Su wane ne ke fafatawa a zaɓen gwamnan jihar Anambra?

Lokacin karatu: Minti 5

Ana gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

A wannan zaɓen, mutum 16 ne gaba ɗaya ke neman kujerar gwamnan Anambra ciki har da gwamna mai ci, Chukwuma Soludo, wanda ke neman tazarce.

Dubban jami'an tsaro ne aka jibge a jihar domin zaɓen, yayin da manyan 'yan takara suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, domin tabbatar da zaɓen cikin lumana da mutunta juna.

Ga wasu muhimman abubuwa da suka kamata a sani game da 'yan takarar da ke fafatawa a zaɓen na gwamnan Anambra na 2025.

Charles Soludo ( Jam'iyya APGA)

Chukwuma Charles Soludo shi ne gwamna na biyar da aka zaɓa ta tsarin dimokuraadiyya a jihar Anambra.

Yanzu haka yana neman wa'adi na biyu a karo na biyu kenan.

A lokacin zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APGA, Gwamna Soludo ne ya lashe zaɓen a lokacin domin babu wanda ya ƙalubalance shi.

Soludo tsohon masanin tattalin arziki ne kuma babban jami'in banki, wanda ya taɓa zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

Haka kuma ya kasance shugaban hukumar gudanarwa ta Babban Bankin Najeriya.

Soludo ya kuma yi aiki a matsayin babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tattalin arziki a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a shekarar 2003.

Ya kuma taɓa kasancewa cikin kwamitin tattaunawar tattalin arzikin shugaban ƙasa a lokacin mulkin Muhammadu Buhari. Sannan ya yi aiki a matsayin shugaban hukumar tsara al'amuran ƙasa (National Planning Commission).

Gwamnan farfesa ne na tattalin arziki, kuma ya yi karatu a manyan jami'o'i irin su jami'ar Nsukka da jami'ar Cambridge da na Brookings da jami'ar Warwick da jami'ar Oxford, kuma yana zuwa koyarwa a lokaci lokaci a kwalejin Swarthmore.

An haife shi a shekarar 1960, daga Isuofia a ƙaramar hukumar Aguata. Ya auri matarsa Nonye Soludo, kuma suna da 'ya'ya shida.

A 2009, Soludo ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Anambra ƙarƙashin jam'iyyar PDP. Amma sai bayan shekaru kusan 12 kafin ya zama gwamnan jihar.

Ya fice daga PDP a 2013, ya koma APGA, amma kwamitin tantancewa na APGA ya ƙi amincewa da shi a wancan lokacin.

Daga bisani ya yi nasara a zaɓen 2021 karkashin jam'iyyar APGA, kuma ya kama aiki a watan Maris 2022, inda ya maye gurbin tsohon gwamna Willie Obiano.

Soludo ne gwamna kaɗai a Najeriya da aka zaɓa karkashin jam'iyyar APGA.

Dr Nicholas Ukachukwu (Jam'iyyar APC)

Nicholas Ukachukwu shi ne ɗan takarar gwamnan Anambra karkashin jam'iyyar APC.

Ya samu tikitin jam'iyyar ne bayan ya kayar da fitattun 'yan jam'iyyar kamar Valentine Ozigbo da Johnbosco Onunkwo da kuma Edozie Madu.

An haife shi ranar 20 ga Maris, 1967. Dan asalin Osumenyi ne, a ƙaramar hukumar Nnewi ta Kudu da ke jihar Anambra.

Ukachukwu sanannen ɗan kasuwa ne. Yana da sanao'i da dama ciki har da man fetur da iskar gas da sana'ar gini (real estate) da harkar noma da kuma kafafen yada labarai.

Shi ne mamallakin jami'ar European da ke Nigeria, tare da wasu kasuwanci daban-daban.

Ya yi digirinsa na farko a fannin nazarin gudanar da kasuwanci a Jami'ar Calabar.

Haka kuma yana da digirin girmamawa daga jami'ar Tensian da ke jihar Anambra.

Ya taɓa zama ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar birnin tarayya Abuja AMAC daga 1999 zuwa 2003.

