Me ya sa hankalin duniya ya karkata kan Zirin Gaza?
Me ya sa hankalin duniya ya karkata kan Zirin Gaza?
Tun bayan hare-haren da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta kai Isra'ila ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba, Isra'ilar ta kashe mutum fiye da 2,200 a Zirin Gaza sakamakon harin ramuwar gayya.
Mutum 1,300 ne mayaƙan Hamas suka kashe, mafi yawansu fararen hula, a harin na ranar Asabar bayan sun tsallaka katangar da ke tsakanin Gaza da Isra'ila.
A wannan bidiyon, mun duba dalilin da ya sa hankalin duniya ya karkata zuwa Zirin Gaza yayin da ake yawan mayar da shi filin yaƙi a rikici tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa na tsawon fiye da shekara 50.
Haruna Ibrahim Kakangi ne ya gabatar.



