Majalisa za ta binciki dalilin da jirgin ƙasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya a daji

Asalin hoton, NRC
Majalisar Wakilan Najeriya ta ce za a gudanar da bincike kan abin da ya haddasa tsayawar wani jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji a dokar daji.
A makon nan ne dai aka yi ta yaɗa hotuna a shafukan intanet da ke nuna wani jirgin ƙasa ya tsaya a kan hanyar Legas zuwa Ibadan, ga kuma fasinjoji sun yi cirko-cirko, ana ƙoƙarin zuba mai.
Hukumar kula da jiragen ƙasa dai ta ce mai ne ya ƙare wa jirgin, sai dai 'yan majalisar wakilai sun ce rashin iya aiki ne ya sa hakan ya faru tun farko.
Honarabul Abubakar Yunus wanda ɗan Majalisar Wakilan Najeriya ne ya bayyana wa BBC cewa sakamakon kuɗaɗen da aka kashe kuma har aka ciwo basukan maƙudan kuɗaɗe don ganin an inganta sufurin jiragen ƙasa, bai kamata a ce cikin shekaru ƙalilan an soma samun irin waɗannan matsaloli ba.
"Wannan wani abu ne da ba a saba gani ba, kuma tare da ganin cewa an ciwo basussukan maƙudan kuɗaɗe kuma aka ga an fara samun irin waɗannan matsaloli shi ne aka ce da walakin goro a miya.
"Gwara a yi bincike ganin cewa jirgi don me zai sa ya taso tun daga tasharshi, rashin mai ne ko dai ganganci ne har mai ya ƙare mashi bai kai inda zai je ya gama zirga-zirgarsa ba," in ji Honarabul Abubakar Yunus.
Ya bayyana cewa ana sa ran kwamitin da zai gudanar da bincike kan wannan lamari zai kammala binciken cikin mako biyu inda zai gabatar da rahoto.
Ya kuma yi ƙarin bayani kan zarge-zargen da aka daɗe ana yi wa ɓangaren sufurin jirgin ƙasa a Najeriya na ɓoye tikiti domin sayar da shi da tsada inda ya tabbatar da cewa ma'aikatan sufurin kan shiga intanet su saye tikitin sa'annan daga baya su rinƙa sayar wa jama'a da tsada.
Ya bayyana cewa suna sane da wannan matsala kuma za su yi ƙoƙarin yin garambawul domin shawo kanta.
Ko a kwanakin baya sai da aka kai wa jirgin ƙasan da ke jigila a hanyar Kaduna zuwa Abuja hari ta hanyar dasa wani abin da ake zargin na fashewa ne kan titin jirgin , wanda hakan ya sa layin dogon ya yanke.











