Dalilai huɗu da suka hana Falasɗinawa samun ƙasarsu ta kansu

Mama na mwana

Asalin hoton, Getty Images

Tun daga shekarar 1948 da aka fara yaƙi tsakanin Larabawa da Isra'ila, har yanzu zaman lafiya bai samu ba kuma yakin ya ki karewa.

Ƙasa da shekara 50 da suka wuce a 1973, an gwabza yaƙin Larabawa da Isra'ila. Tun daga wannan loakci kuma ƙasar ba ta sake yaƙi da wata ƙasar Larabawa ba.

Sai dai kuma, rikici tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila bai tsaya ba. Don kawo ƙarshen rikicin da samar da zaman lafiya, an bijiro da tsarin kafa "ƙasa biyu" a lokuta da dama amma kuma ba a aiwatar da shi ba.

Manufar ita ce kafa Isra'ila da Falasɗinu a matsayin ƙasashe biyu. Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ce ta gabatar da ƙudirin a 1947. An tsara Isra'ila a matsayin ƙasar Yahudawa da kuma Falasɗinu a matsayin ta Larabawa.

Lokacin da aka gabatar da ƙudirin, Yahudawan yankin ba su wuce kashi 10 cikin 100 ba. Amma kuma ƙudirin ƙasa biyu ya tanadi cewa a raba yankin daidai tsakaninsu. Ƙasashen Larabawa ba su amince da tsarin ba.

Ƙin amincewar da ƙasashen suka yi ne ya jawo yaƙin Larabawa da Isra'ila na farko. A wani lokaci, Isra'ila da Falasɗinawa sun amince da ƙudirin. Amma dalilin da ya sa aka kasa aiwatar da shi tambaya ce mai wuyar amsawa.

…

Asalin hoton, Getty Images

Yaya tsarin ƙasa biyu yake?

Isra'ila da Falasɗinawa sun gana a karon farko a 1993 don ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da kuma bin hanyoyin aiwatar da tsarin ƙasa biyu, wanda MDD ta ta gabatar a 1947. An yi taron ne a binrin Oslo na ƙasar Norway.

Ana kiran taron da Yarjejeniyar Oslo (Oslo Accord). An sanar da kafa Hukumar Falasɗinawa (Palestinian Authority) ko kuma PA a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da aka cimma. An damƙa wa hukumar iko da Yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.

An tattauna cewa za a aiwatar da tsarin cikin shekara biyar. A gefe guda kuma, Falasɗinawa za su amince da Isra'ila. Sai dai kuma a hankali aka dinga karya ƙa'ida kuma matsaloli suka dinga tasowa.

Me ya sa tattaunawar zaman lafiya ke jan ƙafa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An amince da yarjejeniyar a taron Yarjejeniyar Oslo. Sai dai kuma, babu tabbas game da lokacin da hakan zai faru.

Manyan abubuwa huɗu da suka kai ga neman kafa ƙasashen biyu ba a warware su ba har zuwa yanzu.

Ga manyan abubuwa huɗun:

1. Daga ina za a shata iyakar waɗannan ƙasashen?

2. Wane ne zai mallaki Birnin Ƙudus?

3. Za a kori 'yan Isra'ila da ke zaune a ƙasar Falasɗinawa?

4. Ya batun Falasɗinawan da ke Isra'ila kuma ba su da matsuguni? Ta yaya za su koma gida?

Yarjejeniyar ta ce za a tattauna waɗannan batutuwa ne bayan kafa hukumar PA cikin shekara biyar. Sai dai kuma hakan ba ta samu ba.

Meir Litvak, farfesa kan Nazarin Gabas ta Tsakiya a Jami'ar Tel Aviv, ya ce za a ɗora wa ɓngarorin biyu alhakin ƙin aiwatar da Yarjejeniyar Oslo. "Akwai ɓangarori biyu da suka nuna adawa da yarjejeniyar, su ne Isra'ila da Falasɗinawa," in ji shi.

"Sun ƙi amincewa da yarjejeniyar ce kowannensu na cewa ƙasar tasa ce," a cewarsa.

A ɓangaren Falasɗinawa, ƙungiyoyin Hamas da Islamic Jihad na adawa da yarjejeniyar, a Isra'ila kuma ƙungiyoyiyn Yahudawa masu tsaurin ra'ayi na adawa da ita. Dalilin haka ne ya sa ba a iya aiwatar da Yarjejeniyar Oslo ba.

Hamas da Islamic Jihad sun fara kai wa Yahudawan suka ƙi amincewa da yarjejeniyar hari a 1993. A gefe guda kuma, Firaministan Isra'ila na lokacin, Yitzhak Rabin, wanda ya goyi bayan yarjejeniyar, Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi ne suka kashe shi.

