Mene ne hatsarin shiga yaƙi ta kasa a Zirin Gaza?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Feras Kilani
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
Isra'ila na tattara dubun dubatar dakaru a kusa da iyakarta da Zirin Gaza, yayin da take shirin ƙadamar da hari ta ƙasa.
Idan dakaru sun kutsa kai, sojojin Isra'ila za su fafata da Hamas a cikin garin da ke da yawan jama'a.
Wakilin Sashen Larabci na BBC Feras Kilani, wanda ya shaida yaƙe-yaƙe a Gabas ta Tsakiya ya duba yadda yaƙin zai iya kasancewa.
Yayin wata ziyara a sansanin 'yan gudun hijira na Al-Shati da ke arewacin Gaza shekara biyar da ska wuce, na lura da wani sauti lokacin da muke wucewa. Kamar muna wucewa ta kan gada saɓanin dandagaryar ƙasa.
Mai ɗaukar hoton da muke tare da shi ya ce min saboda a can ƙarƙashin ƙasar, an fafake shi don gina doguwar hanya. Hamas ce ta gina hanyar da ke da tsawon kilomita masu yawa domin samun damar shigar da kayayyaki birnin ba tare an gan su ba.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ci alwashin "rusawa da tarwatsa" Hamas bayan ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoba da ya kashe mutum 1,400 a Isra'ila.
Dakarun Isra'ilar tuni suka ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya ta sama a kan Gaza kuma mataki na gaba shi ne hari ta ƙasa. Idan hakan ta faru, waɗannan hanyoyin ƙarƙashin ƙasar za su zama babbar dabara ga Hamas a yaƙin.

Asalin hoton, Getty Images
Hamas ta san za a kawo hari ta ƙasa kuma ba mamaki ta tanadi abinci da ruwa da makamai. Hanyoyin ƙasan da aka amince cewa suna kaiwa har cikin Isra'ila, za su bai wa mayaƙan damar yawo ba tare da wata matsala ba don yi wa dakarun Isra'ila kwanton-ɓauna.
Isra'ila ta ce Hamas na da mayaƙa 30,000 da ke iya aiki da manyan bindigogi, da manyan makaman gurneti da na harbe tankar yaƙi. Kazalika, sauran ƙungiyoyi kamar Islamic Jihad za su ƙara wa adadin mayaƙan yawa.
Tarihi na baya-bayan nan ya nuna mana irin haɗrin da ke tattare da yaƙi a cikin gari, kuma na gani da idona yadda sojoji masu horo sosai suka yi yunƙurin yi wa mayaƙa ƙawanya a irin wannan yanayi.
Yaƙin cikin gari
A 2016, ina tare da dakarun Iraƙi na musamman lokacin da suka fara kai hari garin Mosul.
Dakarun gwamnati sun tabbatar da cewa sun zagaye mayaƙan tare da hana su wata hanya da za su iya guduwa. Hakan ya sanya garin cikin haɗarin ƙazamin yaƙi.
Ranar farko da muka shiga birnin Mosul, ƙwarin rai da mayaƙan nan suka nuna ya zarta misali. Suka dinga harba mana abubuwa kan jerin motocinmu masu sulke da makamai da makaman da suke harbawa daga kafaɗa.
Sun saka tarko kusan a kan komai - a na'urar firji da talabijin ta na gidajen mutane, da fitilu, har ma bindigogin da suka zubar a ƙasa.
Duk abin da ka taɓa ko ka tsaya a kai mutuwa ce kawai.
Dakarun Isra'ila za su iya fuskantar irin wannan yanayin idan suka shiga Gaza.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ƙarshen yaƙin na Mosul, na lura cewa manufar dakarun Iraƙi da yawa ta sauya. Fafatawar ta yi tsanani kuma ta zama mai haɗarin gaske, har ma suka koma tunanin yadda za su tsira tare da tunanin daina bai wa fararen hula kariya.
