Sabbin bayanan gaskiya guda 5 bayan mako huɗu na yaƙin Gaza

Gaza destruction

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Nan bayan wani hari ne a kan sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia a Gaza farkon wannan mako
    • Marubuci, Daga Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan BBC kan al'amuran duniya

Ɗaya daga cikin abubuwan farko da za a fahimta, game da ba da rahotanni da ƙalailaice bayanai da sharhin da aka yi ta kwararowa, tun bayan hare-haren Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba, shi ne babu wanda ke da cikakken labari.

Ba haka ba ma, kamar ko yaushe, da wuya a iya kutsawa cikin ƙurar yaƙi don aikin gano abin da ke faruwa a fagen daga.

Sabuwar siffar rikici tsakanin 'yan Isra'ila da Falasɗinawa, har yanzu ba ta bayyana ba tukun.

Har yanzu al'amura ba sa tafiya cikin sauri.

Tsoron cewa wannan yaƙi na iya fantsama, gaskiya ne matuƙa. Sabbin abubuwa na haƙiƙa da za su iya faruwa a Gabas ta Tsakiya na can a wani wuri, sai dai siffarsu da kuma sigar da za su ɓulla, sun dogara ne a kan hanyar da yaƙin ya gudana nan gaba cikin wannan shekara, da kuma mai yiwuwa bayan ta.

Nan, ga wasu abubuwa ƙalilan da muka sani, da kuma wasu 'yan ƙalilan ma da ba mu sani ba a game da yaƙin.

Lissafin dai ba shi da yawa. Wasu mutane sun riƙa yin shaƙiyanci ga Donald Rumsfeld, sakataren tsaron Amurka a lokacin mamayen ƙasar Iraƙi cikin 2003, lokacin da ya yi magana game da "abubuwan da kwata-kwata ba a san da su ba".

Amma a wannan sashe na duniya, kamar sauran, ba shakka akwai su - kuma idan suka bayyana, suna iya yi kawo gagarumin sauyi.

1.

Abu ɗaya da ya zama tabbas, shi ne goyon bayan da 'yan Isra'ila ke bai wa yaƙin da sojojin ƙasar ke yi don karya ƙashin bayan Hamas a Gaza, ita da ƙanwarta, Islamic JIhad.

Sun harzuƙa ne saboda hare-haren Hamas da suka gigita su, ta hanyar kashe fiye da mutum 1,400 da kuma ganin cewa har yanzu suna garkuwa da kimanin 240 a Gaza.

Kibbutz attacked by Hamas

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Harin da Hamas ta kai wa Isra'ila, ya halaka mutum 1,400, da yawa mazaunan yankunan kibbutz ne da ke daf da Gaza
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Na gamu da Noam Tibon, wani janar ɗin sojan Isra'ila da ya yi ritaya, don jin yadda ya tuƙa mota tare da matarsa zuwa Nahal Oz, wani yanki na kibbutz a kan iyaka da Gaza, bayan Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoba.

Niyyarsa wadda ya yi nasara kanta, ita ce ya kuɓutar da ɗansa da agolarsa da kuma 'ya'yansa 'yan mata biyu da ke cikin maɓoya, suna jin 'yan bindigar Hamas na kai-komo a waje.

Ko da yake, Tibon ya yi ritaya amma da ganin sa, har yanzu da sauran lafiyar jiki a shekararsa ta 62. Ya dai ɓuge da samun bindiga da hular kwanon da ya tsinta na wani sojan Isra'ila da ya rasu, inda ya jagoranci rukunin wasu sojoji da ya tattara daga hargitsin ranar, suka kakkaɓe maharan daga kibbutz tare da kuɓutar da iyalansa, har ma ƙarin wasu mutane da dama.

Janar ɗin, alewa ce irin ta da, hafsan sojin Isra'ila ne mai magana babu kwane-kwane.

"Gaza za ta ɗanɗana kuɗa… babu wata ƙasa da za ta yarda maƙwabciyarta ta zo ta hallaka jarirai da mata da kuma mutane. Kamar dai yadda ku ('yan Birtaniya) kuka murƙushe abokan gabanku lokacin Yaƙin Duniya na Biyu. Wannan muke buƙatar yi a Gaza. Ba imani."

