Bitar rukunin farko zuwa na hudu a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023

Mohamed Salah, Sadio Mane and Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohamed Salah ya yi rashin nasara a wasannin ƙarshe biyu na Afcon - ciki har da wanda ya kara da Mane na Senegal a 2021 - yayin da Najeriya ke fatan Victor Osimhen zai taimaka mata wajen lashe kofin

Za a fara gasar Kofin Ƙasashen Afirka (Afcon) a Ivory Coast a tsakiyar watan Janairu bayan an matsar da ita saboda kada ta shiga lokacin damina a Afirka ta Yamma.

Yayin da Senegal ke shirin kare kambinta, gasar mai tawaga 24 na nufin tawaga biyu da ke kan gaba a kowane rukuni ne za su tsallaka zagaye na biyu, inda kuma tawaga huɗu waɗanda suka fi ƙoƙari amma suka maƙale a mataki na uku za su bi sawunsu.

An samu abin mamaki a gasar da ta gabata a Kamaru, inda ƙasashen Comoros da Gambiya suka wuce zagaye na gaba yayin da Ghana mai kofin har huɗu ta koma gida da wuri.

Amma me za mu tsammata a gasar ta bana karo na 34?

Sashen wasanni na BBC ya tattauna da 'yan wasa, da masana ƙwallon Afirka, da 'yan jarida don tsefe rukunan A, da B, da C.

Rukunin A - Ivory Coast da Najeriya da Equatorial Guinea da kuma Guinea-Bissau

An haɗa masu masaukin baƙin da Najeriya, wadda ta ɗauki kofin sau uku, da Equatorial Guinea, wadda ta ba da mamaki na zuwa zagayen 'yan 16 a gasar da ta gabata.

Guinea-Bissau, wadda ke neman wuce matakin rukuni a karon farko, za ta gamu da ƙungiyoyin da tsohon ɗan ƙwallon Ivory Coast, Didier Drogba, ke ganin zai yi mata "tsauri sosai".

''Dukkan tawagogin nan sun cancanci shiga gasar, kuma za su yi kokarin taka rawar gani - in ji wanda ya ci wa Ivory Coast kwallo 65.

''Najeriya da Victor Osimhen da sauran 'yan wasan da take da su fitattu a duniya, za ta taka rawar gani, za ta yi kokarin ganin ta lashe kofin nan.''

Super Eagles na fuskantar caccaka daga magoya bayan kasar bayan canjaras biyu da ta buga da Lesotho da Zimbabwe a wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 a cikin watan Nuwamba.

Frank Onyeka ya ce yana da wuya magoya baya su mara wa Super Eagles baya.

''Na san cewa sun fusata, amma muna bukatarsu,'' kamar yadda mai shekara 25 ɗin ya bayyana.

''Mun kwana da sanin kwazon da ake bukata wajen lashe kofin Afirka. Canjaras biyun da muka yi wani mataki ne na daukar darasi.''

Super Eagles ta fice daga gasar a zagayen 'yan 16 a Kamaru, kuma Onyeka na sa ran Najeriya za ta wuce zagayen cikin rukuni.

''Ba abu ne mai sauki ba karawa tsakanin kungiyoyin Afirka, dole sai ka shirya sosai.''

Jadawalin wasannin rukunin farko

  • Asabar, 13 ga watan Janairu: Ivory Coast da Guinea-Bissau
  • Lahadi, 14 ga watan Janairu: Nigeria da Equatorial Guinea
  • Alhamis, 18 ga watan Janairu: Ivory Coast da Nigeria, Equatorial Guinea da Guinea-Bissau
  • Litinin, 22 January: Equatorial Guinea da Ivory Coast, Guinea-Bissau da Nigeria

Rukuni na biyu - Masar da Ghana da Cape Verde da kuma Mozambique

Mohammed Kudus celebrates scoring for Ghana against South Korea at the 2022 World Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohammed Kudus ya ci wa Ghana kwallo biyu a gasar Kofin Duniya a Qatar, yana kuma taka rawar gani a West Ham tun bayan da ya koma Premier League
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana sa ran Masar za ta taka rawar gani a gasar 2024, bayan da ta yi rashin nasara a wasan karshe karo biyu, bayan da Kamaru ta doke ta a 2017 da wanda Senegal ta lashe kofin a 2021.

'Yar jaridar Masar Inas Mazahar ya ce hakika a koda yaushe ana sa ran kasarza ta yi abin kikrki a wasannin.

''Mozambique za ta yi kokarin fitar da kanta kunya a wasan farko a rukuni da Masar, amma wasa na biyu da Masar za ta buga da Ghana zai yi zafi domin a lokaci kowacce tawaga na lissafin yadda za ta kai zagayen gaba.''

''Wasa na gaba da Cape Verde zai bai wa Masar damar jan ragamar rukunin - idan kuma ta kai quarter finals daga wajen za ta hadu da fitattun kasashe.

