Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?

Israel-Gaza war

Asalin hoton, getty images

Ƙungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai ta ƙaddamar da farmakin da ba a taɓa ganin irinsa ba, a kan Isra'ila ranar Asabar, inda ɗaruruwan 'yan bindiga suka kutsa cikin garuruwan da ke kusa da Zirin Gaza.

'Yan Isra'ila fiye da 1,000 ne aka ba da rahoton cewa an kashe, yayin da ake riƙe da gomman sojoji da fararen hula, ciki har da mata da ƙananan yara, a matsayin waɗanda ake garkuwa da su a Gaza.

An kuma kashe Falasɗinawa sama da 700 a ɗaruruwan hare-hare ta sama da sojojin Isra'ila suke kai wa, don mayar da martani a kan Gaza.

Haka kuma tana tattara dakarun sojinta a kan iyaka da Gaza, yayin da Falasɗinawa ke sauraron wani mamayen sojoji ta ƙasa.

Maganar shekara 100 da ta wuce

Israel-Gaza war

Asalin hoton, Getty images

Bayanan hoto, Baitu-laham a farkon ƙarni na 20

Birtaniya ta karɓi iko da yankin da aka sani da Falasɗin bayan an ci galaba kan masu mulkin wannan ɓangare na Gabas ta Tsakiya wato Daular Usmaniyya a Yaƙin Duniya na Ɗaya.

Yahudawa tsiraru da Larabawa masu rinjaye ne ke zaune a wannan ƙasa.

Zaman ɗar-ɗar ne tsakanin al'ummomin biyu ya ƙaru ne lokacin da al'ummar duniya ta bai wa Birtaniya aikin kafa wata "ƙasar zaunarwa" a Falasɗin ga al'ummar Yahudawa.

Ga Yahudawa ita ce ƙasar kaka da kakanninsu, amma Larabawan Falasɗin suna iƙirarin mallakar ƙasar kuma sun nuna adawa da matakin.

Israel-Gaza war

Asalin hoton, Getty images

Bayanan hoto, Wani Haganah mayaƙin (ƙarƙashin ƙasa na Yahudawa) kafin fara Yaƙin Ƙwatar 'Yancin kan Isra'ila a 1948

Tsakanin shekarun 1920 da 1940, yawan Yahudawan da ke zuwa can ya ƙaru, da yawansu suna tserewa musgunawa a Turai, inda suke neman wani wurin zama bayan kisan ƙare dangi na Holokos lokacin Yaƙin Duniya na Biyu.

Tarzoma tsakanin Yahudawa da Larabawa da kuma a kan mulkin Birtaniya ta ƙaru.

A 1947, Majalisar Ɗinkin Duniya ta kaɗa ƙuri'ar raba Falasɗinu zuwa ƙasar Yahudawa da ta Larabawa, inda Ƙudus zai kasance wani birni na al'ummar duniya.

Wannan shiri ya samu karɓuwa daga shugabannin Yahudawa amma ɓangaren Larabawa sai suka yi watsi da shi kuma bai taɓa tabbata ba.

Israel-Gaza war

Asalin hoton, Getty images

Bayanan hoto, Sojojin rundunar gamayyar ƙawancen Larabawa suna harbi kan mayaƙan Haganah, dakarun hukumar kare-kai ta Yahudawa a watan Maris ɗin i1948

Kafa ƙasar Isra'ila kuma masomin 'Bala'i'

A 1948, ganin sun kasa warware matsalar, masu mulki na Birtaniya sai suka fice, shugabannin Yahudawa kuma suka ayyana kafa Ƙasar Isra'ila.

Da yawan Falasɗinawa sun yi watsi da matakin daga nan sai yaƙi ya ɓarke. Dakaru daga ƙasashen Larabawa masu maƙwabtaka sai suka mamaye.

Dubun dubatar Falasɗinawa suka tsere ko kuma aka tursasa musu ficewa daga gidajensu a wani abu da suke kira Al Nakba, ko kuma "Bala'i".

Ya zuwa lokacin da faɗan ya ƙare, da wata yarjejeniyar tsagaita wuta a shekarar da ta biyo baya, Isra'ila na iko da mafi yawan yankin.

Jordan ta mamaye ƙasar da ta zamo wadda ake kira Gaɓar Yamma, Masar kuma tana mamaye da Gaza.

An raba Ƙudus gida biyu tsakanin dakarun Isra'ila a Yammacin birnin da kuma sojojin Jordan a Gabashi.

Da yake ba a taɓa cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya ba - ga kuma kowanne ɓangare na zargin ɗayan - an yi ta samun yaƙe-yaƙe da faɗace-faɗace a shekaru gommai da suka biyo baya.

Taswirar yankin a yau

Kan iyakokin Isra'ila a yau

y

A wani yaƙin cikin 1967, Isra'ila ta mamaye Gabashin Ƙudus da Gaɓar Yamma da kuma mafi akasarin Tuddan Golan na Siriya da kuma Gaza da yankin tekun Sinai.

