Afcon 2023: Rukuni na huɗu da na biyar da na shida

Asalin hoton, Getty Images
Bayan da aka sauya lokacin Gasar Cin Kofin Afrika daga 2023 zuwa 2024, saboda lokacin damuna, Ivory Coast ta shirya gudanar da wasan daga Janairu zuwa Fabrairu.
Senegal na fatan kare kofin da ta lashe a Kamaru, kuma gasar ta tawaga 24 na nufin biyun da suka ja ragama za su kai zagayen gaba kai tsaye, yayin da hudun da suka hada maki da yawa za su hadu da su don buga quarter finals.
Jadawalin da aka fitar ya hada da Morocco 'yan sawun farko, wadda ta zama ta farko daga Afirka da ta kai daf da karshe a gasar kofin duniya a Qatar a 2022.
Mai rike da kofi, Algeria an yi waje da ita a zagayen cikin rukuni a Kamaru, yayin da Afirka ta Kudu da Tanzania da kuma Zambia za su koma buga gasar.
Sashen BBC na wasannin Afirka ya tattauna da 'yan wasa da 'yan jarida kan wasannin cikin rukuni na hudu da na biyar da kuma na shiga.
Rukunin D - Algeria da Burkina Faso da Mauritania da Angola
Algeria ta kasa kare kofinta a gasar Afirka a 2021, wadda ta kasa taka rawar gani a gasa biyu za ta fuskanci kalubale, in ji dan jarida, Maher Mezahi.
"Kungiyar ta The Fennecs ta je Kamaru da kyakkyawan fata a lokacin da ta yi wasa 36 a jere ba tare da an doke ta ba,'' kamar yadda ya fada.
''Sai dai su Riyadh Mahrez sun kasa ɗaga daragar tawagar, wadda aka yi ma ta fatan kare kofin Afirka.
''Duk da an fitar da tawagar, koci Djamel Belmadi ya ci gaba da amfani da tsoffin 'yan wasa a karawar neman shiga gasar kofin duniya a 2022. Hakan bai yi wa kasar dadi ba, wadda ta kasa samun tikitin shiga gasar kofin duniya da ta kayatar a 2022 a Qatar.''
Belmadi ya yanke shawarar ci gaba da jan ragamar Algeria, bayan watanni, wanda ke ta kokarin gina tawaga.
''Ya kwashe shekarar 2023 wajen tayar da sabbin jini don hada 'yan wasan da Algeria za ta iya gogayya da kowacce tawaga, amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.'' in ji Mezahi.
''Belmadi bai nuna fitattun 'yan wasa 11 da zai yi amfani da su. Ana ganin Algeria za ta yi abin kirki. Tawagar ta hada matasan 'yan kwallo, amma ba su da kwarewa.''
Cikin rukunin akwai Burkina Faso da ta kai daf da karshe a Kamaru har da Mauritania da Angola, wadanda za su koma buga wasannin a karon farko tun 2019.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dan jarida, Mark Gleeson ya hangi kwazo da tawagar za ta yi a Afcon, duk da cewar koci, Pedro Goncalves na fuskantar kalubale har da na rashin tsayayyun 'yan kwallon da yake fara wasa da su a fili.
''Goncalves zai gayyaci 'yan wasa da ke taka leda a gasar Portugal da Turkiya da wasu daga Faransa da Jamus. Haka kuma zai yi amfani da 'yan wasan da ke taka leda a gida a kungiyar Petro Atletico, kungiyar da ta buga sabuwar gasa ta African Football League," in ji Gleeson.
"Angola na fatan nasara a kan Mauritania da kuma Burkina Faso domin kai wa zagaye na biyu, amma ta kwana da sanin fafatawar da za ta yi da Algeria ba zai zo ma ta da sauki ba.''
Damar da take da shi shi ne rarrashin dan wasan Fiorentina, M'bala Nzola da tsohon wanda ya buga wa Portugal wasa, Ivan Cavaleiro da su buga ma ta wasannin.
''Rabon da Nzola ya buga wa kasar tamaula tun cikin watan Yuni, yayin da Cavaleiro, wanda ke taka leda a Lille ya koma buga wa Angola tamaula, duk da goron gayyata da aka yi ta mika masa tun cikin watan Satumba.'' in ji Gleeson.
Jadawalin rukuni na hudu
- Ranar Litinin, 15 ga watan Janairu: Algeria da Angola
- Ranar Talata 16 ga watan Janairu: Burkina Faso da Mauritania
- Ranar Asabar 20 ga watan Janairu: Algeria da Burkina Faso, Mauritania da Angola
- Ranar Talata 23 ga watan Janairu: Angola da Burkina Faso, Mauritania da Algeria
Rukunin E - Tunisia da Mali da Afirka ta Kudu da Namibia