Wani haɗarin shi ne na ɓoyayyun maharba, waɗanda za su ɓuya a kan gine-gine da kuma cikin ɓaraguzai. Sojojin Iraƙi sai da suka koma dasa bam ta sama, su lalata wuri mai yawa don su gama da su.
Dakarun Isra'ila za su fuskanci zaɓi ɗaya cikin biyu; ko dai su yaƙe maharbar da ke da ƙwarewa ba Hamas, ko kuma su dinga ragargaza gine-gine.
Motocinmu da muke ciki a Mosul sun fuskanci hare-haren bam a mota da yawa, inda biyar daga cikin dakarun da muke tafe tare da su suka mutu cikin wata fashewa daga baya.
Irin ɗimuwar da waɗanda suka tsira a harin suka shiga, waɗanda suka rayu da mutanen da suka mutu a harin, a bayyane take.
Ba a san Hamas da amfani da bama-bamai na mota ba, amma ta yi amfani da 'yan ƙunar-baƙin-wake a baya, kuma akwai haɗari mai yawa da hakan zai iya haifar wa dakaru.
Babu tabbas kan tsawon lokacin da hari ta ƙasa a kan Gaza zai ɗauka, amma zazzafan yaƙin da mayaƙan Islamic State suka yi a Mosul ya nuna cewa sai da dakarun Iraƙi suka ɗauki wata tara kafin su ƙwace birnin.

Hanyar tsira
Lamarin ya sha bamban a birnin Raƙƙa na Syria a 2017, inda aka zagaye mayaƙa a wani wuri mai cike da al'umma. Amma wannan karon, dakarun da sojojin Amurka da na Ƙurdawa ke jagoranta sun bai wa mayaƙan damar guduwa.
Na aiko da rahotonni game da gwagwarmayar Ƙurdawa a kan ƙungiyar IS, wata rana ɗaya daga cikin kwamandojinsu ya ɗauke ni zuwa wata ganawa da wani kwamandan Amurka a Syriya. Ya amince da roƙon shugabannin Larabawa cewa a ƙyale mayaƙan IS da iyalansu su gudu daga Raƙƙa.
Wannan yarjejeniyar ta sa ba a lalata birnin ba baki ɗayansa saboda yaƙi, abin dake nufin adadin mutanen da suka jikkata a ɓangaren sojoji da kuma farar hula ba su da yawa kamar a Mosul.
Kwana ɗaya bayan mayaƙan sun gudu daa garin, fararen hula ska fito daga gidajensu da murnar tsira da rayuwarsu. Sun shiga firgicin cewa za su mutu a harin da za a kawo kan birnin.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai yanayin birnin Gaza ba lallai ne ya ba da damar ƙulla irin wannan yarjejeniya ba. Raƙƙa wani ƙuye ne a Syriya, mayaƙan da aka ba wa dama su gudu za su tsallaka gefen ƙasar ne.
Zirin Gaza ƙarami ne idan aka kwatanta da Raƙƙa kuma babu inda mayaƙan za su iya tsallakawa.
Gudun hijira
A baya, an sha cimma yarjejeniyar tura mutane nesa. A shekarar 1982, ƙungiyar Palestinian Liberation Organisation (PLO) ta amince ta bar Lebanon, inda dakarun Isra'ila suka kewaye ta tsawon wata uku, inda suka koma wasu ƙasashe.
Shugabannin PLO sun koma Tunisiya yayin da wasu suka nemi mafaka a arewacin Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya.
Duk da cewa irin wannan yarjejeniya za ta rage yawan kashe-kashe a Gaza, amma abu ne mai wuya a iya ƙulla ta. Gwamnatin Isra'ila ta ci alwashin tarwatsa Hamas, saboda haka barin shugabannin ƙungiyar su koma wata ƙasa zai jawo mata suka.
Idan har ba a samo wata mafita ba, arewacin Gaza zai zama ƙazamin filin yaƙi a kan tituna tsakanin dakarun Isra'ila da na Hamas, kuma hakan zai iya ritsawa da dubban fararen hula.










