Wanne irin taimako mutanen Gaza ke buƙata?

Wani Bafalasdine yana dauke da buhun garin flawa da aka bayar a matsayin taimako ga iyalai a cibiyar rabar da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Shati da ke birnin Gaza a ranar 31 ga Yuli, 2023.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iyalai da yawa a Gaza sun dogara da taimako kamar na garin flawa. An dauki hoton nan a sansanin 'yan gudun hijira na Al-Shati a ranar 31 ga Yuli 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa a halin yanzu Gaza na fuskantar matsanancin karancin abinci da man fetur, da ruwan sha yayin da dubban tan na agaji ke shirin shiga ta kan iyakar yankin da Masar.

Rikicin Isra'ila da Hamas ne ya haifar da wannan mummunan yanayi, wanda ya sa shugabannin duniya da kungiyoyin agaji suka yi kira da a bayar da agajin gaggawa zuwa Gaza.

Yayin da ake sa ran kusan manyan motoci 20 dauke da kayan abinci da ruwa da magunguna za su shiga ta kan iyakar kudancin yankin da Masar a cikin kwanaki masu zuwa, babban jami'in bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths ya jaddada cewa ana bukatar tireloli 100 na agaji a kowace rana domin bayar da taimako ga mazauna Gaza miliyan 2.1.

Me ya sa ba za a iya kai agajin gaggawa zuwa Gaza ba kuma me ake bukata?

An ajiye motar ayarin motocin agaji ga Zirin Gaza a wajen kofar iyakar Rafah, Masar, 18 ga Oktoba, 2023.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Motar agajin jin ƙai da aka yi niyya zuwa Zirin Gaza ta taso a kan iyaka da Masar a ranar 18 ga Oktoba

Isra'ila da Masar dai sun kakaba takunkumin hana zirga-zirgar kayayyaki da jama'a zuwa Gaza tun bayan da Hamas ta karbe ikon yankin a shekara ta 2007.

Suna masu cewa kangewar ta zama dole saboda dalilai na tsaro. An kange Gaza da wani shingen da ke hana shige da fice.

Akwai mashiga guda uku da ake kula da su sosai, duk an rufe su bayan harin da Hamas ta kai Isra’ila wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 1,400.

Dangane da harin na ranar 7 ga watan Oktoba, ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant ya ba da umarnin "cikakkiyar killacewa" a Gaza, yana mai cewa ba za a samu wutar lantarki da abinci, ko man fetur ba, kuma za a rufe dukkan wuraren shiga.

Tun farkon rikicin baya-bayan nan, Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoton mutuwar mutum 3,785 da waɗanda suka jikkata 12,500 a yankin.

An rufe biyu daga cikin mashigar Gaza, Erez da ke arewacin yankin da Kerem Shalom a kudancin yankin, masu kai wa Isra'ila.

Hanya ta uku, Rafah, zuwa Masar, ita ce hanya daya tilo da za ta iya kai kayan agaji. Sai dai hare-haren na Isra'ila sun lalata hanyar, kuma ana ƙoƙarin gyara ramuka domin samun damar wucewar manyan motoci lafiya.

Me Isra'ila ta ce game da taimakon Gaza?

Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Isra'ila ta bayyana cewa ba za ta bari wani taimako ya bi ta cikin kasarta ba har sai an sako mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

A cewar mai magana da yawun sojin Isra'ila, ana kyautata zaton an yi garkuwa da mutane aƙalla 203 da suka hada da kananan yara 16 a harin na ranar 7 ga watan Oktoba.

Bayan tattaunawa da shugaban Amurka Biden, Isra'ila ta amince da barin wasu kayan agaji shiga Gaza daga Masar ta kan iyakar Rafah.

Sai dai mahukuntan Isra'ila sun bayyana ƙarara cewa idan har akwai alamun Hamas na yunƙurin ƙwace kayan agajin da aka bari a kai Gaza, to za su dauki mataki.

Ina ne mashigar Rafah?

...
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dangane da rikicin Isra'ila da Hamas da ke ci gaba da ruruwa, mashigar Rafah ta zama abin da aka fi mayar da hankali a matsayin muhimmiyar hanyar shigar da kayan agaji zuwa Gaza.

Tana a kudancin Gaza, ita ce mashigar kan iyaka da ba ta da alaƙa kai tsaye da Isra'ila, a maimakon haka ta ba da damar shiga yankin Sinai na Masar.

Masar ta bayyana shirin sake buɗe wannan mashigar ta Rafah domin bai wa masu fasfo na kasashen waje damar ficewa daga Gaza da kuma sauƙaƙa kai kayan agaji.

Ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shoukry, ya bayyana wa BBC cewa, ta fuskar Masar, mashigar Rafah da ke bangarensu a hukumance a bude take, duk da haka, ya daura laifin rashin amfani da hanyar tsallakawar a kan hare-haren Israila ta sama, wanda ya sa motocin agaji ba za su iya kai kaya ba.

Shugaban Masar Abdel Fattah El-Sisi ya jaddada mahimmancin zaman jama'ar Gaza a kasarsu domin kare lamarin Falasɗinawa, yayin da ya kuma bayyana damuwarsa kan yiwuwar kutsawar masu iƙirarin jihadi cikin Masar sakamakon hare-haren da suke ke ci gaba da yi a yankin Sinai.

Wane ne ke aikawa da taimako zuwa Gaza?

Ma'aikata sun loda wani jirgin sama da zai nufi Masar dauke da kayan agaji da kayan agaji zuwa zirin Gaza

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ƙungiyar agaji ta ƙasashen duniya da ke Dubai ta aika da kayan agaji da aka yi niyya zuwa Gaza

Kimanin tan 3,000 na kayan agaji ne aka jibge a mashigar Rafah, tare da muhimman kayan abinci da man fetur da ruwa da kuma magunguna da ke jira kasa da kilomita ɗaya daga kan iyakar, da ke shirin shiga Gaza.