''Koci, Rui Vitoria bai fuskanci kalubale mai girma ba tun bayan da ya karbi aiki a Yulin 2022, kalubalen da tawagar Masara za ta fuskanta kenan.

''Dan kasar Portugal zai fuskanci kalu bale daga magoya da masu sharhin wasannin, wadanda ba za su amince da wani korafi ba, idan ya kasa kai wa wasan karshe.''

Ana kuma sa ran Ghana za ta yi abin kirki a Ivory Coast - mai gabatar da shirye- shirye a BBC Sports, GeorgeAdo Jr ya ce ''Magoya baya sun damu kan irin rawar da Black Stars ke takawa, wadda ba ta kai zagayen quarter finals ba a gasar kofin Afirka tun daga 2017.

''An fitar da Ghana a zagayen 'yan 16 a 2019, ta kuma kasa cin wasa da rashin kai wa zagaye na biyu daga fafatawar cikin rrukuni a gasar da aka yi a Kamaru,'' kamar yadda ya kara cewa.

''Black Stars na kasa sa kwazo a zangon farko a kowanne wasa karkashin Chris Hughton kawo yanzu - wasa daya ne daga tarada ta yi ta zura kwallo a mintin 45 din farko.''

''Sai a mintin karshe ta doke Madagascar a wasan neman neman shiga gasar kofin duniya, sannan ta kasa nasara a Comoros, Addo Jr ya ce ba wani babban buri daga tawagar Ghana.''

''Duk ana damuwa kan wasan da za ta fuskanci Cape Verde da Mozambique duk don rashin kaka rawar gani a wasanninta.'' kamar yadda ya fada.

''Nasara ce mai girma idan ta kai quarter finals. Ya kamata Hughton ya samu fitattun 'yan wasa 11 da zai ke amfani da su a kowanne wasa.

''Ya kamata Black Stars ta tabbatar fitattun 'yan wasanta na kan ganiya, idan har tana fatan taka rawar gani a Ivory Coast a 2024.

Jadawalin rukuni na biyu

  • Lahadi, 14 ga watan Janairu: Masar da Mozambique, Ghana da Cape Verde
  • Alhamis, 18 ga watan Janairu: Masar da Ghana
  • Juma'a, 19 ga watan Janairu: Cape Verde da Mozambique
  • Litinin, 22 ga watan Janairu: Mozambique da Ghana, Cape Verde da Masar

Rukuni na uku - Senegal da Kamaru da Guinea da kuma The Gambia

Sadio Mane reacts after winning the Africa Cup of Nations with Senegal in Cameroon in February 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sadio Mane ya lashe kofin Afirka a Fabrairun 2022, amma yanzu mai shekara 31 yana taka leda a gasar Saudi Arabia

Kamaru da ta lashe kofin nahiyar Afirka biyar jimilla ta kare a mataki na uku a gasar da ta dauki nauyi a 2020.

Duk da canjaras da ta yi da Senegal, magoya bayan Indomitable Lions ba za su ji dadi ba idan kasar ba ta lashe kofin da za a buga a Ivory Coast ba.

Lawrence Nkede dan Kamaru mai sharhin kwallon kafa ya ce: ''Muna son su kawo mana kofin gida, saboda a Abidjan muka fara lashe kofin farko a 1984."

Yadda Andre Onana ke kasa taka rawar gani a Manchester United da rashin tabbas din Bryan Mbeumo, tuni Kamaru ta fara tunkarar kalubale kafin wasan da za ta kara da Guinea.

Tawagar Syli Nationale ta Gambia ta kai zagaye na biyu a gasa uku baya, yayin da za ta koma buga karawa bayan da ta kai kwata fayinal a gasar farko da ta fara zuwa a Afcon.

''Ya kamata The Scorpions ta zama tana kan ganiya domin kai wa zagayen gaba, bayan da ta kasa taka rawar gani a wasa biyu na neman shiga gasar kofin duniya," in ji dan jarida Momoudou Bah.

"Koci Tom Saintfiet zai fuskanci Senegal a karawar hamayya a wasan farko a cikin rukuni, karon farko da tawagogin biyu za su fafata tun bayan shekara 15 a irin wannan matakin.''

Kwallon kafar Gambiya na kara samun cigaba, inda matasanta 'yan shekara 20 suka shiga gasar Kofin Duniya karon farko cikin shekara 16, amma koci, Saintfiet na fuskantar kalubale kan salon horar da tamaularsa.''

Jadawalin rukuni na uku

  • Litinin, 15 ga watan Janairu: Senegal da The Gambia, Cameroon da Guinea
  • Juma'a, 19 ga watan Janairu: Senegal da Kamaru, Guinea da The Gambia
  • Talata, 23 ga watan Janairu: Guinea da Senegal, The Gambia da Kamaru