Sabbin alƙawuran da Tinubu ya yi wa Katsina kan 'yanbindiga - Radda

Shugaba Tinubu da tawagar dattijan jihar Katsina

Asalin hoton, Kano State Government

Bayanan hoto, A ranar 3 ga watan Satumba ne Gwamna Dikko ya jagoranci dattijan jihar Katsina zuwa fadar Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin jihar Katsina a arewacin Najeriya ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi alƙawarin taimaka mata da sababbin kayan daƙile hare-haren 'yanfashin daji da ke addabar mazauna jihar a kullum.

Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ne ya bayyana wa BBC hakan a wata hira ta musamman, inda ya ce cikin kayayyakin har da jirage marasa matuƙa na kai hari.

Shugaba Tinubu ya yi wa gwamnatin jihar alkawuran ne lokacin da gwamnan ya jagoranci wata tawagar al'ummar jihar da suka ziyarci fadar shugaban kasar.

Tawagar gwamnan wadda ta kunshi dattawa da maluma na Katsina, ta kai ziyarar ne bayan wani mummunan hari da 'yanbindigar suka kai kan masallata a unguwar Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a kwanakin baya.

Gwamnan ya bayyana harin da ire-irensa da suke kaiwa a kusan kowace rana a matsayin "kura ta kai bango, wadda ta zama dole su dangana da fadar shugaban kasar domin daukar mataki".

Jerin alƙawuran

Dikko Umaru Raɗɗa

Asalin hoton, OTHERS

Gwamna Radda ya zayyana wa BBC jerin alkawuran da ya ce Shugaba Tinubun ya yi wa tawagar tasu kan matsalar tsaro kamar haka:

1- ''Ya ce mana zai kira jami'an tsaro ya tabbatar da sun sauya salo da dabarun da suke amfani da su wajen yakar ta'addanci.''

2- ''Ya ce zai tabbatar da an kawo mana karin karfi na sama, musamman jiragen sama marasa matuka wadanza za su rika kai hari da jefa bamabamai a kan wuraren da 'yanta'adda suke.''

3- ''Zai rika kiran jami'an tsaro domin su ba shi bayanin abin da ake ciki kan umarnin da ya bayar."

4-''Lokacin da hafsan-hafsoshin soji ya zo mana Katsina, ya ce za a kafabataliya a kudancin Katsina. Wannan ma Shugaban ya ce za a yi hakan.''

5- ''Sannan akwai alkawarin da ke tsakaninmu da shugaban 'yansanda cewa za a bude sukwaduron (sansani) na 'yansandan sintiri a kudancin Katsina, shi ma mun jaddada masa kuma ya yi alkawarin hakan.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamnan ya ce kafin alkawuran da shugaban kasar ya yi wa jihar don magance matsalar tsaron, an kara yawan jami'an tsaron da ke aiki a jihar, lamarin da ya kai ga raguwar irin hare--haren barayin dajin.

''Jami'an soja da 'yansanda da jami'an tsaro na gwamnatin jiha da kuma maharba da muka dauko daga Maiduguri duka sun kara kaimi a yaki da barayin daji.

''A sanadiyyar hakan da auran matakai abubuwan na raguwa inda sai dai ka ji sun kashe mutum daya nan da can ko an kora su, sabanin tarin mutane, ko kuma su barayin dajin an kora su ko an kashe su.

''An samu cigaba sosai ta yadda za ka ga wata rana ma ba inda barayin dajin suka kai wa al'umma hari.

Gwamnan ya ce a yain ganawar tasu da Tinubu : ''Mun sheda mashi halin da kudancin Katsina suke ciki tun da a gwargadon ikonmu a nan arewacin Katsina wanda da nan ne wurin yakin yake.

''Allah kuma Ya kawo mana sauki ta hanyar tattaunawa da al'umma suka yi da 'yanta'addan aka samu maslaha a garuruwa irin su Batsari da Jibiya da Danmusa da Safana, da ba inda ake ta'asa kamar nan.''

Gwamnan na jihar Katsina a kodayaushe yana cewa ba zai taba yin sulhu da 'yanta'adda ba, ko ya ba shi kudi ko wani abu domin sulhu ba, amma ya ce ba shi da matsala idan su 'yan ta'addan suka nemi sulhun da gwamnati da kansu ko kuma da jama'ar da suke yi wa ta'addancin.

Matakin sulhun ya sa aka ga saukin hare-haren 'yanta'addan a wasu garuruwan na jihar ta Katsina, amma kuma ya ta'azzara a wasu sassan da babu sulhun, wanda hakan ya sa gwamnatin jihar ta ce ta tashi tsaye domin neman gwamnatin tarayya ta taimaka musu da gaske kan matsalar tsaron wadda shekara da shekaru ta addabe su, duk da matakan da jihar da ita ma gwamnatin tarayya ke dauka.