Wani lokaci nakan koma gefe na fashe da kuka - Ɗan jarida daga Gaza

Matar ɗan jarida Mahmoud Bassam da ɗansa ɗan wata 11 na cikin masu shan luguden wutar Isra'ila a Zirin Gaza

Asalin hoton, Mahmoud Bassam

Bayanan hoto, Matar ɗan jarida Mahmoud Bassam da ɗansa ɗan wata 11 na cikin masu shan luguden wutar Isra'ila a Zirin Gaza

Yana kira duk lokacin da ya samu dama. Ko kuma dai duk lokacin da ya samu damar yi wa wayarsa caji.

Yana cin abinci ne kawai idan ya samu. Yakan zagaya daga wurin da aka ɗaiɗaita zuwa wani matuƙar dai zai samu man fetur.

Bugu da ƙari, Mahmoud Bassamna cike da damuwa game da matarsa da ɗansa ɗan wata 11 saboda ya zama dole su yi hijira don guje wa hare-haren bam. Saboda duk lokacin da ya bar gida da safe ba shi da tabbas zai dawo ya tarar da su a inda ya bar su.

Ana maganar idan ma ya dawo ke nan. Ma'ana idan ba a tare hanyar ba ko kuma hare-haren sun yi ƙamarin da ba zai iya bin hanyar ba.

A Birnin Gaza a 'yan kwanakin nan, rayuwar Mahmoud na cikin yaƙi, abin da zai haifar da kuma abin da asarar da yake haifarwa.

Tun bayan fara yaƙin nan sati uku da suka wuce, Mahmoud yake zagayawa asibitoci da kuma sansanonin 'yan gudun hijira.

Iriin wannan aikin nasa da kuma taimakon wakilin BBC Rushdi Abualouf, da su ne BBC take iya samun damar bayar da labaran fararen hular Gaza, waɗnda ke shan luuguden wutar Isra'ila a kodayushe.

Da na same shi ta waya bayan shafe awanni ina ƙoƙari, mahmoud ya bayyana irin wahalar aikin da yake yi.

"Duk irin ƙoƙarin da nake yi, da irin juriyar kallon abin da nake gani wajen nemo labarai," in ji shi, "wani zubin sai na koma gefen kyamara na fashe da kuka. Daga baya kuma abin da zan yi shi ne shuru."

'Yan jaridar Gaza kan ɗauki labaran wahalar da ake sha wadda su ma suke cikinta

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, 'Yan jaridar Gaza kan ɗauki labaran wahalar da ake sha wadda su ma suke cikinta
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akasarin 'yan jaridar da na sani suna aiki a wuraren yaƙi kan ji cewa sun gaza saboda yawan wahalar da suke ganin mutane a ciki. Ta yaya za ka iya taimakawa bayan akwai masu buƙtar taimakon da yawa? Ta yaya za ka iya yin aikin idan ka tsaya taimaka wa mutane da abinci ko agaji?

Mu ba ma'aikatan agaji ba ne. Amma kuma mutane ne.

Irin wannan yanayi na ƙara zama tabbas a idanun Mahmoud idan ya haɗu da sauran abokansa. Wakilai da ke aiki da gidajen jarida na ƙasashen waje na da damar hawa jirgi su tanfi gida. Babu mamaki mu dinga yaƙin amma dai aƙalla mun yi nesa da shi da kuma iyalanmu.

Zirin Gaza ƙaramin wuri ne sosai - murabba'in kilomita 366 ne kawia baki ɗayan zirin. Mahmoud kan gano wani da ya sani a wannan wurin cikin sauƙi.

"Ni ɗan jarida ne kuma aikina shi ne bayar da rahoton abin da na gani," kamar yadda ya faɗa min. "Amma wani zubin dole nake tsayawa mu zauna tare da yaran nan, don na ba su ruwa kuma na ga abin da suke buƙata don na ba su."

Idan ya turo bidiyon da ya naɗa zuwa ofis, ni da sauran abokan aikina sai mu dinga mamakin irin natsuwarsa. Bai taɓa manatawa da cewa akasarin waɗanda yake ɗaukar hoto ko bidiyonsu ba su taɓa yin magana a kyamara ba a rayuwarsu a irin wannan halin.

Wannan yaƙin na ɗaya daga cikin waɗanda 'yan jarida suka fi shan wahala. An kashe fiye da 30 zuwa yanzu. Cibiyar Committee to Protect Journalists (CPJ) ta ce waɗanda suke Gaza na ɗanɗana kuɗarsu.

Ɗan jaridar Al Jazeera ke nan Wael Al-Dahdouh lokacin da yake jagorantar jana'izar matarsa da ɗansa da jikansa waɗanda aka kashe a yaƙin nan na Gaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ɗan jaridar Al Jazeera ke nan Wael Al-Dahdouh lokacin da yake jagorantar jana'izar matarsa da ɗansa da jikansa waɗanda aka kashe a yaƙin nan na Gaza

"Wannan lokaci ne mai haɗari ga 'yan jarida a Gaza," a cewar Sherif Mansour, wani ƙwararre kan Gabas ta Tsakiya na cibiyar CPJ.

"Mun ga yadda aka kashe adadi mafi yawa cikin shekara 21 na wannan rikici cikin sati uku kacal. 'Yan jarida da yawa sun rasa abokan aikinsu, da 'yan uwa, da gidajen iyayensu, kuma an tilasta musu hijira zuwa wurin da babu tabbas game da rayuwarsu."

A ƙramin wuri irin Gaza, ba abin mamaki ba ne idan labarin rashin abokin aiki ya karaɗe wuri nan take.

Yara Eid 'yar jaridar Falasɗinu ce wadda ta girma a Gaza. Yanzu tana zaune a Birtaniya cikin makokin abokinta Ibrahim Lafi, wanda aka kashe shi a farkon wannan yaƙin.

"Na yi rashin babban abokina Ibrahim. Ɗan jaridar Falasɗinu ne, amma ba ɗan jarida ba ne kawai. Shekararsa 21. Ɗan uwa ne, babban aboki, mai cike da fata," in ji ta.

"Mai ɗaukar hoto ne, kuma yana ƙaunar rayuwa sosai. Yana da yawn murmushi. Duk lokacin da zan gan shi yana murmushi."

"Shi ne ya fi taimaka min sosai cikin abokaina. Tabbas yana da fata masu yawa, kuma ya so ya zama mai ɗaukar hoton da zai nuna wa duniya irin kyawun Gaza."

'Yan jarida a Gaza kan tafi aiki ba tare da tabbacin cewa za su koma gida ba ko kuma za su tarar da iyalansu. Shugaban ofishin Al Jazeera Gaza, Wael al-Dahdaouh, ya rasa matarsa, da ɗansa, da 'yarsa, da kuma jaririn jikansa a harin Isra'ila.

Kwana ɗaya bayan haka ya koma bakin aiki, yana mai cewa wajibinsa ne. Mu da muke hangen abin daga nesa a nan Birnin Ƙudus, mun san cewa jajircewar ba ƙarama ba ce.