Mafi yawan Falasɗinawa 'yan gudun hijira har zuwa 'ya'ya da jikokinsu na zaune a Gaza da Gaɓar Yamma, da kuma a Jordan mai maƙwabtaka da Siriya da Lebanon.

Isra'ila ba ta bari su ko 'ya'yansu sun koma gidajensu ba - Isra'ila ta ce hakan zai ba su damar cika ƙasar kuma su zamo barazana ga kasancewarta a matsayin ƙasar Yahudawa.

Israel-Gaza war

Asalin hoton, Getty images

Bayanan hoto, Kwamandojin sojin Isra'ila sun isa Gabashin Ƙudus lokacin Yaƙin Kwana Shida a 1967

Duk da haka Isra'ila ta ci gaba da mamaye Gaɓar Yamma, ko da yake ta fice daga Gaza a 2005, amma Majalisar Ɗinkin Duniya na yi wa yankin kallon wanda ke ƙarƙashin mamaya.

Isra'ila ta riƙa iƙirarin cewa duka Birnin Ƙudus ne babban birninta, yayin da Falasɗinawa ke yi wa Gabashin Ƙudus, kallon babban birnin ƙasar da za su samu.

Amurka ce, ƙasa guda ɗaya cikin jerin manyan ƙasashen duniya da ta amince da Ƙudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Cikin sama da shekara 50, Isra'ila ta yi ta gine-gine a Gaɓar Yamma da kuma Gabashin Ƙudus, inda yanzu sama da Yahudawa 600,000 ke rayuwa.

Waɗannan gine-gine sun ci karo da dokokin duniya, domin haka a matsayin haramtattu suke - wannan ita ce matsayar Majalisar Dinkin Duniya da Birtaniya da kuma sauran ƙasashe - amma Isra'ila ta yi watsi da hakan.

Israel-Gaza war

Asalin hoton, Getty images

Me ke faruwa yanzu?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hamas - wata ƙungiyar masu ikirarin jihadi da ke jagorantar ra'ayin rushe Isra'ila ce - ke iko da Gaza. Birtaniya da wasu ƙasashe masu ƙarfin faɗa-a-aji a duniya na kallonta a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda.

Hamas ce ta lashe zaɓen Falasɗinawa da aka yi a 2006, kuma suka karɓe iko da Gaza shekara guda bayan hamɓarar da gwamnatin abokan hamayya, Shugaba Mahmoud Abbas da ke jagoranci a Gaɓar Yamma.

Tun daga nan, Mayaƙan da ke Gaza suke ta fafata faɗa da Isra'ila, wadda suke tsaron iyaka Zirin Gaza tare da Masar domin mayar da Hamas saniyar ware, da kuma matsa mata lamba ta daina kai hare-hare, musamman harba makaman roka zuwa biranen Isra'ila.

Falasɗinawan da ke Gaza sun ce matsewa da kuma harin da Isra'ila ke kai wa ta sama a kan yankin da jama'a ke da yawa, wani hukunci ne a kan kowa da kowa.

Wannan shekarar ita ce mafi muni ga Falasɗinawan da ke Gaɓar Yamma da kuma Gabashin Ƙudus.

Sun kuma koka da cewa an taƙaita musu zirga-zirga, ga kuma fatattakar da sojoji ke yi musu, wadanda duka matakan ramuwa ne ga harin da ake kai wa Isra'ila.

Waɗanne ne manyan matsaloli?

Akwai wasu batutuwan da ba za a iya cimma matsaya kansu ba tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa.

Batutuwan su ne:

  • Me zai faru ga 'yan gudun hijrar Falasɗinawa
  • Me zai faru ga gine-ginen Yahudawa a Gaɓar Yamma da aka mamaye shin za su ci gaba da kasancewa ne ko kuma kawar da su za a yi.
  • Ko ɓangarorin biyu za su iya amincewa su riƙa amfani da Birnin ƙudus su biyu
  • Sai kuma abin da ya fi kowanne rikitarwa - ko za iya yiwuwa a kafa ƙasar Falasɗinawa tare da Isra'ila

Tun daga shekarun 1990, ake tattaunawa tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa amma aka gaza samun nasara, a ƙarshe tattaunawar ta watse a 2014.

Mece ce makomar wannan rikici?

A taƙaice, babu lokacin warwaruwa wannan rikici a nan kusa.

Masana sun yi gargaɗin lamari irin wannan zai iya faruwa matuƙar ba a iya shawo kan wannan lamari ba, amma an ta ƙoƙarin samun mafita kan lamarin ba a yi nasara ba.

Tattaunawa ta kusan nan da aka yi, an yi ta ne a lokacin Shugaban Amurka da ya gabata Donald Trump, wadda aka yi wa suna da "yarjejeniyar ƙarni" da shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu ya shirya.

Amma Falasɗinawa suka yi watsi da ita suna cewa wannan shiri ne na ɓangare guda.