Sabon harin Isra'ila ya kashe fararen hula fiye da 30 a Gaza

Asalin hoton, Getty Images
Ma’aikatar lafiyar Hamas ta zargi Isra’ila da sake kai mummunan hari kan fararen hula a Gaza.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya ce mutane fiye da 30 aka kashe a luguden da Isra’ilan ta yi a sansanin ƴan gudun hijira na Maghazi da ke tsakiyar Zirin Gaza.
Wani ɗan jarida mai aiki da kafar yaɗa labaran Turkiyya ya ce an kashe masa ɗa da kuma ɗan-uwa a harin.
Kakakin sojin Isra’ila ya ce har yanzu basu tantance ko dakarun su ne suka kai wannan hari ba.
Wakilin BBC a Gaza ya ce Isra’ilan ta fara kai hari ne a kusa da asibitin birnin Gaza, inda ta yiwa wani gidan Burodi ruwan wuta.
Can kuwa a Arewacin Gaza, sojin Isra’ila na ci gaba da fafatawa da Hamas, lamarin da ke hana fararen hula damar tsallakewa daga yankin.
Mutanen da suka yi yunƙurin tsallakewa, bayan Isra’ila ta sanar da umarnin yin hakan sun ci karo da cikas saboda lalacewar da hanyar da zasu bi ta yi, lamarin da ke hana motoci wucewa.
Wasu da suka nemi tsallakewar sun ce sun yi ƙoƙarin bi ta babban titin Salah al-Din amma tilas suka canza tunani.
Ehab al-Jundi yana cikin masu neman tsallakewar, kuma ya ce: "Bayan sanarwar da Isra’ila ta fitar da ke nuna cewa babu haɗari a tafiya daga nan zuwa yankin da ba a faɗa, mun kama hanya ta babban titin Salah al-Din da nufin kwaso ƴan uwanmu da suka maƙale a Jabalia, amma hanyar ta lalace sosai, ga gawarwaki jibge, ga kuma motoci da suka lalace sun cika hanyar, muna kuma jin ƙarar tashin bama-bamai da harbin bindiga daga nesa."
Isra’ila dai ta ce Hamas ce ke hana fararen hula damar tsallakewa zuwa wajen da yaƙin ba zai shafe su ba.














