Wa'adin Messi a Barcelona bai kare ba, Juventus za ta raba Liverpool da Firmino

Shugaban kungiyar Barcelona Juan Laporta ya ce wa'adin Messi a Barcelona ba ta kare ba, bayan da dan wasan mai shekara 35 dan Argentina ya kawo karshen zaman shekara 21 da yayi a Camp Nou inda ya koma Paris St-Germain a kakar wasa ta bara. (ESPN)

Barcelona ba ta amince da wani tayi daga kungiyoyi kan Frenkie de Jong, dan wasan tsakiya dan Netherlands mai shekara 25, sai dai Manchester United ta fi bayyana shawa'arta kan dan wasan. (ESPN)

Sai dai United ta mayar da hankalinta kan Sergej Milinkovic-Savic, dan wasan tsakiya mai shekara 27 a matsayin wanda zai maye gurbin de Jong. (Calciomercato - in Italian)

Liverpool na tunanin ko ta amince da tayin yuro miliyan 23 da Juventus ta yi ma ta kan Roberto Firmino, dan wasanta na gaba mai shekara 30. (Tuttomercato - in Italian)

Tottenham ta shirya sayar da Tanguy Ndombele dan wasan tsakiya mai shekara 25 idan ta sami wanda yayi tayi mai tsoka, inda Galatasaray ke kan gaba wajen masu sha'awar raba shi da Spurs. (Media Foot - in French)

Juventus ma ta bayyana cewa tana tunanin sayo Anthony Martial, dan wasan gaba na Manchester United mai shekara 26, sai dai Old Trafford ta ce tana bukatar ya ci gaba da taka ma ta leda. (Mirror)

Jules Kounde, dan wasan baya na Sevilla da Faransa mai shekara 23 ya fi so ya koma Barcelona. (Fabrizio Romano)

Chelsea na iya hana Barcelona sayen Cesar Azpilicueta, dan wasan baya mai shekara 32 idan kungiyar ta 'yan yankin Catalan ta sha gabanta wajen mallakar Kounde a Stamford Bridge. (Mail)