Yadda aka gaza samun nasara kan binciken makaman sirri na ƙasar Iraqi

Asalin hoton, JIM WATSON
Shekaru ashirin bayan mamayar Iraqi, har yanzu ana samun ce-ce-ku-ce kan ci gaba da kasancewar makaman ƙare dangi a ƙasar wanda kuma ya nuna da hannun Birtaniya a ciki.
An samu sabbin bayanai a wani bincike da BBC ta yi a kan makaman ƙare dangi bayan shekara 20 da mamayar Iraqi da aka yi musamman ma bayan tattaunawa da gwamman mutane da abin ya shafa.
"Abin mamaki." Wannan shi ne martanin da wani jami’in rundunar M16 ya yi lokacin da wani abokin aikinsa ya faɗa masa a 2001 cewa da gaske Amurka take kan yaƙin Iraqi.
Ga Birtaniya, idan aka zo ɓangaren faɗan abubuwa kan Iraqi, musamman irin barazanar da makaman ƙare dangi na ƙasar ke yi – wani abu ne na yin taka tsan-tsan.
A wani lokaci can baya, an bayyana cewa gwamnatin Birtaniya ta bijiro da zargin mallakar makaman ƙare dangi da ake yi a Iraqi. Sai dai, ministoci a lokacin sun ce an tabbatar musu da cewa babu makaman.
"Yana da muhimmanci a gane cewa irin bayanan sirri da nake samu da su na dogara, kuma ina tunanin cewa da bayanan zan dogara,’’ in ji tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair.
Ya ce a jajiberin ranar da za a ƙaddamar da mamayar, ya yi tambaya – kuma an ba shi tabbaci daga kwamitin haɗaka na tattara bayanan sirri. Ya ƙi yin suka ga kwamitin kan gazawa da ya yi.
Wasu ministoci sun ce suna da shakku a lokacin.
"Kusan lokuta uku, na aza ayar tambaya kan bayanan sirri da Richard Dearlove ya bayar,’’ in ji sakataren harkokin waje, Jack Straw. “na matsu kan bayanan. Sai dai, Dearlove ya tabbatar min cewa za a iya dogara da waɗan nan jami’ai.” Amma, mista Straw ya ce hakan nauyi ne da ya rataya kan ƴan siyasa, saboda sune suke ɗaukar mataki na ƙarshe.
Da aka tambaye shi kan gaza samun bayanan sirri a kan Iraqi, Sir Richard ya ce “A’a. “Har yanzu ina da yaƙinin cewa Iraqi na da wasu makamai sannan an ma tsallaka da wasu kan iyaka zuwa Syria.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai wasu basu yarda da hakan ba. “babbar gazawa ce,'' in ji Sir David Omand, mai kula da harkokin tsaro da leƙen asiri na Birtaniya a lokacin. Ya ce nuna son kai ya sa ƙwararrun jami'an gwamnati suka saurari bayanan da basu cika ba da ya goyi bayan ra'ayin cewa Saddam Hussein yana da makaman ƙare dangi, tare da rangwame duk wanda ba shi da shi.
Wasu a cikin jami'an MI6 sun ce su ma sun damu. "A lokacin na ji cewa abin da muke yi bai dace ba," in ji wani jami'in da ya yi aiki a Iraki, wanda bai taɓa yin magana ba kuma ya nemi a sakaya sunansa.
"Babu wani sabon labari ko ingantaccen bincike ko sa ido wanda ya nuna cewa Iraqi ta sake fara shirye-shiryen mallakar makaman ƙare dangi da kuma haifar da wata barazana," in ji tsohon jami'in. "Ina tsammanin daga mahangar gwamnati shi ne kawai abin da za su iya samu.
Jami'an MI6 a Iraqi ba su da wani bayani game da makaman ƙare dangi ko kaɗan, kuma akwai buƙatar son sabbin bayanan sirri daga majiyoyi don ƙarfafa batun, musamman lokacin da aka shirya yin takarda a watan Satumba.