Me? Na yi tambaya game da Falasɗinawa fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba, da ake kashewa?

"Abin takaici ne, hakan na faruwa. Muna rayuwa ne da wasu maƙwabta 'yan ta-kife, kuma muna buƙatar mu rayu… mu ma sai mun zama 'yan ta-kifen. Ba mu da zaɓi."

Ɗumbin 'yan Isra'ila ne ke jaddada irin wannan tunani nasa, cewa mace-macen Falasɗinawa fararen hula abin takaici ne, amma ana kashe su ne saboda abin da Hamas ta aikata.

2.

Kuma a bayyane take ƙarara cewa farmakin da Isra'ila ke kai wa kan Hamas, yana haddasa mugun zubar da jini. Alƙaluman baya-bayan nan na Falasɗinawan da suka mutu daga ma'aikatar lafiyan Gaza wadda Hamas ke tafiyarwa, sun zarce 9,000 - waɗanda kimanin kashi 65% ƙananan yara ne da mata.

Babu masaniya ƙarara nawa ne a cikin mazan da aka kashe suka kasance fararen hula, kuma nawa ne ke faɗa domin Hamas ko kuma ƙungiyar Islamic Jihad. Shugaba Joe Biden da 'yan Isra'ila ba su amince da alƙaluman ma'aikatar ba. Sai dai, a rikice-rikicen baya, ƙungiyoyin ƙasashen duniya na ɗaukan ƙiyasin mutanen da aka kashe daga Falasdinawa a matsayin na haƙiƙa.

Wani mugun abin tarihi yana tahowa cikin sauri. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fararen hula kimanin 9,700 aka kashe a Ukraine tun bayan fara cikakken mamayen Rasha wata 21 da ya wuce.

Wasu daga cikin Falasɗinawan da suka mutu na iya kasancewa 'yan Hamas ne. Amma ko da sun yawan kashi 10%, wanda ba lallai ne ba, hakan na nufin cewa Isra'ila ta kama hanyar kashe Falasɗinawa mafi yawa a tsawon wata ɗaya idan an kwatanta da yawan mutanen da Rasha ta kashe a Ukraine tun a watan Fabrairun 2022.

Gaza war victims

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna cewa hare-haren Isra'ila a kan Gaza na iya kasancewa laifukan yaƙi

Daga ranakun farko bayan hare-haren Hamas, Shugaba Biden ya goyi bayan shawarar Isra'ila ta amfani da ƙarfin soja don kawar da Hamas daga kan iko. Sai dai ya ƙara da sharaɗin cewa akwai buƙatar yin hakan "ta hanyar da ta dace". Yana nufin cewa ya kamata Isra'ila ta kiyaye dokokin yaƙi wajen kare fararen hula.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya sauka a Tel Aviv. Kafin ya tashi, ya ce: "Idan na ga yaro Bafalasɗine ko yarinya - an zaƙulo su daga cikin ɓaraguzan wani gini da ya ruguje, hakan na kaɗa har hantar cikin cikina kamar yadda idan na ga wani yaro daga Isra'ila da ko ma ina ne."

Na ɗauko rahotanni daga duk yaƙe-yaƙen Isra'ila a cikin shekara 30 da ta wuce.Ba zan iya tuna wani jami'in gwamnatin Amurka da ya bayyana haka a bainar jama'a ba cewa akwai buƙatar Isra'ila ta riƙa bin dokokin yaƙi. Ziyarar Blinken na nuna cewa ya yi imani Isra'ila ba ta ɗaukan shawarar Biden.

3.

Wani abu da kuma tabbas muka sani shi ne cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana cikin gagarumin matsin lamba.

Saɓanin manyan hafsoshin soji da na tsaron Isra'ila, bai ɗauki wani alhaki a kansa ba kan jerin manya-manyan gazawa da ta bar garuruwan kan iyakar Isra'ila kusan ba kariya ranar 7 ga watan Oktoba.

Ranar Lahadin da ta wuce, 29 ga watan Oktoba, ya janyo tada jijiyoyin wuya lokacin da ya wallafa wani saƙo a shafin X, yana ɗora laifi a kan hukumomin leƙen asiri. Netanyahu dai ya goge saƙon kuma ya nemi afuwa.

