Amfani 10 na ƴaƴan kashu

Hoton kwallon yazawa a hannu

Asalin hoton, GRACE CARY VIA GETTY IMAGES

Lokacin karatu: Minti 3

Mene ne ƙwallon yazawa?

Shi dai kwallon yazawa ko kashu ko kuma kanju kamar yadda wasu ke ce masa, ana daukarsa tamkar gyada, amma kuma a bangaren kimiyyar tsirrai shi iri ne, saboda ana samunsa ne daga 'ya'yan itacen yazawa, kamar mangwaro.

Ita bishiyar yazawa tana yi ne a yankunan da suke da yanayi na zafi, kamar kasar Indiya da Vietnam, wadanda suna daga cikin kasashen da aka fi samar da wannan dan itace.

Shi dai kwallon yazawa kamar yadda aka sani, karami ne, da siffar koda, da launin kore-kore.

Ina iya cin kwallon haka danye, ko a gasa ko a dafa shi da dai sauran hanyoyiun sarrafa shi a ci.

Sinadaran gina jiki da kwallon ke dauke da su

Wata mata da kwallon yazawa a hannunta

Asalin hoton, CLEMENT TARDIF VIA GETTY IMAGES

'Ya'yan yazawa suna dauke da sinadarai masu yawa masu amfani ga jikin mutum, amma babban sinadarin da ya fi bayarwa shi ne furotin (protein), da kuma maiko

Saboda yawan sinadarin furotin mai gina jiki da kuma maiko maras illa da kwallon yake dauke da su, idan aka ci kamar kwallo 15 (30g) sai mutum ya ji ya wadata.

Haka kuma wannan kwallo 15, yana iya ba mutum kashi 20 cikin dari na sinadarin maganiziyom (magnesium), wanda jiki ke matukar bukata, da dai saurna sinadarai masu matukar amfani ga jikin mutum.

Amfanin 'ya'yan yazawa ga lafiyar mutum

Wani mutum da kwallon yazawa cikin tangaran a hannunsa

Asalin hoton, AARONAMAT VIA GETTY IMAGES

  • Yana taimaka wa wajen hana tsukewar jijiyar raba jini zuwa sassan jiki (arteries)
  • Yana taimakawa mutum ya yi tsawon rai
  • yana dauke da sinadarai masu yaki da cutuka, inda yake kare mutum kamuwa daga wasu cutuka
  • Yana rage hadarin cutar zuciya da bugun jini
  • Yana rage alamun cutar rashin bargon dake mahadar kasusuwa
  • Yana rage matsalar kumburin hanji da ke iya sa mutum saurin jin bahaya da gudawa da ciwon baya
  • Yana iya sa ka rage teba a tsanaki
  • Yana taimakawa wajen daidaita yawan sukarin cikin jini
  • Yana iya taimakawa wajen kare mutum daga hadarin bugun jin
  • Yana taimakawa wajen kare mutum daga cutar mantuwa

Ko 'ya'yan yazawa na da amfani a gare ka?

'Ya'yan yazawa a bishiya

Asalin hoton, Getty Images

1. Suna taimaka wa wajen hana tsukewar jijiyar raba jini zuwa sassan jiki (arteries)

2. Suna taimakawa mutum ya yi tsawon rai

3. Suna dauke da sinadarai masu yaki da cutuka, inda yake kare mutum kamuwa daga wasu cutuka

4. Suna rage hadarin cutar zuciya da bugun jini

5. Suna rage alamun cutar rashin bargon dake mahadar kasusuwa

6. Suna rage matsalar kumburin hanji da ke iya sa mutum saurin jin bahaya da gudawa da ciwon baya

7. Suna iya sa ka rage teba a tsanaki

8. Suna taimakawa wajen daidaita yawan sukarin cikin jini

9. Suna iya taimakawa wajen kare mutum daga hadarin bugun jin

10. Suna taimakawa wajen kare mutum daga cutar mantuwa

Ko ya dace kowa ya ci 'ya'yan yazawa?

Yana iya yuwuwa jikin wani ba ya son 'ya'yan yazawa, saboda haka idan har ka ci su kuma ka ga wata alama ta kan-jiki kamar, matsalar numfashi, ko kumburar fuska, harshe ko lebe, to sai ka yi sauri ka nufi asibiti domin hakan zai iya kasancewa barazana ga rayuwarka.

Mutanen da ba sa iya cin gyada suna iya gamuwa da matsalar kan-jiki idan suka ci 'ya'yan yazawa.

Abubuwan da suke da muhimmanci…

'Ya'yan yazawa suna da amfani sosai ga lafiyar mutum kuma suna samar da sinadaran gina jiki sosai - wadanda suka hada da furotin (protein) da maiko maras hadari ga jiki, tare kuma da bitamin da yawa wadanda ke taimaka wa jiki wajen bunkasa da gina garkuwa daga wasu cutuka.

Kamar dai sauran 'ya'yan itatuwa dangin gyada, ya fi dacewa mutum ya ci su daidai-wa-daida, wato kada ya ci ya wuce hankali.

Haka kuma sun fi amfani a ci su haka danyu ba tare da an gasa ko soya su ko dafa su ko hada su da gishi ko sukari ko wani abu ba, domin hada su da wani abin zai iya rage musu amfanin da za su yi maka a jiki.