Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dani Alves ya koma Pumas UNAM ta Mexico
Dani Alves ya saka hannu kan kwantiragin komawa kungiyar kwallon kafa ta Mexico mai suna Pumas UNAM.
Dan kwallon Brazil mai tsaron baya, zai koma taka leda a babbar gasar Mexico, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Barcelona a karo na biyu da ya koma Camp Nou.
Mai shekara 39 ya sake zuwa Barcelona a karo na biyu a Nuwambar 2021, shekara biyar bayan da ya bar Camp Nou zuwa Juventus.
A watan jiya Alves ya tabbatar da cewar ba zai tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a kungiyar ta Sifaniya ba, wadda ya yi wa karawa 408.
Rabon da Pumas UNAM ta lashe kofin lik na Mexico tun 2011, wadda ta kammala kakar da ta wuce a mataki na 11 a kan teburi.
Alves, wanda ya yi kaka takwas a Barcelona ya lashe La Liga shida da Champions League uku.
Ya kuma buga wa tawagar Brazil wasa 125, wanda ke fatan zuwa gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a bana.