Ofishin kare 'yancin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ganin yadda aka kashe tare da jikkata fararen hula masu yawa a hare-haren Isra'ila ta sama, yana cike da tsananin damuwar cewa hare-haren sun wuce a kwatanta, kuma suna iya zama laifukan yaƙi.

Prime minister Netanyahu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Daga wasu ɓangarori, ana dora wa firaministan na Isra'ila alhaki kan abubuwan da suka faru ranar 7 ga watan Oktoba

'Yan Isra'ila uku, wani tsohon mai shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya da tsohon shugaban hukumar Shin Bet (hukumar tattara bayanan sirri ta cikin gidan Isra'ila) da kuma wani ɗan kasuwa a fannin fasahar sadarwa, sun rubuta wani sharhi a wata mujalla kan al'amuran hulɗa da ƙasashen waje suna cewa bai kamata Mista a ce Netanyahu ya sa hannu a yaƙin ba da kuma duk wani abu da zai zo daga baya.

Firaministan Isra'ilan yana da magoya baya 'yan alƙawari amma dai ya rasa ƙwarin gwiwar da wasu hamshaƙan jiga-jigai na rundunar soji da harkokin tsaron ƙasar ke da shi a kansa.

Noam Tibon, janar ɗin sojan da ya yi gumurzun fitar da kansa a kibbutz Nahal Oz don kuɓutar da iyalinsa, ya kwatanta Mista Netanyahu da Neville Chamberlain, firaministan Birtaniya wanda aka tilasta wa yin murabus a 1940, tare da maye gurbinsa da Winston Churchill.

Tibon ya faɗa min cewa: "Wannan ce kasawa mafi girma a tarihin ƙasar Isra'ila. Gazawa ce ta rundunar soji. Gazawa ce ta jami'an leƙen asiri. Kuma gazawa ce ta gwamnati… ta waɗanda ke kan mulki - kuma duk wani alhaki ya rataya ne a wuyansa - shi firaminista, Benjamin Netanyahu… Shi ne a kan mulkin da aka tafka gazawa mafi girma a tarihin Isra'ila."

4.

Abu ne kuma a fayyace ƙarara, cewa matakin da ake kansa na baya ya ruguje.

Wannan, abu ne maras daɗi kuma yana da hatsari, amma ga alama yana da wani yanayin nutsawa mai cike da turɓunewar da aka saba da shi.

Tun lokacin da aka kawo ƙarshen yamutsin Falasɗinawa na wajen 2005, an samu wata sara da ta ɓulla, cewa Mista Netanyahu ya yi imani za ta ɗore har illa masha Allah. Wannan wani magagi ne mai hatsari, ga duk Bafalasɗinen da ya damu, har ma da 'yan Isra'ilan.

Muhawarar da aka yi ta yi ita ce Falasɗinawa sun daina kasancewa barazana ga Isra'ila.

Maimakon haka, su, wata matsala ce da za a iya ciyo kanta. Dabarun da ake amfani da su, su ne tsumagiya da alewa, sai kuma hikimar mutanen da "raba kawuna don a yi mulki".

Benjamin Netanyahu wanda ya kasance firaminista a mafi yawan lokuta tun daga 2009 - da wani zangon farko-farko a 1996 da kuma 1999 - ya yi ta musu cewa Isra'ila ba ta da wata abokiyar ƙawancen zaman lafiya.

Mai yiwuwa a gaba za ta samu. Hukumar Falasɗinawa wadda ita ce babbar abokiyar hamayyar Hamas, ƙungiya ce mai matuƙar gazawa, kuma ɓangarori da dama da ke tallafa mata sun yi imani cewa, akwai buƙatar tsohon shugabanta Mahmoud Abbas ya sauka, ya koma gefe.

Amma dai ta yarda da hikimar kafa wata ƙasar Falasɗinawa a kusa da Isra'ila can baya a shekarun 1990.

