Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hukunci 10 da kotu ta yanke kan zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kano
A ranar Talatar nan ne wata babbar Kotun tarayya a kano ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Simon Amobeda ta rushe shugabancin hukumar zaɓe ta jahar Kano bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar mata na rashin cancantar shugabannin hukumar bisa kasancewarsu ƴan siyasa masu ɗauke da katin Jam'iyyar NNPP.
Wani ɗan jam'iyyar APC Hon Aminu Tiga da Jam iyyarsa ta APC ne dai suka shigar da ƙara inda suka roƙi kotun da ta rushe shugabannin hukumar zaɓen ta Kano bisa kasancewrsu ƴan jam'iyya mai mulki.
Ga dai hukunce-hukuncen da kotun ta yanke:
Hukunci 10 da kotu ta yi kan zaɓen
- Shugabannin hukumar zaɓen jihar Kano ba su cancanci jagorancin hukumar ba kasancewarsu masu ɗauke da katin jam'iyyar NNPP wanda ya ci karo da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a 1999.
- Shugaban hukumar zaɓen na Kano, Farfesa Sani Lawal Malumfashi bai cancanci naɗin da aka yi masa ba saboda ba ma'aikacin gwamnatin jihar Kano ba ne wanda ke ƙasa da muƙamin mataimakin darekta kamar yadda dokar hukumar zaɓen ta Kano ta 2001 ta tanada.
- Gamayyar shugabannin hukumar zaɓen ta Kano ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka yi wa kwaskwarima a 1999 da tanade-tanaden da suka kafa hukumar zaɓen ta Kano na 2001, saboda haka ba za su iya gudanar da zaɓe a kananan hukumomin jihar 44 ba har sai an naɗa waɗanda suka cancanta tukunna.
- Duk wasu shirye-shirye da hukumar zaɓen ta yi a baya ko kuma take yi ko shirin yi a nan gaba dangane da zaɓen ƙananan hukumomi na jihar na 2024 da suka haɗa da fitar da ƙa'idojin zaɓe, tantance ƴantakara, sayar da fom ɗin shiga takara duka haramtattu ne.
- Daga yanzu an rushe kuma an kori waɗanda ake ƙara daga muƙamansu na shugabancin hukumar zaɓen da mambobinta.
- An hana hukumar zaɓen ta Kano gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na 2024 har sai an naɗa waɗanda suka cancanta.
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC ka da ta bai wa hukumar zaɓen ta Kano kayan zaɓe dangane da zaɓen ƙananan hukumomi na 2024 da suka haɗa da jerin sunayen masu zaɓe, har sai an naɗa waɗanda suka cancanci jan ragamar hukumar.
- Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta, INEC ta yi maza ta karɓe duk wasu kayan da ta bai wa hukumar zaɓen Kano idan har ma ta yi hakan, har sai an samu shugabannin da suka cancanta a hukumar zaɓen ta Kano.
- Ka da hukumar DSS ta Kano da rundunar tsaro ta NSCDC su shiga harkar zaɓen na 2024 a ƙananan hukumomi 44 na Kano har sai lokacin da aka naɗa mutanen da suka cancanta kamar yadda doka ta tanada.
- Waɗanda ake ƙara na biyu (Majalisar Dokokin Kano) da na uku (Kwamishinan Shari'a na Kano) su tabbatar da cewa an bi ƙa'ida wajen naɗa mutanen da suka cancanta domin shugabancin hukumar zaɓen ta Kano kamar yadda kundin tsarin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a 1999 da tanade-tanaden da suka kafa hukumar zaɓen ta Kano na 2001.
Jerin waɗanda aka yi ƙara
- Hukumar Zaɓen jihar Kano mai zaman kanta (KANSIEC)
- Majalisar Dokokin jihar Kano
- Kwamishinan shari'a na jihar Kano
- Hukumar Zaɓen Najeriya mai zaman kanta (INEC)
- Darektan hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS, reshen jihar Kano
- Kwamishinan ƴansanda na jihar Kano
- Waɗanda suke ƙara
- Kwamandan rundunar tsaro ta NCSDC
- Anas Muhammad Mustapha
- Farfesa Sani Lawal Malumfashi
- Mukhtar Garba Dandago
- Isyaku Ibrahim Kunya
- Shehu Na Allah Kura
- Kabir Jibril Zakirai
- Amina Inuwa Fagge
Martanin waɗanda ake ƙara
Ɗaya daga cikin lauyoyin waɗanda ake ƙara, barista Ibrahim Isa Wangida wanda ke kare majalisar dokokin jihar Kano ya ce "wannan ba shi ne hukunci na ƙarshe ba."
"Mun zauna da waɗanda suka ɗauke mu aiki kuma mun ba su shawarwari. Yanzu muna jiran umarninsu dangane da mataki na gaba. Ba wannan ne hukuncin ƙarshe ba.
Akwai damar ɗaukaka ƙara. Kuma da zarar an samu wani hukunci a kotun gaba da za ta iya jingine wannan hukuncin ka ga ita hukumar zaɓe ta Kano, KANSIECza ta iya ci gaba da aikinta." In ji barista Wangida.