'Mawuyacin halin da muke ciki tun bayan sace 'yan uwanmu a jirgin kasan Abuja-Kaduna'

Jirgin kasa

Asalin hoton, NRC

'Yan uwa da makusantan fasinjojin da 'yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai a jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a makon jiya sun bayyana mawuyacin halin da suke ciki tun bayan sace 'yan uwan nasu.

A ranar Litinin din makon jiya ne maharan da hukumomi suka ce 'yan Boko Haram ne suka kai hari kan jirgin kasan lamarin da ya yi sanadin mutuwar fasinja takwas da jikkatar wasu da dama.

Makusanta da dangin fasinjojin na ci gaba da zaman zullumi, yayin da a karshen makon jiya hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta kasar ta tabbatar cewa fasinjoji fiye da 200 ne suka kuɓuta daga harin.

Wani dan uwan daya daga cikin fasinjojin wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya shaida wa BBC Hausa cewa "Ubangiji ne kawai yake rike da mu domin halin (da muke ciki) ba mai dadi ba ne, amma mun bar komai ga Allah."

Ya kara da cewa sun yi magana da 'yar uwarsa da aka sace kuma "ta shaida mana suna cikin koshin lafiya, ba a taba su ba, ba a yi musu wani abu ba, daga nan ba mu sake jin komai ba."

Sai dai ya kara da cewa har yanzu gwamnati ta ba ta tuntube su ba game da sace 'yan uwan nasu.

Amma a wata hira da manema labara, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai, ya ce mayakan Boko Haram ne suka sace fasinjojin yana mai cewa ba su tuntubi gwamnati game da bukatarsu ba.

A sanarwa ta baya bayan nan da hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya ta fitar, ta ce fasinja 362 ne a cikin jirgin da aka kai wa hari ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata.

"An tabbatar da cewa fasinjoji 186 da suka shiga jirgin suna cikin koshin lafiya a gidajensu. Sannan akwai karin mutum 14 da su ma yau aka tabbatar sun tsira. Wayoyin salula na mutum 51 da suka shiga jirgin suna kashe ko kuma ba a iya samun su bayan kiran da aka yi musu tun daga ranar Talata da safe," in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa fasinja 22 ne suka bata, kamar yadda 'yan uwansu suka bayyana wa hukumar.

Hukumar kula da sufurin jirgin kasan ta ce taragwan da suka lalace sakamakon harin, kawo yanzu an gyara wasu daga cikinsu tare da dora su a kan layin-dogon da aka gyara.

Sanarwar ta cce da hadin gwiwar jami'an tsaro, hukumar kula da sufurin jirgin kasan bisa umarnin shugaban kasa, na yin duk mai yiwuwa don tabbatar da ceto wadanda suka bata sakamakon harin.

Karin bayani

Harin da 'yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin din da ta wuce da daddare ya tayar da hankalin ƴan Najeriya tare da sanya fargaba a zuƙatan mutane da dama.

Wannan batu ya zama matsalar tsaro ta baya-bayan nan mafi muni da ta faru a Najeriya da kuma ta ɗimauta mutane.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama jigo mai sada miliyoyin mutane da arewacin ƙasar daga babban birnin tarayya Abuja da kuma kudanci.

Hakan ne ya sa mutane suka fi raja'a da bin jirgin ƙasan ganin yadda ya zama wata hanyar sufuri da mutane suke ganin ita ce mafi tsaro, fiye da bin hanyar mota, yayin da jirgin sama kuma ya yi tsadar da sai masu ido da kwalli ne za su iya biya.