Ƙasashe biyar mafiya zaman lafiya a duniya a 2025

Asalin hoton, Getty Images
A Shekarar 2025, zaman lafiya ya kasance babban arziki ga duniya. Yaƙe-yaƙe sun bazu, an tsaurara tsaron kan iyakoki, yayin da dambarwar kasuwanci ta tsananta.
Alƙaluman cibiyar lura da zaman lafiya ta duniya da ake yi wa laƙabi da 'Global Peace Index (GPI)', sun nuna cewa yawan rikice-rikice da aka samu a cikin ƙasashen duniya ya kai matsayin da ba a taɓa gani ba, tun bayan yaƙin duniya na biyu.
Yayin da sabbin yaƙe-yaƙe uku suka ɓarke a 2025, ƙari kan waɗanda shekarar ta tarar, mafi yawan ƙasashe sun ƙara ƙarfafa rundunonin sojojinsu.
Sai dai duk da ƙaruwar rikice-rikicen da duniya ta gani a 2025, wasu ƙasashen sun ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da lumana.
Cibiyar ta GPI ta bibiyi ƙasashen duniya tare da yin nazarin zaman lafiyarsu, ta hanyar auna rikicin cikin gida da na waje da suke fama da su, da ayyukan sojinsu da ayyukan ta'addanci da kisan gilla da irin matakan tsaron da suke ɗauka.
Bayan nazarin cibiyar ta GPI ta gano wasu ƙasashe biyar da ta ce su ne mafiya zaman lafiya da lumana a duniya a 2025.
Mun yi magana da mazauna wasu waɗannan ƙasashe domin jin yadda yadda rayuwa take a cikinsu da irin tsare-tsaren da ƙasashen suka yi da suka taimaki zaman lafiya da tsaronsu.
Ƙasashen da rahoton ya bayyana sun haɗa da:
Iceland

Asalin hoton, Getty Images
Iceland ta kasance wadda ta fi kowace ƙasa zaman lafiya a duniya tun 2008, ta hanyar yin zarra a fannoni auna zaman lafiya uku, da suka ƙunshi amince da tsaro da kuma fannin rikici da sayen makamai.
A wannan shekarar ƙasar ta samu ƙarin matsayi da kashi 2 cikin 100, lamarin da ya sa ta bai wa ƙasa ta biyu tazara mai yawa.
Mazauna ƙasar sun bayyana yadda suke walwalarsu ba tare da wata fargaba ba.
"Za ka iya yawo kai kaɗai tsakar dare, ka je inda kake so, ba tare da wata fargaba ko damuwa ba'' in ji Inga Rós Antoníusdóttir, wadda aka haifa a Iceland, kuma take aiki a wani kamfanin shirya tafiye-tafiye.
''Za ka ga jarirai suna barci ko wasa cikin zanin goyo a gafen wuraren cin abinci ko kantunan sayayya, yayin da iyayen nasu ke cin abinci ko sayayya cikin kwanciyar hankali'', in ji ta.
Ta ƙara da cewa a Iceland ƴansanda ba sa riƙe bindiga, saboda riƙe ta ba shi amfani.

