Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken

Antony Blinken

Asalin hoton, REUTERS

Bayanan hoto, Antony Blinken ya bukaci a tsahirta don shigar da kayan agaji a Gaza amma ya kasa yin kira da a tsagaita bude wuta

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce idan Isra'ila ta tsagaita wuta a Gaza, Hamas za ta samu damar hada kan mayaƙanta don kai sabbin hare-hare.

Amma ya ƙara da cewa akwai buƙatar Isra'ila ta ɗauki matakan da suka dace don kare rayukan fararen hula.

Mista Blinken ya yi wannan jawabi ne yayin ganawarsa da shugabannin Larabawa ranar Asabar a Jordan bayan sun buƙaci a gaggauta kawo karshen yaki.

Sun zargi Isra'ila da tafka laifukan yaƙi.

Yayin taron manema labaran, Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ya ce: "Ba za mu yarda cewar don kare kai suke kai hari ba.''

Amurka na ci gaba da goyon bayan damar da Isra'ila ta ke da ita ta kare kai daga Hamas.

Mista Safadi ya bayyana rikicin a matsayin wani kazamin yaki da ke kashe fararen hula da rusa gidaje da asibitoci da makarantu da masallatai da kuma majami'u.

Ana fargabar yakin zai janyo 'yan-sa-kai daga wasu yankuna, al'amarin da zai iya ɗaiɗaita Gabas ta Tsakiya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mista Blinken, wanda ya yi kira da a tsahirta a yaƙin saboda ayyukan agaji maimakon tsagaita wuta, ya ce yayin da Amurka ba ta amince da shugabannin kasashen Larabawa kan wasu hanyoyin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin ba, burinsu ɗaya ne.

Isra'ila ta fara kai hare-hare a Gaza bayan Hamas ta kashe mutum fiye da 1,400 a Isra'ila yayin harin ba-zata na ranar 7 ga watan Oktoba. Sama da mutum 200 aka yi garkuwa da su kuma har yanzu ana kyautata zaton suna tsare a Zirin Gaza.

Ma'aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta ta bayyana cewar akalla mutum 9,770 aka kashe a Gaza, cikinsu akwai yara 4,880 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Ziyarar Mista Blinken a Jordan ta zo kwana daya bayan ya ziyarci Isra'ila, inda ya tattauna da firaminista Benjamin Netanyahu, wanda ya ce ba za a tsagaita wuta ba har sai an sako dukkan Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su.

Dakarun Isra'ila (IDF) sun karkatar da hare-harensu arewacin Gaza bayan gargadin da suka yi wa fararen hula da su fice.

Kimanin fararen hula 400,000 ne har yanzu suke yankin, a cewar wakilin Amurka na musamman kan lamuran jin-kai a yankin Gabas ta Tsakiya, David Satterfield.

Duk da haka dakarun na IDF na kai hare-hare a kudancin kasar, kuma tuni Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta bayyana fargabar cewa babu wani wuri a Gaza da ke da tsaro.

Mista Blinken ya yi magana a ranar Asabar din da ta gabata game da bukatar kara yawan tallafin da ke shiga cikin yankin ta mashigar Rafah ta Masar.

Kayan agaji kalilan ne suke isa Gaza, makwonni bayan Isra'ila ta sanar da yi wa yankuna kawanya da katse wutar lantarki da ruwan famfo.

Har ila yau, sakataren harkokin wajen Amurka ya gana da Firaministan Lebanon Najib Mikati, inda suka tattauna tashe-tashen hankali a kan iyakar kudancin Lebanon da Isra'ila, yankin da ake gwabza fada tsakanin 'yan Shi'a na Hezbullah da sojojin Isra'ila.

Shugaban kungiyar Hezbullah Hassan Nasrallah ya ki yin kira da a tsananta hare-hare kan Isra'ila, amma ya bar kofa a bude domin daukar mataki.

Mista Blinken zai ziyarci Turkiyya a ranar Lahadi don tattauna batun rikicin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Ziyarar ta zo a lokacin da Ankara ta umarci jakadanta a Isra'ila ya koma gida, bayan yanke duk wata alaƙa da Mista Netanyahu a wani mataki na yin Allah-wadai da zubar da jini a Gaza.