'Ina kallo ambaliyar ruwa ta wuce da iyalina amma na kasa yin komai'

Adamu Yusuf tsaye cikin tarkace

Asalin hoton, Gift Ufuoma

Bayanan hoto, Yusuf ya rasa matarsa da jaririnsa a ambaliyar ruwa da ta mamaye garinsu.
    • Marubuci, Azeezat Olaoluwa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Mokwa Town
  • Lokacin karatu: Minti 6

Rayuwar Adamu Yusuf ta canza gaba ɗaya tun bayan da ambaliyar ruwa ta hallaka 'yan uwansa tara a Tiffin Maza, ɗaya daga cikin ƙauyuka biyu a garinsu da ambaliyar ta fi shafa a arewa maso tsakiyar Najeriya.

Adamu, wanda yake da shekara 36 kuma da ɗa ɗaya, ya ce matarsa da jaririnta na daga cikin wadanda ruwa ya ɗauka a ambaliyar da ta faru da sassafe ranar Alhamis a jihar Neja.

"Ita ce ta fara tashi na ta ankarar da ni game da ambaliyar, nan da nan na tattara iyalina na ce mu riƙe juna. Yayin da muka fito, sai muka ga ruwa cike a ko'ina, nan fa sai suka fara firgita nan take muka rabu da juna."

Matarsa da jaririnsa sun dawo garin Mokwa ne kwana ɗaya kacal kafin faruwar lamarin, bayan sun zauna a gidan iyayensa na ɗan wasu makonni tun bayan ta haihu.

"Na kalla cikin bakin ciki yayin da ruwa ke ɗaukar iyalina. Ni na tsira ne saboda na iya iyo. Allah ne ya ceci rayuwata," in ji Adamu.

Jami'an gari sun ce adadin mutanen da ambaliyar ta hallaka ya kai sama da 200 ranar Lahadi, ƙaruwa sosai daga 110 da aka tabbatar ranar Juma'a.

Ana fargabar adadin zai iya ƙaruwa nan gaba, domin hukumomi sun ce akwai kimanin mutum 500 da ba a san inda suke ba.

Tarin tarkace a garin Mokwa.

Asalin hoton, Gift Ufuoma

Bayanan hoto, Ana tunanin cewa shekaru da dama ba a taɓa samun ambaliya a Mokwa mai muni irin wannan ba

Ambaliyar ta lalata kusan duk wani abu da ta ci karo da shi, tun daga kayan amfani da ginegine sannan uwa uba rayukan mutane.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayin da yake tsaye a kan dandamali mai launin shuɗi, wanda shi ne kawai alamar inda ɗakinsa ya kasance a da, Adamu ya ce "Na rasa komai a wannan ambaliyar, amma abin da ya fi min zafi shi ne na rasa iyalina. Abu ɗaya da na mallaka yanzu shi ne wannan tufafin da yake jikina, wanda abokina ya ba ni."

Ya bayyana cewa an samu ɗaya daga cikin danginsa ya mutu, kuma ya riga ya saka a ranshi da cewa ba lalle sauran danginsa su dawo a raye ba.

Isa Muhammad, ɗan shekara 19, wanda kwanan nan ya kammala makarantar sakandare, yana cikin bakin ciki tun lokacin da ya ji labarin cewa gidan malamin da yake ƙauna ya rushe, yayin da malamin da 'yan uwansa takwas suke cikin gidan.

Isa ya ce, "An samu gawar mutane biyu, ɗaya daga cikinsu jaririn malamin ne yayin da har yanzu ba a ga malamin da ɗansa na biyu da ƙanwarsa da wasu 'yan'uwa huɗu ba.

"Wani gini ya rushe kan matar malamin inda nan take ta mutu."

Muhammad ya kuma rasa wasu daga cikin iyalinsa, inda kawunsa na cikin waɗanda suka mutu a cikin wannan bala'i.

Ya ce, "Kawuna Musa abokina ne sosai. Bayan mahaifina ya mutu a 2023, kawuna Musa ne ya kula da ni. Kullum yana koya min muhimmancin ilimi da yin abin da ya dace. Duk lokacin da na ke tunanin mutuwarsa, hawaye sukan zubo min. Ban samu barci ba tun lokacin da wannan bala'in ya faru," in ji Muhammad.

Ruwan ambaliyar a yanzu ya ja baya, kuma mazauna ƙauyen sun tattaru a ranar Asabar don ta'aziyya ga waɗanda bala'in ya rutsa da su tare da taimakawa wajen bincike.

Wasu mazauna sun shaida wa BBC cewa ruwan ambaliyar ya kai kusan ƙafa bakwai (wato mita 2.1) a wasu sassa na ƙauyen.

Wari mai ƙarfi ya ɗume Tiffin Maza inda mazauna yankin suka yi imanin cewa akwai gawarwaki a ƙarƙashin laka da ambaliyar ta kawo.

