United na son Baleba, mece ce makomar Grealish da Lookman?

Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta tuntuɓi Brighton kan ɗanwasan Kamaru na tsakiya Carlos Baleba, mai shekara 21. (Athletic - subscription required)

Everton ta soma tattaunawa domin karɓo ɗanwasan Ingila Jack Grealish, mai shekara 29, daga Manchester City. (Sky Sports)

Ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak an faɗa masa ya yi atisaye shi kaɗai a Newcastle United saboda farautarsa da Liverpool ke ci gaba da yi. (Mirror)

Newcastle ta taya ɗanwasan baya na Jamus Malick Thiaw kan sama da fam miliyan 26 amma AC Milan ta ƙi amincewa da tayin inda take son riƙe ɗanwasan mai shekara 23. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Nottingham Forest na dab da cimma yarjejeniya da Juventus kan ɗanwasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Everton ma na son Douglas Luiz amma kamar Forest, tana diba yiyuwar karɓo shi aro da zaɓin sayensa daga baya. (Mail)

RB Leipzig na tattaunawa Liverpool kan ɗanwasan tsakiya na Ingila mai shekara 22 Harvey Elliott. (Fabrizio Romano)

Inter Milan na diba yiyuwar ɗauko ɗanwasan gaba na Manchester United da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, idan ta kasa samun ɗanwasan gaba na Najeriya Ademola Lookman, mai shekara 27, daga Atalanta. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Ƙungiyoyin Saudiyya sun tuntubi ɗanwasan tsakiya na Manchester City Mateo Kovacic, mai shekara 31, amma ɗanwasan ba ya son tafiya. (Fabrizio Romano)