Waiwaye: Jana'izar Aminu Ɗantata da amincewa da ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka

Lokacin karatu: Minti 5

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Yadda aka gudanar da jana'izar Alhaji Aminu Dantata a Madina

A yammacin ranar Talata ne aka gudanar da jana'izar hamshaƙin ɗankasuwar nan na Najeriya, Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a masallacin Annabi (S.A.W) da ke birnin Madina.

Jana'izar ta gudana ne bayan sallar magariba, inda kuma aka binne gawarsa a maƙabarta Baƙiyya mai tarihi a birnin na Madina.

Mutane da dama ne daga Najeriya suka halarci jana'izar - wadda aka jinkirta tun da farko sakamakon wasu dalilai na ciƙa ƙa'ida.

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ta halarci jana'izar, tare da tawaga mai ƙarfi da ta ƙunshi manyan jagororin jihar.

Ƴan hamayya sun amince da ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka

Gamayyar wasu jiga-jigan ƴansiyasa a Najeriya da ke hamayya da gwamnatin jam'iyyar APC sun amince da African Democratic Congress (ADC) a matsayin jama'iyar da za su ƙulla ƙawancen haɗaka a cikinta.

Ƴansiyasar sun ce sun amince da ADC ne da nufin haɗa ƙarfi da ƙarfe a cikinta da nufin kawar da jam'iyyar APC daga mulkin Najeriya a zaɓen 2027.

An cimma ƙawancen ne a taron haɗakar da aka gudanar ranar Laraba a babban ɗakin taro na Ƴar'adua Centre da ke birnin Abuja.

Tuni dai haɗakar ƙawancen ta zaɓi wasu ƙusoshin tafiyar sabon ƙawancen domin su jagoranci sabuwar tafiyar.

Kotu ta buƙaci majalisa ta mayar da Sanata Natasha bakin aiki

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta buƙaci majalisar dattijai ta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wanda aka dakatar bakin aiki.

Da take yanke hukunci ranar Juma'a, mai shari'a Binta Nyako ta kwatanta cewa dakatar da Natasha tsawon watanni shida da aka yi, ya yi tsauri.

Kotun ta kuma ce shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio bai yi laifi ba, lokacin da ya hana Natasha yin magana a majalisa saboda lokacin ba ta zauna kan ainihin kujerar da aka ware mata ba.

Ta kuma buƙaci Sanata Natasha ta bai wa majalisar hakuri.

Mai shari'a Nyako ta kuma kori batun da Akpabio ya gabatar cewa kotun ba ta hurumin tsauraron ƙarar.

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla mayaƙan Boko Haram/ISWAP takwas a wani artabu da ya ɓarke a ƙauyen Manawaji, cikin ƙaramar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno.

Rundunar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Litinin, 30 ga Yuni, 2025.

Rundunar sojin Operation Hadin Kai, tare da hadin gwiwar ƙungiyoyin ƴan sintiri na CJTF da dakarun Hybrid Forces ne sun gudanar da wannan nasarar.

A yayin gumurzu mai zafi da suka fafata da mayaƙan, dakarun sun samu nasarar kashe guda takwas daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka.

"Bayan kammala fafatawar, sojojimu sun ƙwato bindigogi da dama da harsasai daga hannun mayaƙan da suka mutu da kuma waɗanda suka tsere." In ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa "Babu wanda ya jikkata ko ya mutu daga ɓangaren sojoji, da sauran da aka yi haɗin gwiwa da su."

Dangote ya rage farashin litar man fetur zuwa naira 840

A cikin makon da muke bankwana da shi ne kuma, matatar man Dangote ta sanar da rage farashin litar man fetur daga naira 880 zuwa naira 840 ga dillalan da ke siyan man daga matatar, a wani mataki da ya zo gabanin fara rabon man a faɗin ƙasa daga 15 ga watan Agusta.

Shugaban hulɗa da jama'a na matatar, Anthony Chiejina, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa rage farashin ya biyo bayan faɗuwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

A baya-bayan nan, kamfanin man Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin fetur zuwa naira 925 a wasu tashoshinsa a Legas, daga naira 915.

Dangote ya ce sun sayi motoci 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG) don sauƙaƙa rabon mai ba tare da cajin ƙarin kuɗin sufuri ba.

NAHCON ta kammala jigilar alhazan Najeriya daga Saudiyya

Hukumar Alhazan Najeriya ta kamala jigilar alhazan ƙasar da suka sauke farali a aikin hajjin bana.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kammala aikin kwaso alhazan daga ƙasa mai tsarki a ranar Laraba 2 ga watan Yulin 2025.

Kimanin alhazan Najeriya 41,291 ne suka sauke farali a wanan shekara, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Jirgin ƙarshe da ya ɗauko alhazan jihar Kaduna ya taso ne a safiyar ranar Laraba.

Lakurawa sun kashe mutum 15 a Sokoto

Wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne sun kashe mutum 15 a wani mummunan hari da suka kai ƙauyen Kwalajiya da ke ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata.

Ana zargin harin martani ne bayan kashe wasu mutum uku daga cikin ƙungiyar, ciki har da wanda ake zargin shugabansu ne a wani harin da ya ci tura da suka kai a baya a garin.

Ɗaya daga cikin shugaba a yakin da ya nemi a ɓoye sunansa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa maharan sun dira ƙauyen ne a daidai lokacin da jama'a ke cikin masallaci suna sallar Azahar.

"Muna cikin masallaci lokacin da suka kawo hari da yawansu.

"Da zuwansu suka fara harbe-harbe." inji shi.

Kotu ta ɗaure ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke wa wani matashi ɗan Tiktok, mai suna Umar Hashim Tsulange hukuncin ɗaurin shekara guda saboda samunsa da laifin taka doka.

Shafin Freedom Radio a jihar ya ruwaito cewa kotun ta ba shi zaɓin zaman gidan yari ko biyan tarar naira 80,000.

Umar Tsulange ya yi fice shafin Tiktok inda a wasu lokutan ake ganinsa yana wanka ko kwanciya ko wani abu da zai ɗauki hankalin jama'a a tsakiyar titi gaban ababen hawa da danja ta tsayar.

Kazalika kotun ta umarci Tsulangen ya biya Hukumar Tace Fina-finai diyyar Naira 20,000 ladan wahalar da ta yi na gurfanar da shi.

A watannin da suka gabata ne rundunar ƴansandan jihar Kano ta ja hankalin matasan da ke tsayawa tsakiyar titi domin ɗaukar bidiyo, tana mai cewa hakan na haifar da hatsura a wasu lokuta.