Blinken and Mahmoud Abbas

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mista Netanyahu ya yi ƙoƙarin haddasa rashin jituwa tsakanin Hamas da Hukumar al'ummar Falasɗinawa a ƙarƙashin jagorancin Mahmoud Abbas (na dama a lokacin da yake gaisawa da Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken)

"Raba kawuna don a yi mulki" ga Mista Netanyahu na nufin a bar Hamas ta shimfiɗa mulkinta a Gaza, don yi wa Hukumar al'ummar Falasɗinawa illa.

Ko da yake firaministan na Isra'ila mafi daɗewa a kan mulki ko da yaushe yana hattara game da abin yake faɗa a bainar jama'a, amma ayyukansa tsawon shekaru sun nuna, ba ya son bai wa Falasɗinawa damar kafa wata 'yantacciyar ƙasa.

Matakin dai yana nufin sai ya sallama wani yanki na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ciki har da Gabashin Ƙudus, wanda 'yan Isra'ila masu tsattsauran ra'ayi suka yi imani cewa mallakar Yahudawa ce.

Lokaci zuwa lokaci, ana tsegunta furuce-furucen da Netanyahu ya yi.

A 2019, wasu majiyoyin Isra'ila sun ambato shi yana faɗa wa rukunin wasu 'ya'yan jam'iyyarsa ta Likud a majalisar dokokin ƙasar, cewa idan suka nuna adawa da kafa ƙasar Falasɗinu, to sai su goyi bayan shirye-shiryen tura kuɗaɗe - waɗanda akasari Qatar ke samarwa zuwa Gaza.

Ya faɗa musu cewa zurfafa ɓaraka tsakanin Hamas a Gaza da Hukumar al'ummar Falasɗinawa a Gaɓar Yamma, zai sa mafarkin kafa wata ƙasa, ya kasance ba abu ne mai yiwuwa ba.

5.

Kuma a bayyane take cewa Isra'ila, da goyon bayan Amurkawa, ba za ta lamunci wata yarjejeniya da za ta bai wa Hamas, damar ci gaba da mulki ba.

Hakan tamkar wani tabbaci ne na ɗumbin ƙarin zubar jini. Lamarin kuma ya bijiro da manyan tambayoyi game da to mene ne, da kuma wane ne zai maye gurbinsu, zuwa yanzu dai, ba za a iya amsawa ba.

Rikici tsakanin Larabawa da Yahudawa don ƙwace iko da yankin da ke tsakanin kogin Jordan da Bahar Rum, ya kwashe fiye da shekara 100.

Darasi ɗaya na wannan dogon tarihi mai cike da zub da jini ya koyar, shi ne ƙarfin soja, ba zai taɓa zama masalaha ba.

A shekarun 1990, an hau teburin tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya don kawo ƙarshen rikicin, ta hanyar kafa wata Falasdinawa da babban birninta a Gabashin Ƙudus a gefe ɗaya kuma ga Isra'ila.

Yunƙurin ƙarshe na farfaɗo da ita, bayan shekaru ana tattaunawar ta-ci-ba-ta-ci-ba, ya faru ne zamanin gwamnatin Obama. Ta dai gaza ita ma, shekara goma da ta wuce, kuma tun daga lokacin aka bar rikici yana ta ƙazancewa.

Obama and Abbas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yunƙurin ƙarshe na tattaunawar zaman lafiya shi ma ya gaza a lokacin mulkin Shugaban Amurka Barack Obama

Kamar yadda Shugaba Biden da sauran mutane da dama suka ce, damar da mai yiwuwa kawai ake da ita, ta kaucewa ƙarin yaƙe-yaƙe, ita ce ta kafa wata ƙasar Falasɗinawa, mai maƙwabtaka da Isra'ila.

Hakan kuwa ba mai yiwuwa ba ne da shugabannin da ke kan mulki a kowanne ɓangare.

Masu tsattsauran ra'ayi a duka Isra'ila da Falasɗin, za su yi duk yadda za su yi su ɓata wannan tunani, kamar yadda suka yi tun a shekarun 1990.

Wasu daga cikinsu sun yi imani suna bin maganar Allah ne, wanda ya sanya shi zama abu maras yiwuwa a shawo kansu su yarda su karɓi wani sassauci wanda babu ruwansa da wani addini.