Wani jami'i ya tuno yadda ya naɗi wani sakon murya, inda ya ce "babu wata muhimmiyar rawa" ga hukumar leƙen asirin sama da shawo kan al'ummar Birtaniya kan lamarin don ɗaukar mataki. Sun ce an yi tambayoyi idan hakan ya dace, kuma an goge sakon.

Asalin hoton, DAN KITWOOD
A ranar 12 ga watan Satumba, Sir Richard ya kai ziyara wani wuri a kan titin Downing bayan samun wata majiya da zai samu sabbin bayanai.
Wannan mutumin ya yi iƙirarin cewa ana sake ƙulla shirye-shiryen, Saddam Husseini kuma ya yi alƙawarin bayar da sabbin bayanai nan ba da jimawa ba.
Duk da cewa wannan majiyar ba ta yi cikakken bincike ba, kuma ba a raba bayanansu ga masana ba, an miƙa cikakkun bayanai ga firaministan.
Sir Richard ya yi watsi da tuhumar da ake yi masa na cewa ya kusanci Downing Street a matsayin "abin ba'a", Sai dai, ya ce ba zai yi tsokaci ba kan cikakkun bayanai kan ƙarar ko kan majiyoyi ba.
Sai dai a cikin watanni masu zuwa, ba a taɓa isar da wannan majiya ba, kuma a ƙarshe an yi la'akari da cewa an yi hakan, in ji wasu majiyoyin leƙen asiri. Sun kuma ƙalubalanci cewa abubuwa da dama na taɓarɓarewa.
Sai dai watakila wasu sabbin kafofin na neman bayanai ne don kuɗi ko kuma don su ga an hamɓarar da Saddam. A cikin watan Janairu 2003, na haɗu da wanda ya sauya sheƙa daga hukumar leƙen asirin Saddam a Jordan.
Ya yi iƙirarin cewa yana da hannu wajen samar da ɗakunan gwaje-gwajen tafi-da-gidanka don yin aiki a kan makaman ƙare dangi, ba tare da ganin masu sa ido na Majalisar Ɗinkin Duniya ba.
An sanya iƙirarin nasa a cikin jawabin da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ya gabatar ga Majalisar Dinkin Duniya a watan Fabrairun 2003, duk da cewa wasu a cikin gwamnatin Amurka sun riga sun bayar da sanarwar "ƙonawa", yana mai cewa ba za a amince da bayanan ba.
Wata majiya mai suna "Curveball", wadda Amurka da Birtaniya suka dogara da ita, ita ma tana neman yin cikakkun bayanai game da ɗakunan gwaje-gwajen.

Asalin hoton, Getty Images
Ana kuma tuna cewa Saddam ya taɓa mallakar makaman ƙare dangi. Makonni kaɗan kafin yaƙin 2003, na ziyarci ƙauyen Halabja da ke Arewacin Iraqi, na kuma ji mutanen yankin suna bayyana ranar a 1988 da sojojin Saddam suka jefa musu makamai masu guba.
Gaskiyar abin da ya faru da waɗan nan makaman ya bayyana ne bayan yaƙin.
Saddam ya bayar da umarnin lalata yawancin shirinsa na mallakar makaman ƙare dangi a farkon shekarun 1990 bayan yakin Gulf na farko da fatan samun ƙudurin lafiya daga masu sa ido kan makamai na Majalisar Ɗinkin Duniya, kamar yadda ɗaya daga cikin manyan masana kimiyya na Iraqi ya shaida min.
Mai yiwuwa shugaban na Iraqi ya yi fatan sake fara shirye-shiryen a wani lokaci. Amma ya lalata komai a asirce, domin ya ci gaba da kasancewa da wani abin da zai iya amfani da shi a kan maƙwabciyarta Iran, wadda suka yi yaƙi da ita.
Sai dai daga baya lokacin jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya suka nemi Iraqi da su tabbatar da cewa sun lalata komai, sun kasa yin hakan.
