bayan nan, suka yi aure a wani ƙwarya-ƙwaryar biki a Windsor Guildhall.
Tsawon shekaru, ana tafka muhawara kan ko za a kira ta a matsayin sarauniya. Yayin da a dokance za ta iya amfani da taken, sai dai a hukumance za a riƙa kiranta ne a matsayin Gimbiya wato "Princess Consort, a matsayin hanyar gamsar da wadanda suke zarginta da kawo ƙarshen auren Charles da Diana.
A ƙarshe Sarauniya ta shiga tsakani inda a 2022 ta ce fatanta shi ne idan lokaci ya yi a kira Camilla a matsayin Queen Consort wato matar Sarki.
A nan tabbatarwa ce cewa Camilla ta samu matsayinta a wajen Charles. An kuma kawo ƙarshen duk wata muhawara. Idan Sarauniya tana shakkar Camilla, tabbas hakan ya fi faruwa da Yarima William da Harry. Dukkansu za su yi fama da tasirin mutuwar auren iyayensu sannan da mutuwar mahaifiyarsu lokacin da William yake da shekara 15, Harry kuma 12.
A 2005, ƴan watanni bayan aurensu, Harry wanda ya kusa cika shekara 21 a lokacin, ya ce Camilla mace ce mai kirki wadda take sanya mahaifinsu cikin farin ciki.
"Ni da William muna ƙaunarta sosai kuma muna zaman lafiya da ita. "Ɗan uwansa bai yi magana game da yadda suke ji da zuwan Camilla rayuwar mahaifinsu ba." Sai dai kallon yadda William da mai ɗakinsa Catherine ke tafiyar da harkokinsu a wuraren taruka - da alama akwai kyakkyawar dangantaka.
Yanzu da take tsakiyar shekara 70, rayuwar Camilla ta karkata ga tallafa wa mijinta da iyalinta. Camilla kaka ce ga mutum biyar. Tana son mijinta da yaranta da kuma jikokinta. Ɗan uwanta Ben Elliot ya faɗa wa mujallar Vanity cewa "Camilla ta kuma yi tasiri a ɓangarori da suka shafi wayar da kai kan cutar osteoporosis da ke raunana ƙasusuwan jiki - cutar da ta shafi mahaifiyarta da kakarta, yin bayani kan cin zarafi a gidan aure da fyaɗe da cin zarafi ta hanyar lalata, neman ta koyawa wasu son kratu kamar yadda ta yi gado daga wajen mahaifinta inda ta buɗe wani shafi a Instagram na masu sha'awar litattafi.
Yayin da nake ɗaukar rahoto a wani bikin samar da tallafi a Clarence House, na hangi Camilla tana zagaya bene, tana duba ko kowa ya shirya. Ta sauko ƙasa inda ta runguma tare da sumbatar shugaban gidauniyar tallafin.
A lokacin kullen korona, Camilla ta bayyana takaicin rashin rungumar jikokinta. Yayin da aka sassauta kullen, ƙarara ta jin daɗin yadda ta koma harkokinta.
A yanzu Charles da Camilla sun shafe shekara 17 a matsayin ma'aurata. Irin kusancin da ke tsakaninsu a bayyane yake. Yadda suke kallon juna tare da dariya - zai yi wuya a gansu a taro ba tare da suna nishaɗi ba. "Suna ƙaunar juna da girmama juna kuma suna farin ciki lokaci ɗaya," Mista Elliot ya sanar da Vanity Fair.
Suna rayuwa ta jin daɗi amma cikin sa ido da matsin lamba. "Yana da faranta rai kasancewa tare da wani a gefenka," Yarima Charles ya faɗa wa CNN a lokacin da suka cika shekara 10 da aure.
"Ta kasance mai nuna goyon baya kuma tana ban dariya, godiya ga Ubangiji." "Wani lokacin kamar wucewar jiragen ruwa ne cikin dare," in ji ta game da rayuwarsu tare, "amma muna yawan kasancewa tare mu sha shayi mu kuma tattauna kan rayuwa." "Matsayin sarki ɗaya ne - kuma yadda Charles ya kasance tare da Camilla duk rintsi wataƙila saboda ya san cewa ita kaɗai ce za ta iya ba shi haɗin kan da yake buƙata a sabon matsayinsa yanzu.