Asalin hoton, Getty Images
Inga ta ce a ganin abin da ya sa Iceland ta yi zarra shi ne tsarin da ƙasar ke da shi na bai wa kowa dama ba tare da nuna bambanci tsakanin maza da mata ba.
"Daidaito da tsarin zamantakewa sun samar da adalci da aminci ga kowa," in ji ta.
Ireland
Duk da cewa ƙasar ta fuskaci rikice-rikice a ƙarni na 20, a yanzu ta kasance gaba-gaba wajen wanzuwar zaman lafiya da lumana.
Ta samu maki mai yawa a bana daga cibiyar tattara alƙaluman zaman lafiya ta duniya, bayan da ta rage yawan kashe kuɗi a fannin sojinta.
Ta kuma shiga jerin ne saboda amincin da al'ummarta ke ciki, inda aka samu ƙarancin aikata manyan lafuka.
A Ireland za ka iya neman taimakon mutum, koda baka sans hi ba, kuma ya taimakeka kamar ɗan'uwanka'', in ji Jack Fitzsimons, mazaunin Ireland kuma daraktan wata majami'a a ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Kowa a ƙasar na ɗaukar kowa a matsayin ɗan'uwansa '' wanna ya sa za ka ji kana cikin aminci a akowane lokaci kuma a ko'ina, ko da kana ƙaramin gari ko babba'', a cewar Jack Fitzsimons.
Ya ce babban tallafin harkokin rayuwar yau da kullum da gwamnati ke bayar wa sun taimaka wajen rage bambance-bambance da ke tsakanin al'umma.
''Ƙasa ce da za ka nemi taimakon mutumin da ba ka sani ba kuma ya bar aikin da ke gabansa domin ya taimaka maka'', in ji Jack Fitzsimons.
A matakin duniya kuwa Ireland ta kasance ƴar ba ruwanmu ta fannin soji, lamarin da ya sa ko ƙungiyar Nato ba ta shiga ba.
New Zealand
A wannan shekara New Zealand ta samu ci gaba a fannin zaman lafiyarta, inda koma mataki na uku, bayan da ta samu ci gaba a fannin aminci da taro da raguwar zanga-zanga da ayyuka masu alaƙa da ta'addanci.
A matsayinta na ƙasa da ke kan tsibiri a tekun Pacific, kasancewar New Zealand a tsakiyar ruwa ya taimaka mata wajen samun barazana daga waje , to amma tsare-tsaren da ta yi a cin gida sun taimaka wa mazauna ƙasar jin suna cikin nutsuwa.
"Dokokin ƙasar na mallakar bindiga na daga cikin masu tsauri a duniya, wanda ya taimaka matuka wajen samar da aminci a ƙasar'', in ji lifelong Kiwi Mischa Mannix-Opie, daraktar wani kamfanin makamashi maras gurɓata muhalli.
Ta ƙara da cewa ƙasa ce da ƙananan yara ke zuwa makaranta su kaɗai ba tare da rakiya ba.
''Mutane kan bar ƙofofin gidajensu a buɗe, kuma masu mota kan tsaya su taimaki wanda motarsa ta lalace, akwai aminci mai ƙarfi tsakanin ƴanƙasar'', in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
Armin Pfurtscheller shugaban otal ɗin SPA-Hotel Jagdhof ya ce "hakan ya sa ƙasar ta mayar da hankali wajen gina ƴan ƙasar maimakon yaƙi, inda a yanzu ta zama kan gaba a duniya a fannonin amincin walwalar mutane da ilimi mai inganci da tsarin kiwon lafiya na zamani da kuma aminci tsakanin mutane,'' in ji shi.
A New Zealand ne za su je bakin ruwa tsakar dare ba tare da fargaba ba, ba a kulle gidaje ba a kulle kekuna'', in ji Pfurtscheller.
Austria
Austria ta samu ƙaruwar zaman lafiya a cikinta a 2025, lamarin da ya sa GPI ta sanya ta a matsayi na huɗu.
Kamar dai ƙasar Ireland, Austria na da dokokin da suka sanya ta zama ƴar ba ruwanmu a fannin ƙawancen soji a duniya, lamarin da ya sa ba ta cikin ƙawancen Nato.
Wannan ya sa ƙasar ta mayar da hankalinta kan sarrafa ma'adinanta na cikin gida.
Switzerland
Rahoton na GPI a 2025 ya bayayna ƙasar, Switzerland a matsayi na byar cikin ƙasashe mafiya zaman lafiya a duniya.
Switzerland, ta jima cikin jerin ƙasashen da ke gaba-gaba wajen wanzuwar zaman lafiya da tsaro a cikinsu.
Alƙaluman na Global Peace Index sun nuna cewa Switzerland ta yi matuƙar ƙoƙari wajen rage muyagun laifuka a cikin ƙasar.
Ƙasashe 10 da GPI ta fitar mafiya zaman lafiya a duniya a 2025

Asalin hoton, Getty Images
1. Iceland
2. Ireland
3. New Zealand
4. Austria
5. Switzerland
6. Singapore
7. Portugal
8. Denmark
9. Slovenia
10. Finland







