Me wasikar da Saddam ya rubuta wa Falasɗinawa kafin kashe shi ta kunsa?

Ciraaq
Bayanan hoto, Marigayi Saddam Hussein

Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta miƙa wasikar da Saddam Hussein ya rubuta, wadda aka wallafa a jaridun ƙasar Jordan biyu a watan Agustan 2005, ga ɗaya daga cikin abokan Saddam da ke zaune a ƙasar ta Jordan.

Mutanen da suka gabatar da wasikar sun ce mutumin ya ki a bayyana sunansa.

An yi imanin cewa ita ce wasika ta farko daga wajen Saddam kafin kama shi a watan Disambar 2003, zuwa ga wanda ba ɗan uwansa ba.

"Na sadaukar da kaina da rayuwata ga mutanen mu na Falasɗinawa da kuma ƙasar Iraqi, waɗanda ke fama da rashin lafiya da wahala," in ji wanda ya rubuta wasikar.

Tayseer Homsi, wanda shi ne babban sakatare na jam'iyyar Bacath ta Jordan, ya ce wannan wasikar da aka aika zuwa ga ICRC, an miƙa shi ne zuwa ga wani ɗan siyasar ƙasar Jordan wanda ba a ci zarafinsa ba.

Israa'ila

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shekarar 1988: Shugaban Falasɗinawa Yasser Arafat tare da Saddam Hussein

Rana Sidani, ta tattauna da tawagar ICRC a Amman, babban birnin Jordan, inda ta ce: "ICRC ta tabbatar da sahihancin sakon da aka wallafa a jaridun ƙasar Jordan."

"ICRC ta karɓi sakon," in ji ta. "An tattauna da gwamnati kafin miƙa wasikar ga ICRC domin yaɗa ta."

Iyalan wani abokin Saddam, wanda ya ki bayyana sunansa, ya ce "ina da tabbacin cewa Saddam ne ya rubuta wasikar ɗari bisa ɗari".

Ƴaƴan Saddam mata biyu, Raghad da Rana, suna rayuwa a Amman bayan tserewa Iraqi lokaci da Amurka ta mamaye ta.

Wannan wasika ta zama sananniya daga baya lokacin da aka fara batun tsige Saddam Hussein a kan mulki.

Ɗaya daga cikin lokutan shi ne lokacin da aka yi wa ƴan Shi'a 150 kisan kiyashi a 1982 a garin Dujail, da ke arewacin Bagadaza.

Saddam ya kasance ɗan Sunni marasa rinjaye, inda masu rinjaye suka haɗa da ƴan Shi'a, da Kurdawa da sauransu.

A watan Aifrilun 2003, aka hambarar da Saddam daga kan mulki bayan Amurka ta mamaye Iraqi.

Israa'iil
Bayanan hoto, Lokacin da aka kama Saddam Husseini

Yadda Saddam ya taimaki Falasɗinawa

Palestine

Asalin hoton, SOCIAL

Bayanan hoto, Falasɗinawa da ke rayuwa a Iraki sun yi fafutukar ganin a kwato musu hakkinsu
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lokacin da aka rataye Saddam Husseini, sojojin ƙwatar ƴancin Larabawa ta gina mutum-mutuminsa a yankin Falasɗinawa.

An yi zaman makoki a birnin Qalqilya, wajen da aka gina mutum-mutumin.

Saddam ya daɗe da nuna goyon baya ga Falasɗinawa kuma ya bai wa iyalan waɗanda aka kashe a harin bama-bamai miliyoyin daloli a shekara ta 2000.

Ya zama sananne a cikin Falasɗinawa saboda harba rokoki zuwa cikin Isra'ila lokacin Yaƙin Gulf a 1991.

A wancan shekarar, an kakkafa allunan da ke ɗauke da rubuce-rubucen Saddam a Zirin Gaza.

Yawancin al'ummar ƙasashen Larabawa sun harzuka da kisan Saddam, sai dai akwai martani daga ɓangaren Falasɗinawa.

Lokacin mulkinsa a Iraqi, Saddam Husseini, ya tabbatarwa Falasɗinawa irin ƴanci da ƴan Iraqi ke da shi, kamar samar da ayyukan yi, ilimi kyauta, kuɗaɗe alawus da kuma abinci.

Sai dai gwamnatin da ta biyo baya ta soke wannan ƴanci, wanda ya janyo Falasɗinawa da dama da ke rayuwa a Iraqi gudanar da zanga-zanga.

Yadda aka kashe Saddam

Saadaam

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan shi ne Lokacin da aka rataye Saddam Hussein

A ranar babbar sallah a shekara ta 2006, aka zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga tsohon shugaban Shugaban ƙasar Iraqi, Saddam Husseini.

Lokacin ya kasance a ranar 30 ga watan Disamba.

An rataye Saddam ne da umarnin gwamnatin Iraqi kafin asubahi, bayan samun shi da laifi a kisan kiyashi da aka yi wa ƴan Iraqi.

Amurka ta tumɓuke shi daga kan mulki ne tsawon shekara 20 da zargin shi da laifin.

Gidan talabijin na ƙasar Iraqi, ya saki wani bidiyo a safiyar ranar da za a rataye shi, wanda ya kasance kafa ta isar da sako na gwamnati, wanda ya nuna Saddam sanye da bakaken kaya, inda wasu mutane ke riƙe da shi shi zuwa cikin ɗakin rataya rufe da kansa da fuskarsa.

Wani alkali ɗan ƙasar Iraqi, Munir Haddad, wanda aka yi komai a kan idonsa, ya faɗa wa gidan talabijin na CNN cewa ɗaya daga cikin mutanen da suka rataye Saddam ya yi wata magana, inda ya faɗa masa cewa Saddam ɗan mulkin kama karya ne wanda ya wargaza Iraqi.

Alkalin ya ce wannan ya janyo cacar-baki nan take tsakanin Saddam da direban da ya ɗauke su, inda sai da masu rataye shi da ke cikin ɗakin suka shiga tsakani.

Labari: Daga sashen BBC Somali.