Malaman cocin da suka ce yaƙi ba zai sanya su guje wa Gaza ba

Nuns console bereaved Palestinians

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto, Lokacin da María del Perpetuo Socorro (hagu) da María del Pilar Llerena Vargas, waɗanda tagwaye ne, ke jajantawa waɗanda bama-baman Isra'ila suka shafa a harin da suka kai kan cocin Orthodox a ranar 19 ga watan Oktoba a Gaza
    • Marubuci, Alejandra Martins
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

María del Pilar da María del Perpetuo Vargas ƴan ƙasar Peru, masu wa’azi ne a wani coci da ke birnin Gaza, cocin Katolika tilo ɗaya a yankin Falasɗinawa.

Matan - waɗanda tagwaye ne - suna wa’azi a cocin, tare kuma da wasu mata daga wasu majami'u, inda suke ƙoƙarin taimaka wa mutane fiye da 600 a cocin Gaza, ciki har da naƙasassu yara, marasa lafiya da kuma tsofaffi waɗanda ake tura wa a kekuna.

Isra'ila ta kaddamar da harin bam a Gaza, sa'o'i bayan harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 1,400 tare da yin garkuwa da sama da 200,

Hakan ya yi sanadin mutuwar fararen hula fiye da 5,000, ciki har da yara sama da 2,000 a cewar ma'aikatar lafiya a Gaza da ke karkashin ƙungiyar Hamas.

The sisters María del Perpetuo Socorro (left) and María del Pilar Llerena Vargas

Asalin hoton, Familia Religiosa IVE

Bayanan hoto, Hoton malaman cocin biyu waɗanda ƴan uwan juna ne a coci Katolika ɗaya tilo a birnin Gaza

Shugaban sashin kula da ofishin jakadancin Peru a Masar, Giancarlo Pedraza Ruiz, ya tabbatar wa BBC cewa ofishin jakadancin Peru "ya yi ƙoƙarin kwashe 'yan ƙasar da 'yan uwansu na ƙasashen waje daga Gaza zuwa Masar".

Pedraza Ruiz ya yi nuni da cewa akwai jimillar mutane tara: 'yan ƙasar Peru huɗu, ciki har da wata yarinya 'yar shekara shida, da ƴan uwanta.

Sai dai duk dayaƙin da ake yi, malaman cocin mata biyu sun ɗage cewa ba za su bar Gaza ba.

Wannan shi ne abin da ’yar’uwa María del Pilar ta faɗa wa BBC.

Grey line
Bayanan hoto,
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

María del Pilar, kin bayyana cewa cocin ba shi da ruwa ko kuma wutar lantarki. Wane hali ake ciki yanzu?

Akwai mutum 400 a nan. Ba mu da ruwan sha kamar sauran garuruwa. Amma muna da wata rijiya da muke ɗebo ruwa, muna amfani da ruwan wajen zuwa bayan gida da kuma yin wanki da sauransu...ruwan zai iya karewa kowane lokaci. Mun kuma sayo ruwan roba domin mutane su sha. Kuɗin ya ninƙa sau uku.

Kin ce kin halarci jana'izar Kiristoci 18 waɗanda suka mutu lokacin da wani harin bam ya faɗa kan cocin Orthodox na St Porphyrius.

Isra'ila ta musanta cewa ta hari kan ginin cocin, kuma mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Lior Hayat ya faɗa BBC cewa abin da ya faru "hari ne na kuskure" bayan Isra'ilar ta kaddamar da hari kan gine-ginen hamas da ke kusa da cocin.

Za ki iya bayani kan abin da ya faru?

Mutanen sun mutu ne sakamakon bama-bamai da Isra'ila ta kai; ɗaya daga cikin ɗakunan da suka kwanta a ciki ya rufta. Sakamakon haka, ƴan uwana Kiristoci da dama sun mutu, ciki har da yaran da suka zo yin addu'a a cocin ko kuma suka halarci makarantar mu.

Na fita waje karon farko tun bayan soma yaƙin domin taimakawa iyalai Kiristoci a wurin bizina, da karfafa musu gwiwa, duk da cewa na san hakan yana da matukar wahala.

A ina aka binne waɗanda suka mutu?

Kowanne coci a nan yana da makabarta.

Kin ce kin ga hotunan abubuwan da ba za su taɓa gogewa a zuciyarki ba a wurin jana'izar.

Eh, haka ne.

Idan ka halarci wajen bizina za ka ji raɗaɗin da yaro yake ciki na yin bankwana da mahaifinsa.

Sannan, akwai raɗaɗin iyaye na rabuwa da ƴaƴansu wanda shi ne ya fi ciwo.

Akwai iyalan da - suka rasa ƴaƴansu gaba-ɗaya, da kuma ƴaran da suka rasa iyayensu baki-ɗaya. Abin takaici.