Daga baya wani masanin kimiyya na Iraqi ya bayyana cewa sun yi watsi da wani wuri mai haɗari da hukumomin leƙen asirin ƙasashen yammacin duniya suka ce ba a san inda yake ba, ta hanyar zuba shi a ƙasa.
Amma sun yi haka a kusa da ɗaya daga cikin fadar Saddam Husseini, kuma suna fargabar cewa sanin wannan gaskiyar zai sa shugaban Iraqi ya kashe su.
Sakamakon duk wannan shi ne cewa Iraqi ba za ta taɓa iya tabbatar da cewa ba ta da makamai ba.
A ƙarshen 2002, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun dawo Iraqi suna neman makaman ƙare dangi.
Wasu daga cikin masu sa ido, da suka yi magana da BBC a karon farko, sun tuna da duba wuraren da bayanan sirri daga ƙasashen Yamma, suka nuna cewa za a iya kafa ɗakunan gwaje-gwajen wayar hannu.
Abin da kawai suka gano shi ne abin da ake kira da "motar ɗaukakar ice cream" lulluɓe cikin yanar gizo-gizo.
Jama'a a lokacin ba su taɓa sanin cewa yaƙi na tinkaro su ba, inda majiyoyi suka kasa kai wa, sannan kuma masu binciken sun yi ta jan kunne da kuma nuna damuwa. "Makomata tana hannunku," in ji Mista Blair, cikin ɓacin rai, ga Sir Richard a cikin Janairu 2003, lokacin da matsin lamba ke ƙaruwa don nemo shaidar mallakar maƙaman kare dangi.

Asalin hoton, Getty Images
"Abin ɓacin rai ne a lokacin," in ji Sir Richard. Ya zargi masu sa ido da rashin ƙwarewa saboda gaza samun bayanan da ake buƙata.
Hans Blix, wanda ya jagoranci tawagar bincike kan duba makaman ƙare dangi na Majalisar Dinkin Duniya, ya faɗa wa BBC cewa kafin fara aikin a 2003, yana da yaƙinin cewa akwai makaman ƙare dangi, sai dai ya fara sa shakku kan haka bayan fara binciken. Ya ce yana son ƙarin lokaci domin samun bayanai, amma ba zai samu hakan ba.
Rashin samun “bayanan aikata laifi” bai sa an dakatar da yaƙi da aka yi a watan Maris ɗin 2003.
"Na yi iyaƙar ƙoƙarina wajen ganin ban shiga aikin soja ba,’’ In ji Tony Blair a tattaunawa da BBC.
Shugaba George Bush, cike da fargabar cewa ƙawayensa za su yi rashin nasara a ƙuri’ar da majalisa za ta ƙada a jajiberin fara yaƙin, ya bayyana a cikin wani hoton bidiyo, inda ya ja da baya kan mamayar, amma ya nuna cewa yana son a dama da shi bayan yakin, sai dai firaministan ya ki aminta da hakan.
Ya kare matakin nasa duka bisa ƙa'ida dangane da buƙatar yin mu'amala da Saddam Hussein, amma kuma saboda buƙatar ci gaba da ƙulla alaƙar da Birtaniya da Amurka.
"Da hakan zai yi tasiri sosai kan dangantakar," in ji shi, ya ƙara da cewa: "Lokacin da nake Firaminista, babu shakka ko dai a ƙarƙashin Shugaba Clinton ko Shugaba Bush, kiran wayar waye shugaban Amurkar ya fara ɗaukawa ba. Yau mun fita daga Turai kuma Joe Biden ya ɗauki wayar zuwa ga Rishi Sunak? Bani da tabbacin haka."
Amma ba za a samu wani makamin ƙare dangi daga baya ba. Wani tsohon jami'in MI6 ya ce, "Duk abin ya wargaje, yayin da yake tunawa da wani nazari na cikin gida da aka yi bayan yaƙin. Kuma wannan zai bar babban sakamako mai ɗorewa ga 'yan leƙen asiri da 'yan siyasa.











