Ƙasashen Afrika bakwai da sojojin Amurka suka shiga

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci sojojin kasarsa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana game da yiwuwar far wa ƙungiyoyin "ƴan ta'adda" da ya ce suna yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya, "kuma gwamnati ba ta ba su kariya ba".

Trump bai faɗi kisan gillar da aka yi ba amma kuma zargin kisan ga mabiya addinin Kirista a Najeriya na ci gaba da jan hankali a tsakanin wasu ƴan jam'iyyar Republican a Amurka.

Ƙungiyoyin da ke sanya ido kan rikice-rikice sun ce babu wata shaidar da ke nuna cewa ana kashe Kiristoci fiye da Musulmi a Najeriya, inda suka ce hare-haren ƴan ta'addar na shafar dukkan ɓangarorin biyu ne.

Haka nan gwamnatin Najeriya ta yi watsi da iƙirarin yi wa Kiristoci "kisan ƙare-dangi", tare da bayyana cewa Najeriya na maraba da duk wani matakin taimaka mata wajen daƙile ayyukan "ƴan ta'adda".

Sai dai babban abin da ya fi ɗaukar hankali game da wannan batu shi ne yadda shugaban Amurkar ya nuna cewa abu ne mai yiwuwa Amurka ta iya ɗaukar matakin soji kan Najeriya, ƙasar Afirka mafi yawan al'umma kuma mai ɗimbin arziƙin man fetur.

BBC Hausa ta yi nazari kan ƙasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan daƙile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar "ƴan ta'adda".

Somalia (1992–1994)

..

Asalin hoton, Getty Images

Ƙasar Somalia ta kasance ɗaya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s.

A lokacin da ƙasar ke cikin rikicin yaƙin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya.

Wannan ya haifar da sanannen yaƙin Mogadishu da ake kira "Battle of Mogadishu" a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin ƙalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida.

Amurka ta ƙaddamar da hare‑hare na jiragen sama a kan mayaƙan al-Shabab kuma ta haɗa kai da gwamnatin Somaliya domin dakile Al‑Shabab.

A watan Janairu 2024 an bayar da rahoton cewa Amurka ta kashe 'ƴan ƙungiyar Al‑Shabab uku ba tare da yin wata gagarumar ɓarna ba.

Bugu da ƙari, a watan Fabrairun 2025, Donald Trump ya ce ya umarci a ƙaddamar da hari ta sama kan wasu jagororin ƙungiyar IS da ke arewacin Somalia.

Laberiya (2014–2015)

..

Asalin hoton, Getty Images

A lokacin da cutar Ebola ta ɓulla a yammacin Afirka, Laberiya ta kasance cikin ƙasashen da cutar ta fi shafa. Amurka ta tura sojoji da kayan aiki domin taimakawa wajen daƙile yaɗuwar cutar.

Wannan ya haɗa da gina cibiyoyin kula da marasa lafiya, jigilar kayan agaji, da horar da ma'aikatan lafiya.

Sai dai kuma a shekaru gabanin samun ƴancin kai da bayan samun ƴancin kai, Amurka ta tura dakaru zuwa ƙasar domin daƙile yaƙin basasa da yan ƙasar suka kwashe shekaru suna fama da shi.

Senegal (2014–2015)

Senegal ta kasance cibiyar haɗin gwiwa a lokacin ɓarkewar cutar Ebola. Amurka ta tura sojojinta domin su bayar da tallafi na kayan aiki da kiwon lafiya don haɗa kai a matakan yanki.

Wannan ya taimaka wajen hana cutar ta mamaye ɓangaren kiwon lafiya da ya riga ya kasance da rauni a Senegal da ƙasashen makwabta.

Kenya (1998)

Bayan harin ta'addanci da aka kai wa ofishin jakadancin Amurka a Nairobi, wanda ya hallaka mutane 224, ciki har da Amurkawa 12 da kuma jikkata fiye da mutum 1000, Amurka ta tura sojojinta don bayar da agajin gaggawa, kula da marasa lafiya, da tallafawa wajen ceto rayuka.

Aikin ya fi mayar da hankali kan jin-ƙai da bincike.

Tanzaniya (1998)

..

Asalin hoton, Getty Images

Harin ta'addanci da ya shafi Kenya ya kuma shafi Dar es Salaam a Tanzaniya, kamar yadda aka yi a Nairobi, sojojin Amurka sun shiga don kula da wadanda abin ya shafa, da tallafawa wajen kare yankin daga faɗawa cikin rudani, da gudanar da binciken harin kamar yadda Amurkar ta yi iƙirari.

Libya

Sojojin Amurka sun taɓa kasancewa cikin Libya ta hanyoyi daban-daban, suna shiga su taya yaƙi da kungiyoyi irin su ISIS tare da goyon bayan ƙoƙarin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.

Haka kuma akwai lokutan da Amurka ta shiga kai tsaye: kamar harin soji da ta yi a shekarar 1986 da kuma fitowarta a cikin yaƙin 2011 da ya kawo ƙarshen mulkin shugaban Muammar Ghaddafi.

Bugu da ƙari, tun daga watan Nuwamban 2015 har zuwa 2019, Amurka da ƙawayenta sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da amfani da jirage marasa matuƙi a Libya lokacin yaƙin basasar da ya ɓalle tun bayan faɗuwar gwamnati Muammar Ghaddafi a 2011.

Jamhuriyar Nijar

..

Asalin hoton, Getty Images

Kasancewar sojin Amurka a Jamhuriyar Nijar ya haɗa da tura dakaru na musamman da jiragen yaƙi marasa matuka don taimaka wa gwamnatin Nijar da Faransa wajen yaƙi da ƙungiyoyin ta'addanci a karkashin Operation Juniper Shield.

Ba a san girman adadin sojin Amurka a Nijar ba sosai har sai da aka yi harin Tongo a 2017, inda 'yan ƙungiyar ISGS suka kashe sojojin Amurka huɗu da na Nijar huɗu, lamarin da ya jawo tambayoyi da muhawara game da dalilin da ya sa Amurka ta ajiye sojoji sama da 800 a Nijar a wancan lokaci.

A 2024 ne hedikwatar tsaro ta Pentagon ta sanar da cewa za ta kammala kwashe dakarunta daga Jamhuriyar ta Nijar ya zuwa tsakiyar Satumban shekarar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.

Kuma a ranar 7 ga watan Yulin ne Amurkar ta kammala kwashe dukkannin sojojinta daga sansanin da ake kira da 101, inda kuma ragowar 500 da ke sansanin 201 suka fice daga ƙasar a ranar 5 ga watan Agustan 2024.