Bayani game da abubuwan da ba ku sani ba kan rikicin Isra’ila da Gaza

Asalin hoton, Reuters
Sama da mako uku ke nan da Hamas ta kaddamar da wani hari da ba a taba ganin irin sa ba a Isra'ila, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 1,400.
Isra'ila ta mayar da martani da kazamin harin bama-bamai a zirin Gaza, wanda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce ya kashe fiye da mutane 5,000.
Shugabannin kasashen yammacin duniya sun kai ziyara Isra’ila domin nuna goyon bayansu ga kasar da kuma neman shugabannin Isra’ila da su bi dokokin kasa da kasa da kare fararen hula a Gaza.
Ana sa ran Isra'ilar za ta kai hari ta kasa a Gaza, ko da yake babu tabbacin lokacin da hakan ka iya faruwa.
Halin da ake ciki a yakin na kara rincabewa, don haka wakilanmu da dama a yankin sun yi huɓɓasa domin yin karin bayani da kuma wayar muku da kai da kuma amsa wasu tambayoyin da kuka aikowa BBC kan wannan lamari.
Mene ne tabbacin yaƙin zai iya girmama?

Asalin hoton, Getty Images
Wannan tambaya ce da kuma samu daga Richard Jones, wanda yake neman karin bayani a kan ko wannan yaki zai iya girma ya shafi yankin gabas ta tsakiya baki daya? Sannan ko yana iya haifar da barazana ga Isra'ila?
Wakilinmu na harkokin diflomasiyya Paul Adams da ke aiko mana rahotanni daga birnin Ƙudus (Jerusalem), ya ce kowa zai iya fahimtar babban dalilin da ya sa wasu shugabannin kasashen duniya suka yi ta zuwa Isra'ila domin nuna goyon bayansu ga ƙasar a ƴan makwannin da suka gabata.
Babban barazanar ita ce wadda ake fuskanta a iyakar arewacin Isra'ila, inda a kowace rana ake ta musayar wuta tsakanin sojojin Isra'ila da kuma mayaƙan ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon mai samun goyon bayan Iran.
Isra'ila ta jibge sojoji da makamai a iyakarta da Lebanon din, tare da kwashe dubban fararen hula daga garuruwan kan iyaka.
Hizbullah dai na samun goyon bayan Iran, kuma ta yi gargadin cewa mai yiwuwa ne ta shiga yaƙin idan har al'amura a Gaza suka ci gaba da kazanta.
Ga Isra'ila, tarin makamai masu linzami da Hezbollah ke da su wani abun tsoro ne, don haka wannan babbar barazana ce a gare ta fiye ma da Hamas, nesa ba kusa ba.
Amurka ta aike da karin makamai ga Isra'ila a matsayin tallafi don kare kanta, da kuma wasu jiragen ruwa na yaki biyu zuwa gabashin Bahar Rum, tana cewa ta yi hakan ne domin dakile duk wani yunkurin shiga yakin da Hezbolla da Iran za su iya yi.
To sai dai yayin da halin da ake ciki ke da ban tsoro, har yanzu babu wani ƙwaƙƙwaran mataki da Hezbolla ta ɗauka da zai iya nuna cewa za su shiga yaƙin.
Shin abinci da man fetur na shiga Gaza?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tambayar da muka samu daga Caroline Kelly ke nan, game da dokar ba shiga ba fita da Isra'ila ta kafa a zirin Gaza bayan fara yakin, tana neman karin bayani a kan ko hakan yana nufin cewa a zahiri babu ruwa da man fetur da wutar lantarki ga mutanen Gaza a halin da ake ciki?
Wakilinmu na Gabas ta Tsakiya Tom Bateman, a Urushalima, ya ba da amsa:
Isra'ila ta ce har yanzu wannan doka na nan daran-dam Ministan makamashi na kasar Katz ya ce bayan harin na Hamas, Isra'ila za ta daina ba wa Gaza wutar lantarki da ruwa har sai an sako mata mutanenta da Hamas ta yi garkuwa da su.
Tun a shekara ta 2006, Isra'ila ta kakaba dokar takaita zirga-zirga a gaza bayan da Hamas ta karfafa ikonta a yankin, ta ce ta yi hakan ne da nufin dakatar da shigar da kayan da ake kera makamai da su.
To amma kuma hakan ya jefa rayuwar ƴan Gaza cikin matsi da wahala sosai, kuma duk da hakan Hamas ta samar da wasu hanyoyin karkashin kasa da take iya shigo da duk abun da take so daga Masar.
Shin Isra'ila za ta iya ceto mutanen da aka yi garkuwa da su?

Asalin hoton, Getty Images
Mun samu wannan tambaya ne daga wani sakon email da babu suna, inda ya ke neman karin bayani a kan ko akwai yiwuwar Isra'ila ce mai aika imel da ba a bayyana sunansa ba: Yaya yuwuwar Isra’ila za ta iya ceto mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su?
Wakilinmu kan sha'anin tsaro Frank Gardner ya ce saboda yawan mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza fiye da 200 ceto su na da matukar wahala musamman idan aka ce za a yi amfani da karfin tuwo.
Kamar yadda muka sani, an sako wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su zuwa yanzu, bayan shiga tsakani da Qatar ta yi.
Qatar ta yi imanin cewa za a iya samun maslaha ta hanyar tattaunawa, wannan ne ma ake tunanin ya janyo jan kafar da Isra'ila ke yi a yunkurinta na kai hari ta ƙasa zuwa zirin na Gaza.
Ta ina Hamas ke samun kuɗi?