Mazauna yankin suna ƙoƙarin gano gawarwakin domin yi musu jana'iza kamar yadda suka riga suka yi wa wasu tun daga ranar Alhamis.

Ramat Sulaiman, ƴar shekar 65 ta ce, "Ban taɓa ganin irin wannan ambaliyar ba a rayuwata, amma na godewa Allah da ya tsare iyalina."

Ramat ta ce ambaliyar ya rushe mata gida gaba ɗaya, lamarin da ya bar iyalinta rasa muhallansu kuma ba mafaka.

Ramat Sulaiman tsaye kusa da wani gini da ambaliyar ta lalata

Asalin hoton, Gift Ufuoma

Bayanan hoto, Ramat Sulaiman da iyalanta sun rasa muhallansu.

Ta ce yara 100 da suke kwana a wata makarantar islamiyya da ke tazarar gida biyu daga nata, "duk ruwa ya tafi da su."

"Gani nake kamar mafarki. Yaran na ihu suna neman agaji, amma babu wanda ya iya taimaka musu. Yayin da ihunsu ke ƙaruwa, ginin ya rufta, sannan ruwa ya tafi da su."

Ɗanta, Saliu, shima ya rasa matsugunansa, bubu wani abin da ya rage.

"Na rasa aƙalla dala 1,500 a cikin ambaliyar wanda na samu daga amfanin gona da na siyar ranar da ta gabata. Na yi tunanin komawa ɗaki don ɗibar kuɗaɗen amma ƙarfi da ƙarar ruwan ya firgita ni," in ji Saliu.

"Na kuma rasa buhuna goma sha ɗaya na gyada da buhuna bakwai na wake. Ni da matata ba mu iya ɗaukar komai daga ɗakinmu ba. Amma ina godiya da muka samu damar tserewa da rai. Gawarwaki da dama ne a cikin ruwan."

"Na shiga cikin wani yanayi mai cike da firgici."

Saliu Sulaiman

Asalin hoton, Gift Ufuoma

Bayanan hoto, Ruwan ambaliya mai ƙarfi ya hana Saliu Sulaiman komawa cikin gidansa da ruwa ya rushe domin ɗauko ribar kasuwancinsa.

Hukumomi har yanzu ba su tabbatar ba ko madatsar ruwa ce ta fashe wacce ta ƙara tsananta illar ambaliyar ruwa da aka fuskanta kwanan nan kamar yadda ake ta yaɗawa ba.

Hakimin Mokwa, Alhaji Muhammadu Shaba Aliyu, ya bayyana wa BBC cewa akwai "madatsar ruwa" a yankin da za ta iya zubar da ruwa "duk lokacin da aka samu ruwan sama", amma ya ƙara da cewa girman ambaliyar da suka gani a wannan karon ya yi yawa fiye da yadda aka saba gani.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa ba ruwan sama ne ya janyo ambaliyar ba, domin sun ce lokacin da ruwan ya fara zuwa, ruwan sama ya riga ya dakata.

"Ruwan sama ba shi ne ya kawo ambaliyar ba, saboda ruwan ya tsaya da daɗewa. Ina zaune a waje sai kawai na ga ruwa yana fitowa da sauri yana wargaza komai a gabansa," in ji Malam Muhammed.

Hajiya Ramat Sulaiman ta ce: "Da na tashi zan yi sallah, na buɗe ƙofa na duba waje, babu ko digo na ruwan sama. Amma cikin ƴan daƙiƙa na fara jin mutane na ihu. Har yanzu ba mu san daga ina ruwan ya fito ba."

"Wanda ke cewa ruwan sama ne ya janyo wannan ambaliya, wallahi ba gaskiya suke faɗi ba. Ruwan sama ya tsaya kafin ambaliyar ta zo. Babu wanda ya san musabbabin wannan ambaliyar, sai dai mu ce daga Allah ne," in ji Malam Adamu.

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Mokwa, Musa Alhaji Aliyu Kimboku, ma ya ƙi amincewa da cewa ruwan sama ne ya haddasa ambaliyar.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ce an kai waɗanda suka jikkata asibiti ana ba su kulawa, yayin da waɗanda ambaliya ta raba da muhallansu an kai su sansanonin wucin gadi, kuma an raba kayan agaji.

Hukumar yanayi ta ƙasa ta yi hasashen cewa za a iya samun kwanaki har 200 na damina a tsakiyar Najeriya bana, yayin da a jihohin kudu ana iya fuskantar wani tsawon lokaci.

Tun farkon watan Mayu, gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirye-shiryen wayar da kai game da haɗarin ambaliya domin faɗakar da jama'a.

Jihohi 30 daga cikin 36 da ke ƙasar suna cikin haɗarin ambaliya, kuma Jihar Neja na daga cikinsu.

Yayin da mutanen yankin ke ƙoƙarin tattara ragowar dukiyarsu domin farawa daga farko, waɗanda suka rasa 'yan uwa kamar Malam Adamu sun ce babu yadda za su taɓa mantawa da lamarin, kodayake sun rungumi ƙaddara.