Ƙasashen Afirka huɗu da Amurka ke da sansanin soji a cikinsu

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi bazaranar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, ƴan ƙasar ke ci gaba da fargabar irin matakin da shugaban na Amurka zai ɗauka.
Shugaba Trump ya ce zai ɗauki matakin ne idan har hukumomin Najeriya suka kasa ɗaukar matakan dakatar da abin da ya kira ''kisan kiristoci'' a ƙasar.
Sai dai wasu na ganin matakin da Amurkan ke shirin ɗauka ba alkairi ba ne ga Najeriya - wadda ta fi kowace kasa yawan al'umma a Afirka.
Idan aka zo ga batun daukan matakin soji, matakin na Amurka - wadda ta fi kowace kasa ƙarfin soji a duniya - ka iya zuwa a sigogi biyu, a cewar masana.
Na farko ta kai farmakin soji da nufin kakkaɓe ƙungiyoyin da ake zargin da aikata kashe-kashe domin gamawa da su a lokaci guda.
Ko kuma ta kafa sansanonin soji a cikin ƙasar da nufin ɗaukar lokaci tana bincike tare da gano maɓoyar ƴanbidigar da ƙaddamar da hare-hare a kansu, kamar yadda take yi a ƙasashen da take da sansanoni.
Akwai ƙasashen Afirka aƙalla huɗu da Amurka ke da sansanonin soji a cikinsu, inda take amfani da su wajen bayar da horo ga jami'ai da tattara bayanan sirri da kuma yaƙar ta'addanci a nahiyar.
Cikin wannan maƙala mun duba ƙasashen Afirka huɗu da Amurka ke da sansanonin soji a cikin ƙasashen.

Asalin hoton, Getty Images
Djibouti

Asalin hoton, Getty Images
Djibouti ta kasance ƙasa mai muhimmanci ga Amurka a nahiyar Afirka.
Ƙasar - wadda ke gabashin Afirka - ta ƙasance ƙasar da babban sansanin sojin Amurka yake a Afirka.
Tun da farko Faransa ce ta gina sansanin mai suna 'Camp Lemonnier' da nufin bai wa wasu Faransawa mazauna ƙasar kariya.
Sai dai daga baya an miƙa shi ga hukumomin ƙasar bayan dakarun Faransan sun kammala aiki, inda ita kuma ta miƙa shi ga Amurka a shekarar 2002.
A watan Mayun 2014, tsohon shugaban Amurka, Barrack Obama da shugaban Djibouti, Ismaïl Omar Guelleh suka ƙulla wata yarjejeniyar da ta sahhale wa Amurka ci gaba da amfani da sansanin a matsayin haya har na tsawon shekara 20.
Amurkar na biyan hayar dala miliyan 63 kan sansanin a kowace shekara.
Sojojin Amurka na amfani da sansanin a matsayin cibiyar yaƙi da ta'addanci a Afirka. Alƙaluma sun nuna cewa Amurka na da sojoji kimanin 4,000 a Djibouti.
Kenya

Asalin hoton, Getty Images
Dakarun Amurka na amfani da sansanin Manda Bay, da ke wurin shaƙatawa a matsayin sansaninsu a ƙasar Kenya.
A shekarar 2006 ne wannan sansani ya zama sansanin sojin sama, inda aka ƙara masa jami'ai da jiragen yaƙi.
A cewar Amurka, an kafa wannan sansani ne domin horar da jami'an tsaron Afirka, domin yaƙar masu tayar da rikici tare da kare muradun Amurka.
Sai dai a ranar 5 ga watan Janairun 2020, mayaƙan ƙungiyar al-Shabab kusan 30 zuwa 40 suka ƙaddmar da hari kan wannan sansani, lamarin da ya haifar da mutuwar jami'an Amurkan uku, da raunata wasu da kuma lalata jiragen yaƙi shida.
Masar

Asalin hoton, Getty Images
Sansani ne na ƙawancen dakarun ƙasashen duniya, ƙarƙashin jagorancin Amurka, da aka samar a yankin Sinai da nufin wanzar da zaman lafiya a ƙasar.
An samar da sansanin ne da nufin tabbatar da wanzar da yarjejeniyar kyautata alaƙa tsakanin Isra'ila da Masar.
Haka kuma sojojin Amurka na jagorantar wata cibiyar binciken lafiya ta sojojin ruwa da aka fi sani da Namru a birnin Alkahira.
Ana amfani da cibiyar wajen binciken cutuka masu yaɗuwa da nufin gano matakan kariya daga gare su.
Kamaru

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta samar da wani sansanin sojinta a birnin Garoua da ke arewacin Kamaru da nufin tallafa wa Afirka wajen yaƙi da maƙiya.
Tun da farko Amurka ta aika dakarun ne da nufin tallafa wa sojojin kamaru wajen yaƙar masu tsattsauran ra'ayi.
Ƙasar Kamaru - da ke iyaka da Najeriya - na cikin ƙasashen da ke fama da matsalar Boko Haram, da ta addabi ƙasashen yankin tafkin Chadi.











