Masu bukata ta musamman za su yi azumi da addu'oi saboda matsalar tsaro a Najeriya

'Yan bindiga

A Najeriya, sakamakon yadda matsalar tsaro ta yi kamari, kuma ta ke ci gaba da tayar da hankalin jama'ar kasar, masu bukata ta musamman a kasar sun ware ranakun Litinin 1 ga watan Augusta da Talata 2 ga wata domin yin azumi da gudanar da addu’oi don samun saukin wannan lamari.

Masu bukatar sun ce yin hakan ya zama wajibi bisa la’akari da yadda kasar ke ciki na halin zaman dar-dar saboda hare-haren ‘yan bindiga.

Alhaji Garba Muhammad Nahuta, shi ne sakataren sarakunan makafin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa komawa ga Allah ne kadai mafita ga jama'ar Najeriya, don samun saukin matsalar tsaro da sauran matsalolin da ake fama da su a kasar.

Sakataren sarakunan makafin, ya ce su fa ‘yan bindigar nan ba nakasashshe suka sani ba, haka idan ma an tare mota a hanya basa tambayar akwai makaho ko gurgu ko kuma wani mai nakasa a ciki ba gaba daya kwasar mutane suke yi.

Don haka wannan matsala ta shafi kowa in ji shi.

Alhaji Garba, ya ce ”Idan gari ma ‘yan bindiga suka shiga ko suka kai hari, ba sa tantance makaho ko gurgu ko kuma kuturu, kowa abin ke shafa.”

Ya ce a don haka dole a tsaya ayi addu’a da azumi.

Ya ce sun fitar da sanarwa ce in da aka bukaci duk mai bukata ta musamman a kasar a kan su yi azumi da addu’a a wadannan ranaku da suka ware.

Alhaji Garba Muhammed, ya ce za su yi azumi da addu’ar ne don neman sauki ga kasa a kan irin halin da aka shiga game da tsaro.

Ya ce ana cikin babban tashin hankali kowa zuciyarsa ba dadi ba saboda tsoro da fargaba abin zai iya faruwa.

Matakin masu bukata ta musamman din na gudanar addu’oi da azumi don neman sauki ne a dai-dai lokacin da rundunonin sojin Najeriya suka sha alwashin fitowa da wasu sabbin dabarun magance matsalolin tsaron da ke addabar kasar nan da makonnin masu zuwa.

Lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar da har ta kai ƴan majalisar dattawa daga ɓangaren adawa kiran da a tsige shugaban kasar.

A baya-bayan nan dai ana samun karuwar kai hare-hare daga ‘yan bindiga abin da ta kai ga jama’ar kasar shiga cikin zulumi.