Bayan haka ya nemi kujerar Sanata na Anambra ta kudu a zaɓen 2003.

A shekarar 2006 ya tsaya takarar gwamnan Anambra karkashin jam'iyyar HDP amma bai yi nasara ba. Ya sake tsayawa takarar Sanata a Kudancin Anambra a zaɓen 2019 ƙarƙashin jam'iyyar APGA.

Ya kuma taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukuma a Abuja.

Matarsa ta farko Nnenna Ukachukwu ta rasu sakamakon haɗarin mota a shekarar 2020.

A watan Disambar 2023 kuma, ya sake aure da Mitchel Ihezue, wadda ta kasance Sauraniyar kyau ta Najeriya a shekarar 2023.

Dr George Moghalu (Jam'iyyar LP)

Dr. George Moghalu shi ne ɗan takarar jam'iyyar LP a zaɓen gwamnan jihar Anambra.

Ya taɓa zama babban daraktan hukumar kula da sufurin ruwa na Najeriya, (NIWA).

Moghalu ya samu nasarar zama ɗan takarar LP bayan ya sami ƙuri'u 575 daga wakilan jam'iyyar da suka halarci zaben fidda gwani da aka gudanar a Finotel Hotel da ke Awka, babban birnin jihar.

Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC, amma daga baya ya fice daga jam'iyyar ya koma jam;iyyar LP.

Moghalu ya taɓa yin takarar gwamna a Anambra karkashin jam'iyyar APC amma bai yi nasara a zaɓen fidda gwani ba.

Yana da shekaru 63, kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar arewacin Nnewi ne a Jihar Anambra.

Ya auri Onyinyechi Moghalu, kuma suna da 'ya'ya biyar.

Ya yi karatu a cibiyar nazarin gudanarwa ta IMT da ke Enugu.

Jude Ezenwafor (Jam'iyyar PDP)

Jude Ezenwafor shi ne wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a watan Afrilu.

Shi kaɗai ne ya siya fam na tsayawa takarar gwamna a jam'iyyar, wanda ya kai naira miliyan 40.

Dan takarar ɗan kasuwa ne da ke harkar gina gidaje kuma yana kasuwanci ne a Abuja.

A harkar siyasa, Ezenwafor ya taɓa rike matsayi na mataimakin shugaban ƙungiyar matasan Najeriya.

Yana da shekaru 45. Ya kuma yi aiki da kusan dukkan gwamnonin da suka taba jagorantar Jihar Anambra.

A shekarar 2007 da 2021, ya nemi takarar gwamna a ƙarkashin jam'iyyar LP.. Haka kuma ya taɓa kasancewa ɗan takarar Sanata ƙarƙashin PDP.

Jude Ezenwafor dan asalin garin Nnobi ne a ƙaramar hukumar kudancin Idemil ta jihar.

Sunayen sauran ƴan takara da jam'iyyunsu

Ga jerin sunayen 'yan takara 16 da jam'iyyunsu da ke neman kujeran gwamnan Anambra.

  • Sunayen 'yan takara da jam'iyyunsu sun haɗa:
  • Onyeeze Chidi Charles – Jam'iyyar A
  • Nweke Ezechukwu Japhet – Jam'iyyar AA
  • Ifemeludike Chioma Grace – Jam'iyyar AAC
  • Nwosu Chima John – Jam'iyyar ADC
  • Nicholas Ukachukwu – Jam'iyar APC
  • Soludo Charles Chukwuma – Jam'iyyar APGA
  • Otti Cyprain Echezona – Jam'iyyar APM
  • Nweke Chrispopher Chukwudubem – Jam'iyar APP
  • Okeke Chika Jerry – Jam'iyyar BP
  • Moghalu George Nnadubem - Jam'iyyar LP
  • Onyejegbu Geoffrey – Jam'iyyar NNPP
  • Ndidi Christy Olieh – Jam'iyyar NRM
  • Ezenwafor Jude – Jam'iyyar PDP
  • Chukwurah Vincent – Jam'iyyar SDP
  • Chukwuma Paul Chukwuka – Jam'iyyar YPP
  • Ugwoji Uchenna Martin – Jam'iyyar ZLP