'Yan Bindiga sun kai hari a gidan yarin Kuje

Asalin hoton, AFP
Rahotannin daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kai hari a gidan yarin Kuje.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata da daddare, inda bayanai suka ce wasu daga cikin fursunonin sun tsere.
Wani mutum da BBC ta zanta da shi ya bayyana cewa maharan sun yi ta kabbara tare da harba rokoki a cikin gidan yarin.
A cewar wani da lamarin ya faru a gabansa, 'yan bindigar sun ci karfin jami'an tsaro inda aka yi ta musayar wuta.
"Maharan sun yi ta kabbara sai suka nufi inda ake tsare da 'yan Boko Haram, kafin su kubutar da fursunonin ciki," in ji mutumin.
Mai magana da yawun hukumar da ke kula da gidajen yari ta Najeriya CSC AD Umar, ya fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ya tabbatar da an kai harin da misalin karfe 10 na dare.
Ya kara da cewa "wasu 'yan bindigan da ba a tantance ko su wane ne ba sun kai hari kan gidan yarin Kuje da ke yankin babban birnin Najeriya."
Sanarwar ta kuma ce "jami'an hukumar tare da taimakon sauran jami'an tsaro sun mayar da martani kan maharan kuma an mayar da doka da oda a gidan yarin".
CSC Umar ya kara da cewa za a sanar da jama'a karin bayani da nan ba da jimawa ba.
Akwai fursunoni kusan 70,000 a gidajen yarin Najeriya, kimanin kashi 75 cikin 100 na zaman jiran shari'a ne a cewar hukumomi, yayin da cunkoso ya yi yawa matuka.
Wasu fursunonin kan kwashe shekara da shekaru ba su san matsayinsu ba, wasu ma kan shafe shekarun da suka zarta tanadin da doka ta yi na hukunci mafi tsanani na laifin da ake zarginsu da aikatawa.
Wasu daurarrun kan ma rasa rayukansu.