Phillippe Lazzarini, babban kwamishinan hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), ya yi gargadin cewa wani bala'i da ke kunno kai, yana mai jaddada buƙatar samar da amintacciyar hanya cikin gaggawa don tabbatar da samar da kayan masarufi.

Da yake amsa wata muhimmiyar buƙata daga Hukumar Abinci ta Duniya, da Hukumar Lafiya ta Duniya, da UNICEF da Cibiyar Ba da Agajin Gaggawa ta Duniya a Dubai, sun ƙaddamar da neman kawo tallafin muhimman kayan buƙatu daga ƙasashen ƙetare zuwa filin jirgin sama na El-Arish da ke arewacin Masar.

Bayan haka, filin jirgin ya samu kwararar kayan agaji da suka hada da kayan abinci da safar hannu ta ma'aikatan lafiya.

Daga nan sai aka loda waɗannan kaya a kan manyan motoci, sannan aka dauke su na nisan kilomita 45 zuwa mashigar Rafah, inda suke dakon hanyar shiga Gaza.

An dai ci gaba da gudanar da shirye-shiryen diflomasiyya don sauƙaƙa kai kayan agaji, tare da ziyarar shugaban Amurka Joe Biden da firaministan Burtaniya Rishi Sunak zuwa Isra'ila, inda suka gana da firaminista Israila Benjamin Netanyahu.

Wata yarjejeniyar ba da damar shigar da kusan manyan motoci 20 dauke da abinci da ruwa da kayan kiwon lafiya zai iya ba su damar shiga Gaza a cikin kwanaki masu zuwa.

Za a bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta duba waɗannan kaya tare da yi musu jagora da kuma taimakon kungiyar agaji ta Red Crescent ta Masar da wata ƙungiyar jin ƙai, don tabbatar da cewa babu wani abu da ya wuce na agaji ya shiga yankin.

Ma’aikatan agaji sun bayar da rahoton cewa suna jira a gefen mashigar Masar na tsawon kwanaki, suna neman izinin raba kayan agajin gaggawa.

Mohsen Sarhan na gidauniyar abinci ta Masar ya bayyana takaicinsa na rashin samun taimako duk da cewa akwai motocin agaji 120 da wasu jiragen dakon kaya da dama da ke dauke da kayayyaki daga Turkiyya a jibge a kan iyakar.

Ya kuma jaddada matuƙar buƙatar agaji, ganin yadda al'ummar Gaza ke fama da karancin ruwan sha.

Man fetur da ruwa fa?

Motocin mai dauke da tutar Majalisar Dinkin Duniya suna tafiya zuwa mashigar Rafah a kudancin zirin Gaza, a ranar 16 ga Oktoba, 2023

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Motocin mai dauke da tutar Majalisar Dinkin Duniya suna tafiya zuwa mashigar Rafah a kudancin zirin Gaza, a ranar 16 ga Oktoba, 2023

Man fetur da aka saba jigilar shi zuwa Gaza ta bututun mai a mashigar Kerem Shalom, da tallafin da Qatar ke bayarwa, yanzu ya daina aiki.

Wannan ya haifar da mummunan yanayi, saboda tashar wutar lantarki ta Gaza daya tilo, wadda ke buƙatar lita 600,000 na man fetur a kullum, ta kasance ba ta samun wannan albarkatu na man fetur.

Khaled Mohareb na hukumar samar da man fetur na Gaza ya kwatanta wannan da wani babban rikicin da ya haifar da cikas ga rayuwar yau da kullum.

Tun ma kafin wannan rugujewar, Gaza ta sha fama da matsalar karancin wutar lantarki, wanda ke haifar da katsewa.

Yawancin mazauna wurin sun dogara da janareta waɗanda ke buƙatar mai don aiki.

Asibitoci ma, sun dogara ne da injinan bayar da wuta, amma man da suke da shi yana raguwa.

Tashar wutar lantarki ita ce hanyar rayuwar Gaza, tana bayar da wutar lantarki ga gidaje da wurare masu mahimmanci kamar asibitoci da cibiyoyin kula da ruwa.

Man fetur yana da mahimmanci ga shuka, yana ba da damar samun ruwa mai tsabta ya kwarara zuwa cikin tafkunan mazauna Gaza.

Kafin wannan rikici dai ana ganin ruwan famfo a Gaza bai dace a sha ba, kuma Isra'ila ta rage yawan ruwan da take samu.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da shawarar amfani da aƙalla lita 100 na ruwa ga kowane mutum a kullum don sha da wanka da kuma dafa abinci.

Kafin rikicin, matsakaicin abin da ake amfani da shi a Gaza ya kai kusan lita 84, tare da lita 27 kawai wanda ya dace da amfanin ɗan adam.

A halin yanzu, WHO ta kiyasta cewa matsakaicin yawan ruwa ya kai lita uku kacal ga mutum.

Dr. Ghassan Abu-Sittah, wani likita daga Arewacin London da ke aiki a Gaza, ya bayyana saurin raguwar albarkatun mai, tare da rashin isasshen ruwa don sarrafa wasu kayan aikin likitoci.

Ya ƙara da cewa, hatta kayan yau da kullum kamar sinadarin 'vinegar' daga shagunan kayan amfanin gida ana amfani da su wajen maganin cututtukan kwayoyin cuta.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yaba wa shugabannin Amurka bisa ƙoƙarin diflomasiyya da suke yi na samar da abinci da ruwan sha da magunguna ga Gaza, yana mai cewa, rayuka da dama sun dogara da wannan taimako.