People inside the Holy Family Church in Gaza

Asalin hoton, Familia Religiosa IVE

Bayanan hoto, Ɗaruruwan mutane ne suka samu mafaka a cocin da ke Gaza

Kuna da abinci? Saboda motocin agaji kalilan ne aka bari suka shiga Gaza.

Mun gode Allah, akwai shugabannin coci da ke taimakon mu da kuma su kansu mutane.

Majami'ubn iyu, Latin da Orthodox, suna haɗin gwiwa sosai, kuma wannan babbar albarka ce daga Allah. Muna siyan abinci, muna siyan katifu. Yana da tsada sosai, amma alhamdulillahi muna da abinci.

Shin kuna zama da mutanen da suka nemi mafaka a cocin Orthodox kafin fashewar ranar 19 ga watan Oktoba?

Haka ne, wasu daga cikin mutanen sun yanke shawarar zuwa wurinmu saboda wani ɓangare na ginin ya rushe. Wasu daga cikinsu sun zo tare da mu.

The sisters María del Pilar (left) y María del Perpetuo Socorro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Malaman cocin mata a wani taron addu'a a cocin na Katolika da aka gudanar a watan Dismabar 2022

Ofishin jakadancin Peru a Masar ya tabbatar da cewa yana ɗaukar matakai domin barin ƴan ƙasar ta Peru da iyalansu ficewa. Kina da niyyar barin Gaza?

A'a. Sun kira mu daga ofishin jakadancin Peru a Isra'ila. Sai kuma daga ofishin jakadancin Peru a Masar, sun faɗa mana cewa suna da dukkan bayanan mu, sannan an shirya komai a kan iyaka da zarar mun shirya ficewa.

Sai dai babu wani lokaci da suka taɓa tambayar mu cewa me muke so mu yi.

Ba za mu iya barin mutanen mu ba. Na kasance ina rayuwa a nan tsawon shekara huɗu kuma nan ne rayuwata. Wannan ce majami'ata. Wannan ne mutane na kuma ba an bar nan ba. Suna buƙatar taimakon mu.

Kun san cewa tashin bama-bamai na ƙara sanya ku cikin barazana da kuma haɗarin mutuwa a kowace rana...

Eh, ina sane da haka domin ina jin tashin bama-bamai. Na yi imani cewa kowa a nan a cikin cocin ya san da haka.

Duk waɗannan Kiristocin sun samu damar zuwa kudanci, don ƙoƙarin ceton kansu, amma babu ɗayansu da ya so ya tafi. Kowa ya so ya zauna a cocin da yake. Watau, sun so su kasance kusa da cocin mai tsarki, kusa da Allah, kuma su zauna lafiya a nan.

Sister María del Pilar

Asalin hoton, Familia Religiosa IVE

Bayanan hoto, María del Pilar Llerena Vargas da ƴar uwarta sun fito ne daga birnin Arequipa na ƙasar Peru

Isra'ila ta gargaɗi mutane a arewacin Gaza cewa duk waɗanda ba su koma yankin Wadi Gaza ba suna cikin barazanar ayyana su a matsayin "masu taimakawa ƙungiyar ƴan ta'adda". Me ainihin abin da ke faruwa a can?

A cikin cocin akwai yara nakasassu.

Wasu mutane sun zo ne kan kekunan guragu, muna da tsofaffi kuma yawancinsu ba za su iya tafiya ba. Muna da mai fama da cutar kansa wanda aka yi wa tiyata a kwakwalwa.

Sannan akwai wasu da suka jikkata ƴan cocin Orthodox waɗanda ake yi wa magani a nan, saboda a cikin ƴan gudun hijirar muna da likitoci.

Ta yaya za ka ɗauki mutane 600, ciki har da yara, marasa lafiya, da tsofaffi? Ba za mu iya ba. Gaskiya hakan ba zai yiwu ba.

Kuma na yi imani cewa wannan dalili ne na jin kai da za su iya ganewa, cewa ba za mu iya motsawa daga inda muke ba.

The two nuns María del Pilar (left) and María del Perpetuo Socorro in Gaza

Asalin hoton, Familia Religiosa IVE

Bayanan hoto, Malaman cocin biyu María del Pilar (ɓangaren hagu) da María del Perpetuo Socorro na a Gaza tare da sauran malaman coci ƴan uwansu na majami'un Our Lady of Rosario da Sisters of Mother Teresa

Muna son zaman lafiya, zaman lafiya kaɗai muke so. Haka ne ma ya sa muke ta yin addu'o'i. Fafaroma ya kira taron addu'a na kwana ɗaya a ranar Juma'a (27 ga watan Oktoba). Na yi imanin cewa lokaci ne da dukkanmu za mu haɗa-kai domin addu'ar samun zaman lafiya.

Children and adults singing in front of a Christmas tree and church

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bikin Kirsimeti 2021: Yara Falasɗinawa ke rera wakoki a gaban cocin Holy Family a Gaza