'Yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin ƙasa sun yi barazanar sace Buhari da El-Rufai

Asalin hoton, Other
‘Yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasar nan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris sun yi barazanar yin garkuwa da Shugaba Muhammadu Buhari.
Kazalika 'yan bindgar sun yi alwashin sace Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da sanatoci da sauran jami'an gwamnatin Najeriya.
Cikin wani bidiyo da suka fitar a ranar Asabar, mayaƙan da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun nuna yadda suke azabtar da fasinjojin da suka rage a hannunsu.
"Buhari da El-Rufai, insha Allahu sai mun kawo ku nan," a cewar wani mai magana daga cikin 'yan bindigar.
Gwamnatin Najeriya ko ta Jihar Kaduna ba su mayar da martani ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton. Amma an san yadda Gwamna El-Rufai ke nanata cewa "maganin 'yan fashin nan shi ne kawai a kashe su baki ɗayansu a lokaci guda".
Bidiyo mai tayar da hankali

Asalin hoton, Other
Bidiyon, wanda ya karade shafukan sada zumunta, ya nuna ‘yan bindigar suna lakada wa fasinjojin duka yayin da su kuma suke ta kuka da kururuwa.
A cikin bidiyon wanda ke da matukar tayar da hankali, an ji muryar wani yana bai wa wasu ‘yan bindigar umarni su daina dukan fasinjojin inda yake cewa “Ali, Abdullahi [ku dakata] dukan ya yi.”
Daga nan aka ga ɗaya daga cikin fasinjojin yana yin bayani kan yadda aka sace su da kuma bayyana cewa gwamnati ta gaza kubutar da su.
Ya yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya irin su Amurka da Ingila da Faransa su taimaka su ceto su, yana mai cewa “gwamnatin da ke da hakki ta karbo mu ta gaza”.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar da suka sace su ba su yi niyyar tsare su a hannunsu na lokaci mai tsawo ba.
Ita ma wata mata da aka hango cikin kaduwa ta bayyana gwamnatin tarayyar Najeriya a matsayin azzaluma bisa rashin kubutar da su “bayan mun zabe ka.”
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kazalika an nuno wani dan bindiga yana bayyana cewa gwamnati ce ta janwowa mutanen wulakanci sakamakon rashin yin abin da suka bukaci a yi musu.
Ya ce “mun sani cewa kokarinku shi ne ku karbe su da karfi…ku sani wannan kadan ne daga abin da za mu yi. Kamar yadda muka fada muku a baya idan har ba ku yi gaggawar aiwatar da abin da muke fada ba, nan wurin zai zama kwata.”
Dan bindigar ya sha alwashin sace manya-manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa, ciki har da sanatoci.
A watan jiya ne dai ‘yan bindigar suka sako karin wasu daga cikin fasinjojin jirgin kasan da suka sace a watan Maris bayan sun biya miliyoyin kudade, kamar yadda wasu bayanai suka nuna.
Bayanai sun nuna cewa har yanzu akwai fasinjoji 43 cikin wadanda aka sace.
Shi kuwa mutumin da yake shiga tsakani don ceto sauran fasinjojin, mawallafin jaridar Desert Herald, Malam Tukur Mamu, ya shaida wa BBC gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ce ta sa aka ki sako sauran fasinjojin.
A baya dai Shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar su yi abin da ya kamata domin ceto fasinjojin sai dai lamarin ya faskara.











