Mutumin da ya rasa duka ƴaƴansa huɗu a hari ɗaya da Isra'ila ta kai

Bai taɓa raba ɗaya biyu ba game da abubuwan da idanuwansa ke gani lokacin da yake bincika ɓaraguzai.
Khalil Khader ya zaƙulo mayafi cike da datti na ƴarsa daga ɓaraguzai kuma nan take jimami ya mamaye shi.
Ƴarsa lulluɓe da mayafi. Rosa, ƴarsa wata 18 da haihuwa, jaririyar da kowa ke ƙauna a danginsa.
Khalili ya nuna wani bidiyo daga wayarsa. Rosa na sanye da kayan barci shuɗaye riƙe da hannun 'yan uwanta biyu. Su ukun suna rawa tare.
An ɗauki bidiyon a tsarin "slow" ta yadda aka nuna yaran na cikin jin daɗi na musamman. Suna ta murmushi. Lokacin wasa ne kafin yaƙi ya mamaye rayuwarsa gaba ɗaya.
Khalil ba mutum ne mai magana ba, mai shekara 36, injiniyan kwamfuta a asibitin Al-Najjar da ke Rafah, kuma mahaifin yara huɗu. Ibrahim mai shekara tara; Amal mai biyar; Kinan mai biyu da rabi; da kuma Rosa 'yar auta.
Khalil na tsallaka ɓaraguzan a hankali. Gidan nasa ɗan taƙi ne daga asibitin.
Yanzu ya zama wata dalar ɓaraguzai da ƙarafa, da kayan gida, da kuma kayan wasan yara. Nan ga ƴar ƙaramar ganga, can ga ƴar garayar wasan yara.

Asalin hoton, Khalil Khader
A daren da makamin ya faɗo musu - ranar 20 ga watan Oktoba - Khalil na asibiti wajen aiki.
"Wani ƙatoton bam ne ya fashe," kamar yadda ya faɗa wa ɗaya daga cikin abokan aikina na BBC.
"'Ina aka kai harin?' Sai suka ce min a kusa da gidana ne.'Haka na bazama zuwa wurin don duba lafiyar iyalina. Na yi ta kira amma babu wanda ya amsa. Kamar yadda kuke gani...an yi kaca-kaca da gidan."
Danginsa mutum 11 aka kashe a harin.
Sun haɗa da 'ya'yansa huɗu, 'yan uwansa mata biyu, mahaifinsa mai shekara 70, ɗan uwansa da surikarsa tare da 'ya'yansu mata biyu.
An ji wa matarsa mummunan rauni. Ana kula da ita saboda ƙuna da kuma sauran raunuka da ta ji bayan rushewar ginin.

Asalin hoton, Khalil Khader
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Khalil ya fuskanci yaƙi a Gaza kafin yanzu. Ɗan ƙaramin zirin - da ke da jimillar faɗin ƙasa murabba'in mil 141 (kilomita 365) - wanda ya sha fama da yaƙi tsawon shekaru.
"Ina iya tuna yaƙin 2014, matata tana da ciki," a cewarsa. "An kai wa maƙwabtana hari. Tana da cikin wata bakwai amma sai da ta kusa faɗowa daga kan matattakala saboda ƙarfin fashewar. Nan na fara tunanin ta yaya zan haifi yara a irin wannan yanayi"?
Amma kuma ya yi tunanin cewa komai zai warware.
"Ina fata ga kowanne daga cikin 'ya'yana. Na yi fatan Ibrahim ya zama likita wata rana. Amal na da basira sosai, tana son zane-zane. Ta sha nuna min zanen da ta yi, wani zubin kuma tare muke yi.
"Kinan na da son wasa - kowa na ƙaunar sa.. Yana da son kula da 'yar uwarsa. Kodayushe yana kusa da Rosa don ba ta kariya, sai ka ji ya ce 'kada ku taɓa ta, jaririyata ce!' Amma yanzu duk sun tafi."
Har yanzu Khalili na neman gawar 'yar uwarsa a ƙarƙashin ɓaraguzai. A gefe guda kuma yana taimaka wa matarsa da ke asibiti. An kashe 'ya'yansa duka.
Yayin da yake nuna hoton Ibrahim, da Amal, da Kenin, da Rosa, idanunsa sun nuna alamar rauni.
Ba zai taɓa gushewa ba a matsayinsa na mahaifinsu.