Asalin hoton, Getty Images
Rosemary Maltus ce ta aiko mana da wannan tambaya,
Yolande Knell, wakiliyarmu ta Gabas ta Tsakiya da ke a birnin Kudus, ta ce a farkon kafa kungiyar Hamas ta rika samun kudinta ne daga wasu hamshakan Falasdinawa da kuma kungiyoyin musulmai na gabas ta tsakiya, to amma wananhanyar ta katse bayan da kasashe da dama suka ayyana kungiyar a matsayin ta ƴan ta'adda.
Abu dai mafi muhimmanci shine a yanzu kungiyar Hamas na samun tallafi ne daga kasar Iran, kama daga kan na kudi da kuma makamai.
A cikin 'yan shekarun nan da kasar ta shiga matsin tattalin arziki, Qatar wadda ke taimakawa Falasɗinawa ta rika biyan ma'aikata albashi a Gaza
Shima Baitul malin Amurka ya ce kungiya na da wasu hanyoyin samun kudi da hannayen jari a harkokin kasa da kasa da ke samar mata da kudaden shiga, kuma yanzu haka tana da arzikin da yawansa ya kai daruruwan miliyoyin daloli.
Tana da hannayen jari a wasu kamfanonin da ke aiki a kasashen Sudan, da Aljeriya, da Turkiyye, da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma ƙarin wasu kasashe.
Shin kasashen Yamma za su yi iya kira da a tsagaita wuta?
Wannan ita ce tambayar da muka samu daga Mary Freeman, tana mai ƙarawa da cewa shin rayukan fararen hula nawa ne ake jira a rasa kafin kasashen Yamma su yi kiran a tsagaita wuta?
Wakilinmu Paul Adams ya amsa wannan tambaya da cewa adadin wadanda suka mutu ya zuwa yanzu yana da yawa. Fiye da Isra’ilawa 1,400 ne aka kashe sannan kuma Falasdinawa sama da 5,000, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza.
Wannan mummunar hasarar rayuka ne mai yawan gaske.
Daga abin da na gani na tashe-tashen hankulan da suka faru a baya, kasashen Yamma sun bai wa Isra'ila lokaci don hukunta Hamas kafin su fara kira da a tsagaita wuta, gaba daya gwamnatocin kasashen yammacin duniya na nuna jin dadinsu ga muradin Isra'ila na hukunta Hamas.
Ƙila a iya cewa ba a kai wani mataki da za a ce Hamas ta dandana kudarta ba zuwa yanzu.
Shin Fatah za ta sake gudanar da mulkin Gaza?
Alex a Cyprus yana son sanin ko akwai wata alama da ke nuna cewa kungiyar Fatah za ta iya karbar jagorancin gaza?.
Yolande Knell Ta amsa wannan tambaya da cewa da fari dai Fatah ƙungiya ce ta siyasa wacce ita ce babbar abokiyar hamayyar Hamas.
Shugaban Fatah shi ne shugaba Mahmoud Abbas wanda ke jagorantar Falasdinawa, da ke mulkin wasu sassan gabar yammacin kogin Jordan da Isra'ila ta mamaya.
Shi ne kuma shugaban kungiyar 'yantar da Falasdinu (PLO) wacce ita ce kungiyar da kasashen duniya suka amince da ita a matsayin wadda ke wakiltar al'ummar Palasdinu.
Hamas da Islamci Jihad ba sa cikin kungiyar PLO, wadda ita ce mai shiga tsakani a tattaunawar sulhu kai tsaye da Isra'ila a baya.
Fatah ce ke mulkin Gaza a baya, amma Hamas ta mamaye yankin a shekarar 2007, inda ta kori jami'an tsaron Fatah shekara guda kenan bayan ta lashe zabe.
Mun ga Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken yana ganawa da Shugaba Abbas lokacin da ya ziyarci Jordan bayan fara yakin.
Me Isra'ila za ta yi ta wuce iyaka?

Asalin hoton, Getty Images
Sam, na son sanin ko akwai wani mataki da Isra'ila za ta iya dauka da za a kalla a matsayin wuce kima?
Frank Gardner ya bayar da amsa da cewa: Idan ma akwai to zuwa yanzu dai ba mu ji komai ba, sannan babu wata matsaya guda da kasashen suka dauka kamar yadda suka yi lokacin da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine.
Hasalima taruwa kasashen suka yi don nuna goyon baya ga Isra'ila bayan harin na bakwai ga watan Oktoba da Hamas ta kai.
Sai dai yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare zirin Gaza, wasu kasashe da ke da kusanci da Isra'ila sun fara gargadin cewa Netanyahu ya fara zarce iyaka, ya fara wuce gona da iri.
"Kada ku makantar da fushi kamar yadda muka kasance a Amurka bayan 9/11" shine sakon da shugaba Biden ya yiwa Isra'ila a takaitacciyar ziyarar da ya kai a makon jiya.
''Kada bacin rai da bakin ciki ya rufe maka ido kamar yadda hakan ta faru a kanmu bayan harin sha daya ga watan Satumba'' wannan ita ce shawarar da shugaban Amurka Joe Biden ya ba wa Netanyahu lokacin ziyarar da ya kai Isra'ila a baya-bayan nan.