Sai kuma a 1996, wata jam'iyyar masu tsaurin ra'ayi ta karɓi mulki a Isra'ila. Ba ta son ci gaba da maganar yarjejeniyar. Bayan haka, ɓangarorin sun gana a lokuta daban-daban, amma ba a magance matsalar ba.

A lokaci guda kuma, Isra'ila ta mayar da hankali kan gine-gine a yankunan Falasɗinawa. Bugu da ƙari, gwamnatin mai tsattsauran ra'ayi ta ayyana Birnin Ƙudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

A irin wannan yanayi, ko zai yiwu a cimma kafa ƙasar Falasɗinawa a aikace? Mutane da dama na ganin akwai matsala.

Matsugunan Yahudawa a Falasɗinu

Asalin hoton, Getty Images

Za a iya cimma kafa ƙasar Falasɗinawa kuwa?

Isra'ila ta ayyana Birnin Ƙudus, inda yake da Larabawa masu yawa, a matsayin babban birninta. Ƙasashe da yawa, ciki har da Amurka, sun amince da hakan. Saboda haka ne wasu da yawa ke ganin da wuya a iya kafa ƙasar Falasɗinawa a bayyane.

Shaheen Berenji, mai bincike ne kan batutuwa a Gabas ta Tsakiya kuma mazaunin Amurka, "Kafa ƙasar Falasɗinawa yanzu ya ƙara zama abu mai wahala fiye da shekarun 1990," in ji shi.

Matsugunan Yahudawa sun ci gaba da ƙaruwa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Birnin Ƙudus.

Lokacin da aka ƙulla yarjejeniyar Oslo a 1993, Yahudawan da ke wurin 120,000 ne, amma yanzu sun zarta 700,000. Har yanzu kuma ana gina su.

"Waɗannan gidajen na Yahudawa sun saɓa wa doka," kamar yadda Shaheen ya faɗa wa BBC. "Kuma ma Isra'ila ba ta goyon bayan tsarin ƙasa biyu. A gefe guda kuma, Falasɗinawa sun kasu kashi biyu zuwa Fatah da Hamas.

"Saboda haka, babu shugaban da zai ci gaba da neman ƙasar Falasɗinawa."

Za a iya aiwatar da tsarin ƙasa biyu?

Ƙwararru kamar Farfesa Mir Lithwak na ganin har yanzu akwai damar sasantawa tsakanin ɓangarorin. Amma shin Isra'ila na da niyya?

Farfesa Litvak yana ganin Isra'ila ba ta da niyyar yin hakan. "Ina sukar yadda gwamnatin Isra'ila ke kallon lamarin nan. Saboda sun bar matsalar yadda take ba tare da neman mafita ba. Kamar a Yamma da Kogin Jordan.

"Suna son PA ta karɓi iko a can, saboda suna son hukumar da ba ta da wani ƙarfin iko wadda ba za ta iya yin wani aikin kirki a fili ba," a cewar Lithwak.

Lithwak na ganin kuskure ne Isra'ila ta ce sai ta yi iko da komai, kuma za a samu zaman lafiya ne idan Isra'ilar ta zare hannunta. Ya ce matsugunan Yahudawa ne babbar matsalar da ke daƙile kafa ƙasar Falasɗinawa.

"Dole ne sai Amurka ta janye matsugunan Yahudawa a Gaza, gaba ɗayansu, kuma ta zare hannunta daga iko da yankin. Haka ma a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan," kamar yadda ya bayyana.

Haka nan, akwai yiwuwar a iya cimma yarjejeniya game da Birnin Ƙudus idan kowane ɓangare ya rage buri. Amma yanzu da ake tsaka da yaƙi. Abin tambayar shi ne, wane ne zai yakice kikikakar da aka shafe shekara fiye da 100 tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa?

Gaza

Asalin hoton, Reuters

Ko Amurka za ta ɗauki mataki?

Amurka ma na buƙatar ta yi hakan. Ba'amurke mai bincike Shaheen Berenji ya ce idan Amurka ta yunƙura wajen magance wannan matsalar kuma ƙasashe suka taimaka, za a magance matsalar.

"Tun tuni da ma Amurka ta daɗe tana neman yin wani abu a Gabas ta Tsakiya. Yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Masar da Isra'ila, yarjejeniya da Jordan, da kuma Yarjejeniyar Abrahams ta baya-bayan nan hujjoji ne kan haka."

Sai dai ko Amurka na da niyyar samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya?

"Bayan harin 9 ga watan Satumba, Amurka ta fi mayar da hankali kan yaƙi da ta'addanci fiye da aiwatar da Yarjejeniyar Oslo," kamar yadda Shaheen ya bayar da amsa.

Idan aka duba waɗannan abubuwa, Amurka na da damar zama ƙasar da za ta samar da zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila.

Sai dai kuma, tun bayan fara wannan yaƙin na bayan-bayan nan, babu wanda ke magana a kan zaman lafiya. Amurka da Isra'ila da Hamas, duka ba su damu da wannan ba.