Asalin hoton, Getty Images
Tunisia ce ta uku a jerin wadanda ke kan gaba a taka leda a Afirka, za kuma a dama da ita, duk da 'yan matsalolin da take fuskanta, in ji dan jarida Souhail Khmira.
"Tawagar The Carthage Eagles na fuskantar kalubale, bayan wani mawuyacin hali da ta tsinci kanta, bayan da aka tsare shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Wadie Jary a watan Oktoba, wanda ake zargi da cin hanci da rashawa.'' kamar yadda ya ce.
''Akwai wasu rahotannin da ke cewar mambobin hukumar kwallon kafar kasar za su yi murabus, sannan a dakatar da sabgogin tamaula.''
Tunisia ta fara wasannin neman shiga gasar kofin duniya da kafar dama, wadda ke fatan taka rawar gani don kara lashe kofin Afirka da ta dauka tun 2004.
Mali ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya da aka yi a Qatar, bayan da Tunisia ta taka mata gurbi.
Namibia da Afirka ta Kudu, wadda ta dauki Afcon a 1996 za su buga wasannin bayan da ba su je gasar da aka yi a 2021 ba a Kamaru.
''Bayan da ta kasa shiga gasa hudu daga bakwai baya, idan har Bafana-Bafana ta kai zagaye na biyu a Ivory Coast to ta samu ci gaba sosai.'' in ji dan jarida Mo Allie
"Hugo Broos ya tuna gasar kofin Afirka na karshe da ya horar da tamaula a lokacin da Kamaru ta dauki kofin a 2017. Mai shekara 71 ya kara bunkasa tawagar tun bayan da ya karbi aikin a Mayun 2021.
''Nasarar doke Morocco a gida a watan Yuni da canjaras da Ivory Coast a Oktoba ya nuna cewar lallai Broos zai taka rawar gani da ake bukata.
''Sai dai rashin nasara da Afirka ta Kudu ta yi 2-0 a hannun Rwanda a wasannin neman shiga gasar kofin duniya a cikin Nuwamba ya kara sa wasu na shakkun kwazon da tawagar za ta yi.''
Jadawalin rukuni na biyar
- Ranar Talata 16 ga watan Janairu: Tunisia da Namibia, Mali da Afirka ta Kudu
- Ranar Asabar 20 ga watan Janairu: Tunisia da Mali
- Ranar Lahadi 21 ga watan Janairu: Afirka ta Kudu da Namibia
- Ranar Laraba 24 ga watan Janairu: Afirka ta Kudu da Tunisia, Namibia da Mali
Group F - Morocco da DR Congo da Zambia da Tanzania

Asalin hoton, Getty Images
Morocco tana cikin wadanda ake tsoro a hadu da ita, bayan da ta taka rawar gani a Qatar a 2022 da yadda matasanta suka taka rawar gani da kwazon da tawagar Matan kasar suka yi a gasar kofin duniya ta mata - wannan ne karni mafi kyau a tamaular Morocco in ji dan jarida, Amine El Amri.
''Tawagar The Atlas Lions tana cikin wadanda ake sa ran lashe kofin Afirka a 2024, amma kai wa daf da karshe da ta yi a Qatar a 2022, zai sa ta kara fuskantar kalubale,'' in ji El Amri.
''Wani kalubalen da tawagar za ta fuskanta shi ne yanayin Ivory Coast, mai zafi - musammam ga wasu 'yan wasa da suka dade a Turai suna taka leda.''
An kusa shekara 50 rabon da Morocco ta dauki kofin Afirka tun bayan 1976 a Habasha.
''Burin tawagar Morocco shi ne lashe kofin, wanda kusan shekara 50 rabon ta da shi.
''Da yawa 'yan Morocco ba su san lokacin da kasar ta dauki Afcon a 1976 ba.
Gasar da Ivory Coast za ta shirya dama ce ga Morocco ta faranta ran kasar wajen lashe kofin, wani fanni da 'yan kasar za su yi murna kamar yadda suka yi a Qatar a 2022.''
Jamhuriyar Congo, wadda ta dauki Afcon a 1968 da kuma 1974 da Tanzania, wadda karo na uku za ta shiga wasannin, ba su buga wasannin da aka yi a 2021 ba har da Zambia.
Tawagar The Chipolopolo ba ta samu halartar gasar kofin Afirka uku ba, Patson Daka ya ce ''Mafarkinmu ne ya zama gaskiya da za mu koma buga wasannin,'' wadda ta lashe kofin a 2021.
''Nasara ce mai girma a ce kana cikin 'yan wasan Zambia da za su kara a wasannin da za a yi a 2024,'' kamar yadda dan kwallon mai shekara 25 ya bayyana.
Mai taka leda a Leicester City, bai damu da wasan hamayya da za su kara da Morocco ba, bayan da za su fafata a cikin rukuni a wasannin neman shiga gasar kofin duniya.
'Mun saba da fuskantar kowanne irin kalubale.'' kamar yadda Daka ya ce.
Rukunin F
- Ranar Laraba 17 ga watan Janairu: Morocco da Tanzania, Jamhuriyar Congo da Zambia
- Ranar Lahadi 21 ga watan Janairu: Morocco da Jamhuriyar Congo, Zambia da Tanzania
- Ranar Laraba 24 ga watan Janairu: Tanzania da Jamhuriyar Congo, Zambia da Morocco














