Ambaliya ta kashe mutum 60 a Brazil

...

Asalin hoton, EPA

Gwamnan Rio Grande do Sul ya ce ambaliyar ruwan da aka yi a jihar ta yi muni sosai.

Mutum 60 ne aka tabbatar sun mutu, kuma wasu dubbai sun yi ƙaura daga gidajen su bayan ambaliyar da ta taso daga gaɓar kogin Porte Alegre, babban birnin jihar.

Hukumomi sun umarci mutanen yankin su gaggauta ficewa.

Gwamna Eduardo Leite ya ce akwai buƙatar a sake gina birnin mafi bunƙasa a Brazil.

Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva zai kara ziyartar yankin a yau Lahadi, inda hukumomi suka ce akwai wasu mutum fiye da 70 da ba a sa wajen da suke ba.

A Porto Alegre, babban birnin jihar, gaɓar tekun Guaiba ce ta ɓalle, ta kuma haddasa ambaliyar da ta kwashe duk gidajen da ke kusa.

Mutane aƙalla miliyan ɗaya ne yanzu haka ke rayuwa a yankin mai fama da ɗaukewar lantarki, da rashin ruwan sha mai tsafta, ga shi kuma an hasashen ci gaba da tafka ruwan.

Evandro Lucas shi ne daraktan hukumar tabbatar da tsaro ta yankin.

Ya ce: "Muna buƙatar kayan aiki, da sinadarin tsaftace ruwa, da katifu, domin ta haka ne kawai za a ƙarfaf gwiwar mutane su koma muhallin su."

Hukumar hasashen yanayi ta Brazil ta ce ruwan saman da ake tafkawa ne ya janyo ambaliyar